LAILATUL KADARI DA FALALARTA
ZAWIYAR TIJANIYA ONLINE LECTURES
Karkasin jagorancin Sayyadah Ummuhani Ibrahim Niasse
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah ya tabbata ga Annabi Muhammadu SAW da alayensa da Sahabbansa.
Bayan haka, wannan gajeruwar Makala game da lailatul kadari na kasata zuwa wadannan matakai
Ma;anar 1.Lailatul Kadari, 2. Falalarta 3. Yaushe ne ake samunta, 4. Me ya kamata mutum yayi a cikinta. 5. Alamunta
1. Menene Lailatul Kadari?
Lailatul Kadari dai wani dare ne da Allah ya kebanci Al’ummar Annabi Muhammadu SAW dashi don jin kai Garesu, domin Imam Maliku ya rawaito a Muwaddarsa cewa manzo saw an nuna masa abinda Allah yaso na rayuwar mutanen da suke gabaninsa, sai ya zamo kamar rayuwar al’ummarsa ta zamo gajeruwa ce da bazasi uya riskar abinda wadancan al’ummatan da suka rigayesu ban a ibada, sai Allah ya bashi daren Lailatul Kadari wadda tafi wata dubu. Kuma wannan dare shine wanda Allah swt ya saukar da Alkurani gaba dayansa daga halararsa zuwa wani wuri a sama da ake cewa dashi BAITUL IZZAH. Wanda daga nan ake saukeshi da kadan kadan ga manzo SAW shiu yasa ake kiran watan Ramadan da watan Alkurani.
A wannan gaba Allah saw yake cewa: {إِنَّا أَنزَلْنَهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ}
“Hakika mu mun saukar dashi a cikin daren Lailatul Kadari”
2. Falalar Lailatul Kadari
Lailatul Kadari kamar yadda ya gabata yafi dare Dubu wanda babu irinsa ciki, wannan na nufin duk Bawan da ya tsaida daren to zaa rubuta masa tamkar ya raya dararen watannin dubu ne, ko ace yayi abinda yafi haka, tunda Allah cewa yayi “daren Lailatul Kadari shine yafi Alheri daga watanni 1000. Ita kanta Kalmar KADAR din tana nufin ALKADARI MAI GIRMA. Hakana manzo saw yana fada a cikin hakkinta kamar yadda Bukhari ya rawaito cewa:
((من قام ليلة القدر إيماناً واحتساباً غفر له ما تقدم من ذنبه))
Wanda ya tsaida daren lailatulkadri don Imani da neman ladan Allah to kuwa zaa gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa”
3. Yaushene daren Lailatul Kadari
Akwai sabani mai yawan gaske tsakanin malamai game da ayyana daren Lailatul Kadari wanda akwai zantuka sama da hamsin akan haka, wannan ya samo asali ne daga boye daren da Allah yayi a cikin dararen Ramadan, sannan da samun nassosin hadisai da aka samo mabambamta da sukai isharori game da daren. Dada wadannan Nassosin hadisai akwai:
a. Imam Malik, Da Bukhari sun rawaito hadisi daga Abi Sa’id Alkhudri cewa Manzo saw ya kasance yana Ittikafi a goman tsakiyane na Ramadan, to a wata shekara daya yai ittikafin har said a daren 21 ga Ramadan yazo wato ranar da yake fitowa daga Ittikafin nasa, sai ya fito yayi khudba yace: wanda yake yayi ittikafi tare dani to ya dawo yayi wani ittikafin a wannan goman Karshen, domin ni naga wannan Dare sai aka mantar dani ita, amma dai na ganni a cikinta ina mai yin sujjada akan Ruwa da Tabo, don haka ku neme daren a cikin goman karshe. Ku nemeta a dukkan Mara ( wato wutiri, 21, 23, 25, 27, 29.) Abu Sa’id yace a wannan Dare sai sama tayi ruwa kuma masallacin Manzo saw an masa rufine das Zangar Dabino don haka sai cikin masallacin ya jike sharkaf, sai na kalli fuskar Manzo saw a wannan rana bayan ya dawo daga Sallar Asuba sai naga alamunRuwa da Tabo a goshinsa, wato a Asubahin Daren 21 fawata.
To kunga wanna hadisi yana nuna cewa 21 ne.
b. A wani hadisin da suka rwaito da sanadinsu zuwa Urwatu bn Zubair daga Babansa yana cewa “ku nemi wannan dare na lailatul Kadari a goman karshe.”
c. A wani hadisin daga Abdullahi Bn Umar “ku nemi shi a Bakwai na karshe” bugu da kari akwai wani hadisin daga Ibn Umar din cewa an nunawa wasu dagasahabban Manzo saw cewa shi daren yana cikin bakwai na karshe ne, saboda haka sai Annabi saw yace: naga dai duk abinda kuka gani an nuna muku ya hadu akan cewa daren nan yana cikin Bakwai na karshe, don haka wanda zai neme shi to ya bincike shi a Bakwai na karshe.
d. Abdullahi dan Unais Aljuhaniy shi kuma ya tambayi Annabi saw ne yana cewa: ni mutum ne da gidana yake nesa, don haka wane dare zaka umarceni na zo na sauka a masallaci? Sai yace dashi “ kazoo daren 23 ga wata” Maliku ya rawaitoshi a MUWADDA.
e. Shi kuwa Hadisin Anas Dan Malik cewa yake wata rana Manzo Saw ya fito sai yace: “ni an nuna min wannan dare a Ramadan har said a wane dane sukai jayayya da Musu tsakanainsu sai aka dauke ta, ku nemi daren a 29, da 27, da 25.”
f. A wani hadisin na Bukahri daya rawaita daga Ibn Abbas cewa “daren yana cikin 10 na karshe,: cikin tara da suka shude ko bakwa da sukai saura.
A takaice dai Raayin da yafi rinjaye shine daren yana ciratuwa ne a goman karshe, musamman a cikin mara (21,23,25,27,29) sannan zai iya kasancewa ba cikin MARA ba kamar daren (22,24,26,28) dalili kuwa shine yadda manzo saw a hadisin da muka fada a baya cewa ku nemeshi في سابعة تبقى “a bakwai data wanzu” wadda in watan yazama 29 n3 to zai zama a daren 23 ne, in kuma ya zamo a watan mai 30 n3 to zai zama daren 24 kenan.
Don haka akeso kowa ya zage damtse wajen bauta a kwanakin baki dayansu, domin kuwa haka shi shugaban SAW yake yi kamar yadda Bukhari ya rwaito cewa “idan goman karshe ta shigo sai Manzo saw ya Daure kwarjallensa (ya zage damtse) ya kuma farkar da ahlinsa”
4. Meya kamata Mutumm yayi a wannan Rana.
Tirmizi Nasa’iy da Ibn Majah sun rawaici hadisi daga Sayyadah Aisha RTA tace na tambay Annabi saw cewa in na gane Lailatul Kadri mai zance/ sai Manzo saw yace ki rika cewa:
اللَّهُمَّ إِنَّك عَفْو تحب الْعَفو فَاعْفُ عني "
Wannan ya nuna mafi Alherin Addua a wannan rana itace wanna addua da Shugaba saw ya koyar.
Baya ga wannan Addua anaso Mutum ya yawaita duk adduar data zo a harshensa ta alheri, haka a yawaita sallolin nafila da hailala da tsarkake Allah da kuma salati ga Annabi saw da Karatun Alkurani.
5. Alamomin Daren Lailatul Kadari
Wasu malamai sun Ambaci alamomin Daren Lalatul Kadari wanda hakan wani kokari ne ko kuma kasahfi ne da Allah yake yiwa Sahin Auliya’u, donhaka bana son na tsawaita bayani anan, kawai zan kawo maganar sheikh Abdullahi bn Fodio ya kawo as taafsirinsa Dhiya’ut Taweel inda yace:
“Daga Alamun daren cewa darenta yana kasancewa a nutse ba sanyi ba zafi baa yin Jifa da kibiyar Taurari, zaka ganta tayi wasai, kai kace wata ne rana tana hudowa a safiyarta bata da kwallelen haskenanan.”
Amma fa a sani wannan ba ka’ida bace tabbatacciya, zaa iya samun sabani, hana kuma wasu yankunan Duniya basu da yanayi irin wannan da aka fada.
ALLAH NE MASANI
Dan uwanku
Tahir Lawan Muaz Attijaneey
08060306021
08099475470
20 ga Ramadan 1437
25 ga June 2016

Comments
Post a Comment