LAILATUL KADARI DA FALALARTA
ZAWIYAR TIJANIYA ONLINE LECTURES Karkasin jagorancin Sayyadah Ummuhani Ibrahim Niasse Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah ya tabbata ga Annabi Muhammadu SAW da alayensa da Sahabbansa. Bayan haka, wannan gajeruwar Makala game da lailatul kadari na kasata zuwa wadannan matakai Ma;anar 1.Lailatul Kadari, 2. Falalarta 3. Yaushe ne ake samunta, 4. Me ya kamata mutum yayi a cikinta. 5. Alamunta 1. Menene Lailatul Kadari? Lailatul Kadari dai wani dare ne da Allah ya kebanci Al’ummar Annabi Muhammadu SAW dashi don jin kai Garesu, domin Imam Maliku ya rawaito a Muwaddarsa cewa manzo saw an nuna masa abinda Allah yaso na rayuwar mutanen da suke gabaninsa, sai ya zamo kamar rayuwar al’ummarsa ta zamo gajeruwa ce da bazasi uya riskar abinda wadancan al’ummatan da suka rigayesu ban a ibada, sai Allah ya bashi daren Lailatul Kadari wadda tafi wata dubu. Kuma wannan dare shine wanda Allah swt ya saukar da Alkurani gaba dayansa daga halararsa zuwa wani wuri a sama da ...