SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU
By Tahir lawan Muaz Attijaneey 002348060306021 attijaneeykano@gmail.com 1. GABATARWA Assalamu alaikum jamaa masoya Annabi saw da fatan zamu shga wannan wata mai alfarma cikin saa. Yau wannan makala tamu zata tabo SALLAR TARAWIHI NE DA KUMA TAHAJJUDI saboda Munasabar wannan wata, da fatan Allah ya karbi ibadunmu yasanya mu cikin yantattu. 2. MAANAR TARAWIHI: Kalmar Tarawihi a larabci ta samo asali ne daga TARWIH wato zama don Hutu, sai aka ambaci Sallar da Tarawih saboda hutun zama da ake yi tsakanin rakao’I 4 na sallar a wancan lokaci. Amma a Sharia itace sallar Kiyamullail da Manzon Allah Saw yai Ishara da fadinsa ( من قام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له ) “wanda ya tsaida dararen Ramdana don Imani da neman Lada an gafarta masa” don hakane akacea itace sallar da akeyi don tsaida Ramadan daga bayan Ishai har zuwa hudowar alfijir. 3. ASALINTA A SHARIA Asalinta sh