Posts

Showing posts from July, 2017

SHARUDDAN DARIKAR TIJJANIYA

Image
Tahir Lawan Muaz Attijaneey   Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci ya tabbata ga Annabi Muhammad da Alaye da Sahbbansa.   Bayan haka kamar yadda kowa ya sani cewa wannan darika ta tijjaniya a tsare komai nata yake, babu wani abu komai kankantarsa face yana da tushe a cikin Alkuranai ko Sunna ta Annabi saw ko kuma wani zance shararre na malamai ababan dogaro a musulunci, wannan ne ya sanya Darikar ma ake mata kirari da Darikar Malamai. Zamu iya ganin hakan balo balo cikin yadda aka tsara wuridanta da zikiranta da ma uwa uba rukunai da ladabanta. A wannan makala tamu zatai duba ne ga Sharuddan wannan Darika ta Tijjaniya wadanda gaggamn masana a wannan Darika suka cirodaga Maulanmu Shehu Ahmadu Tijjani RTA da Almajiransa. A cikin Littafin RIMAHU na Sarkin Muminai kuma Jagoran Daular Tijjniyya a Africa ta yamma sayyadi Umar Al Futy ya ambata cewa Darikar Tijjaniya tanada sharudda 23 ne, amma maulammu shehu Abubakar Atiku Sanka a Littafinsa IFADATUL MUR