SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU
By Tahir lawan Muaz Attijaneey
002348060306021
attijaneeykano@gmail.com
1. GABATARWA
Assalamu alaikum jamaa masoya Annabi saw da
fatan zamu shga wannan wata mai alfarma cikin saa. Yau wannan makala tamu zata
tabo SALLAR TARAWIHI NE DA KUMA TAHAJJUDI saboda Munasabar wannan wata, da
fatan Allah ya karbi ibadunmu yasanya mu cikin yantattu.
2. MAANAR TARAWIHI:
Kalmar
Tarawihi a larabci ta samo asali ne daga TARWIH wato zama don Hutu, sai aka
ambaci Sallar da Tarawih saboda hutun zama da ake yi tsakanin rakao’I 4 na
sallar a wancan lokaci.
Amma a
Sharia itace sallar Kiyamullail da Manzon Allah Saw yai Ishara da fadinsa
(من
قام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له)
“wanda ya tsaida dararen Ramdana don Imani da
neman Lada an gafarta masa” don hakane akacea itace sallar da akeyi don tsaida
Ramadan daga bayan Ishai har zuwa hudowar alfijir.
3. ASALINTA A SHARIA
Asalinta shine aikin Manzo saw kamar yadda
Bukhari ya Rawaito cewa (Sayyidah Aisha rta tace manzon Allah saw ya
fito cikin wani dare (a Ramadan) yai Sallah sai mutane suka bishi sukai sallah
a bayansa, sai mutane suka wayi gari suna bada labarin hakan sai mutane suka
taru fiye da jiya sukai sallah a bayansa sai suka wayi gari sukai ta hira hakan
sai suka taru a rana ta uku fiye da ranekun baya Manzo sawya fitoyai sallah
suka bishi, suka sake wayar gari suna masu hirar haka sai suka taru a rana ta
hudu fiye da rana ta ukun har Masallaci ya kasa daukar jamaa amma Manzo bai
fito ba har sai da alfijir ya keto sai ya foto akai Asuba sannan ya juyo ya
kalli jamaa ya godewa Allah sannan yace “hakika ina sane da taruwar da kukai
amma ni naji tsoron kar a farlanta muku wannan Sallah ne kuma kuzo ku kasa” to
har manzo yai wafatiana kan haka.)ga hadisin kamar yadda yazo a Bukhari:
حَدَّثَنَا
يَحْيَى بْنُ بُكَيْرٍ ، حَدَّثَنَا اللَّيْثُ ، عَنْ عُقَيْلٍ ، عَنِ ابْنِ
شِهَابٍ ، أَخْبَرَنِي عُرْوَةُ أَنَّ عَائِشَةَ ، رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهَا ، أَخْبَرَتْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم خَرَجَ لَيْلَةً
مِنْ جَوْفِ اللَّيْلِ فَصَلَّى فِي الْمَسْجِدِ وَصَلَّى رِجَالٌ بِصَلاَتِهِ
فَأَصْبَحَ النَّاسُ فَتَحَدَّثُوا فَاجْتَمَعَ أَكْثَرُ مِنْهُمْ فَصَلَّوْا
مَعَهُ فَأَصْبَحَ النَّاسُ فَتَحَدَّثُوا فَكَثُرَ أَهْلُ الْمَسْجِدِ مِنَ
اللَّيْلَةِ الثَّالِثَةِ فَخَرَجَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم فَصَلَّى
فَصَلَّوْا بِصَلاَتِهِ فَلَمَّا كَانَتِ اللَّيْلَةُ الرَّابِعَةُ عَجَزَ الْمَسْجِدُ
عَنْ أَهْلِهِ حَتَّى خَرَجَ لِصَلاَةِ الصُّبْحِ فَلَمَّا قَضَى الْفَجْرَ
أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ فَتَشَهَّدَ ثُمَّ قَالَ أَمَّا بَعْدُ فَإِنَّهُ لَمْ
يَخْفَ عَلَيَّ مَكَانُكُمْ وَلَكِنِّي خَشِيتُ أَنْ تُفْتَرَضَ عَلَيْكُمْ
فَتَعْجِزُوا عَنْهَا فَتُوُفِّيَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم وَالأَمْرُ
عَلَى ذَلِكَ.
To ana haka har sai da zamanin sayyidin Umar
RTA yazo sai ya fito Masallaci da dare sai yaga mutane suna Sallah kowa daban
daban ko wanan yanayi wasu tsiraru na binsa, sai sayyidina Umar yace wallah ina
ganin da na hade su karkashin Mutum daya
zaifi, sa a karkashin Ubayyu bn Kaabin. Shine har wata rana ya fito ana sallah
sai yaga mutane sunyi sahu suna binsa
sai yace (Madallah da wannan Bid’ah)
Tun daga wannan Rana Tarawihi ta zamo a tsarin
da muke gani.
4.YADDA AKE YIN TARAWIHI
Ya tabbata cewa Sallar tarawihi ana yinta ne
rakaa 10 sai Shafa’I da wutri, ko ayi 20 sai Shafa’I da wutri, ko 36. Amma
abinda aikin Musulmi yafi Tabbata akai shine Rakaa 20 sai Shafa’I da wutri
kamar yadda yake a mazhabar Malikiyya kuma hakan sayyiduna Umar ya aikata, amma
kowace akayi daidai ne. sannan ana yin ta ne rakaa biyu sai ai zaman Tahiya ai
sallama haka har a gama, in mutum yayi hudu hudu ta halatta amma ba haka akaso
ba, haka da zai yi ta baki daya Ishirin ya rika zaman tahiya duk bakin rakaa
biyu da sallama daya a karshe tayi amma hakan MAKARUHI ne, amma banda a wajen
Shafiawa.
5. KARANTA ALKURANI BAKI DAYA
Hakanan anso a samu MakarancinAlkurani ya zamo
Limami da zai karance Alqurani baki daya a cikin Azumin don mutane su
saurareshi baki daya saboda kasancewa sakon ubangji ne da kuma aka saukar dashi
a wannan wata, amma in akwai cutuwar masu bin sallar to abarshi.
6. YIN TARAWIHI A GIDA KO A MASALLACI WANNE
YAFI
Malamai sunyi sabani akan shin ayita amasallaci
ne yafi ko a gida, Malikawa da dama sun tafi kan anso yinta a gida ne sabodayafi
nisanta daga RIYA haka Manzo saw yana cewa cikin hadisin da tirmizi ya rawaita
daga Zaidu daan Sabit rta cewa MAFIFICIYA
SALLOLINKU WADDA AKAYI TA A GIDA IN BANDA SALLAR FARILLAH. Amma suma sun kafa Sharadin in Mutum zai a
gida din to ya tabbata zai fi nishadi, sannan ya zamo ba a Makka bane ko A
madina kuma kada hakan ya bayu izuwa wofintar da Masallatai saboda su
Masallatai ana yabon masu rayasu. Sauran
mazhabobin uku kuwa sai suka ce aa ayi a Masallaci Yafi saboda su ibadu da aka
sharanta an fis ayi a masallaci. Amma a zahiri hujjojin Malalikawa sunfi karfi.
7.KHATIMA
SALLAR
TAHAJJUDI
Magana mafi inganci babu wata Sallah a ramadan
wa ita Tahajjudi, duk dai maganar da zaka samu a littafai na magabata magan ce
akan sallar Tarawihi, ita tahajjudi ta samo asali ne kawai daga cewa an
farlantawa Manzo saw yin sallah a duk dararensa na rayuwa shine Allah swt yake
cewa
(ومن الليل فتهجد به
نافلة للك)
Sai abin ya hadu da zazge dantsen da Manzon
tsira saw yake kara yi a karshen watan wato goman karshe na Ramadan don haka
daga wanna ne Muma muke kara wata sallah akn ta Tarawihi don mu sake zage
dantse kwarai a wannan lokaci.
Saboda haka ita a ShariarvMusulunci sai dai mu
sanya ta a Babin Fadin Annabi saw da
yake cewa (Wanda ya sunnanta wata sunna mai kyau to yana da ladanta da ladan
wanda ya aikata ta har zuwa Alkiyama) dakuma babin raya dararen da ake ganin
anan ne lailatul kadari yake don a rabauta dashi.
Kuma babban abin Shaawar ga mu Tijjanawa shine
kasancewar duk wanda yayi SALLAR TAHAJJUDI a Nigeria to A wurin mu ya koya,
tunda Khalifa Sheikh Ishaq Rabiu KHADIMUL QURAN shine ya fara assasata a
masallacinsa dake Goron dutse a KANO bayan ya gano haka a Makka kuma yaga mu
anan kasar baa yinta don haka ya fara jagorantar ta tare da makaranta daga
yayansa da Khadimansa, sannan kowa ya gani yai koyi da hakan.
A karshe yafi kamata itama ta zama a gida in
kuma an fito wajen to a nisanci Riya da kuma keta Sharia.
Allah ya karbi Ibadunmu ya yanta mu ya barmu da
Annabi saw.
Mungode Aman kasa alfahri kar yabatama lada
ReplyDelete