SHARUDDAN DARIKAR TIJJANIYA



Tahir Lawan Muaz Attijaneey

 
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci ya tabbata ga Annabi Muhammad da Alaye da Sahbbansa.
 Bayan haka kamar yadda kowa ya sani cewa wannan darika ta tijjaniya a tsare komai nata yake, babu wani abu komai kankantarsa face yana da tushe a cikin Alkuranai ko Sunna ta Annabi saw ko kuma wani zance shararre na malamai ababan dogaro a musulunci, wannan ne ya sanya Darikar ma ake mata kirari da Darikar Malamai. Zamu iya ganin hakan balo balo cikin yadda aka tsara wuridanta da zikiranta da ma uwa uba rukunai da ladabanta.
A wannan makala tamu zatai duba ne ga Sharuddan wannan Darika ta Tijjaniya wadanda gaggamn masana a wannan Darika suka cirodaga Maulanmu Shehu Ahmadu Tijjani RTA da Almajiransa.
A cikin Littafin RIMAHU na Sarkin Muminai kuma Jagoran Daular Tijjniyya a Africa ta yamma sayyadi Umar Al Futy ya ambata cewa Darikar Tijjaniya tanada sharudda 23 ne, amma maulammu shehu Abubakar Atiku Sanka a Littafinsa IFADATUL MURID yace guda 29 n3, wanda zamuga Karin kusan sukan zamo wani kari ne na ladubba. kuma acikinsu duk sun kawo sharudda da suke komawa kan mai karba da wadanda suke komawa kan mai bayarwa. Misali Sharadai na farko yana komawa ne kan wanda ya bayar da darika wato:
1.      Mai bayarwarya zamo yana da izini sahihi daga na sama dashi hark an Maulana Shehu Tijjani rta. Domin yankewar sanadi ko karba wurin wanda baida izini yana nuufin yankewar kwaranyen mutum daga sama ne, wato kamar watahanya c eta famfo wadda in aka yanke kafin ftushen ruwa to baza a samu abinda yake tahowa ba.
2.      Shi wannan yana komawa kan mai karba ne wato dole ya zamo baya riko da wani wuridi na sauran waliyyai, in kuma yana yi to ya ajiye sannan a bashi AHDI na Tijjaniya. Wannan ma ba yana nufin an wulakanta da sauran waliyyai bane, sam!! Maulana shehu Ahmadu Tijjani yayi riko da wurdai na waliyyai, amma sadda Manzo saw ya lakkana masa Tijjaniyya said a ya umarce shi day a ajiye duk wani wurdi. Sannan hakan baya nuna cewa Tijjaniya bata amfani da wasu wuridai na waliyyai ba, domin akwai wasu adduoi da maulanmu shehu Tijjani yai amfani dasu ya kuma dora mabiyansa akai kamar HIZBIL BAHRI ta Imam Shazali, duk da cewa suma wadannan adduoi saida Annabi saw yai masa izininsu ba tare da wata wasitah ba.
3.      Dole ne duk wanda yake Batijjane yabar Ziyartar wasu Waliyyai banda na Tijjaniy, krayayyu ne ko Matattu. Shima wannan Sharadi ya jawo cece kuce yadda har wasu ke kallonsa a matsayin ya sabawa sharia datai horo da ziyartar musulmi ga junansa da barin yankewa, amma gamai lura zaiga cewa sam hakan bai saba da shariah ba, kasancewar ba cewa akayi a yanke ba, hasali ma zamuga cewa ana ziyarar juna amma ziyarar da ake Magana itace ziyarar nemanMadadi ko tabarruki wadda wannan abune sananne a da'irah ta Sufanci, zamuga shuwagabanni a Tijjaniya sunada alaka mai karfi tsakaninsu suna ziyartar Junakamar alakar Shehu Atiku da Shehu Maihula da Jagororin Kadiriyya a Kano, da makamantansu, haka alakar Sayyadi Hafiz Almisry da Manyan Sufaye a Kasar Misra.
4.      Dawwama akan Salloli Biyar na Farillah da sharuddansu sanannu a littafan Fikhu, domin duk mai son Shiga halarar Ubangiji to sune matakai na farko da zai fara dasu.
5.      Dawwamar soyayyar Shehunsa a kodayaushe batare da yankewa ba har mutuwa. Wannan abune mai girma day a zamo dole ga dukkan muridi, kuma asali ne tabbatacce a dukkan darikun da suke rigayi Tijjaniya,
6.      Rashin aminta daga makarun Ubangiji: maana kada mutum ya rudu da cewa tunda nai riko da Tijjaniyya na tsira, Allah swt yana cewa " shin sun aminta daga makarun ubangiji ne? ai kuwa ba mai aminta dafgga makarun Allah sai mutane tababbu" don haka abinda yanzu yaje faruwa na fariya day an uwa suke na samun makamai da ganin an samu tsira abune mai hadari, domin hanya mai falala da yawa tana da kayoyi da santsi, da zarar wani rashin ladabi ya gifta ana iya samun matsala. Shehu tijjani yana cewa "duk wanda ya somu har ya mutu kan haka zaa tashe shi cikin amintattu a kan kowane hali yake,matukar bai sanya rigar amici daga makarun Allah ba."
7.      Kada ya sake a samu wani abu na Kiyayya a zuciyarsa a janibin shehu Tijjani rta balle ace ma takai ga zagi ko bakar Magana.
8.      Dawwama akan wridin har mutuwa: shima wannan sharadi ne na Tijjaniya cewa baa fita domin bakance da Allah yake yabon masu cikashi. Wasu na ganin wannan sharadi abune day a saba da shariah amma sam abun bah aka yake ba, domin aduk sadda ka daukarwa kanka wani lazimi na ibada don kanka to ya zamo maka wajibi. Shi yasa Annabi saw yake cewa "cikin hadisin Sayyadah Aisha da Bukhari da Muslim suka rawaito "ku kallafawa kanku abinda zaku iya domin Allah bazai gajiya ba ma dammar bakugajiba kuma." Hakanan zamuga yadda  Annabi saw sukayi da Abdullahi bn Amru Bnil As rta yadda Manzo saw ya nuna masa ya rage yawan Azumi da Tsayuwar dare sai ya kafe kan cewa ai zai iya, lokacin yana jin samartakarsa, amma daya tsufa sai ya zamo yana jin jiki kan yayi abun da yayi alakwarin yinsa tun yana sayrayi sai yake cewa "inama na karbi saukin da Annabi saw yayi dani na karba" kaga hakan na nuna in ka shiga wani aikin alkheri zaka iya shiga da niyyar bazaka bari ba har karshen rayuwarka.
9.      Kudurcewa: wato mika wuya ga zantukan Shehu Tijjani ba tare suka ba.
Shehu Atiku yana fada a wata kasidarsa ta Hausa daya nazzama sharudan Tijaniya:
Kazam I'itikadi kabar intikadi ** li aqwali af'ali Tijjaniya
 Wannan Asali ne daga asalan sufanci da kowace darika tazo dashi ba wai Tijjaniya kawai ba, shi yasa zakaji ana cewa in ka abokanci sufi to ka aboce shi da sallamawa, don kuwa in babu wannan sallamawar to bazaar amfana ba, kamar yadda ya faru tsakanin Khidr da Musa. Annabik saw yana cewa Allah yajikan dan uwana Musa AS da yayi hakuri da Khidr day a nuna mana abubuwan ban mamaki masu yawa"
10.  Wannan sharadin ciokn na baya ne wato in ka kudurce to kada kayi Naqadi wato suka cikin harkokin Darikar da falalolinta.
11.  Ya zamo shima Muridin ya samu mai laqqanawa sahihi daga wani abin koyi babba a Darika, wannan sharadi wata falala ce da ake so kowane muridi ya samu don Annabi saw sadda ya gayawa Shehu Tijani wasu falaloli na wanda suka karbi darika a hannunsa sai yace da Annabi saw shi shin wannan falala ta kebanta ne da wanda ya karbi darika a hannuna mubasharatan ko har wanda ya karba ta hanyar wani? Sai Annabi saw ya amsa da cewa "duk wanda kai masa Izini a wannan wuridi shima yayiwa wani tro kamar ya karba ne daga gareka ne baki da baki"
12.  Kada wani ya bada Darikar nan sai yana da izini sahihi don yin hakan yuana sanya mutum yai mummunan karshe Allah ya karemu. Shehu Atiku yana fadi a cikin wannan sharadi:
Kabar yin (TASADDURU) shine gabata ** Cikin bada wuridi na Tijjaniya
Fa sai inda izniy sahihi kawiyyi ** Gurin shaikhuna ka ga mai bibiya[1]

13.  Girmama duk wanda ya danganta d Shehu Tijjani da Darikarsa musamman Manyan Jagororin Darikar.
14.  Bin iyaye: shima sharadine wanda yake da karfin gaske, don ba yadda zaka amfana da romon Darikar Tijjaniya matukar iyayenka suna fushi dakai ko kana saba musu.
15.  Ka nisanci zama da Munkirai kamar yadda Shehu Atiku yake cewa:
Kazam nisatar zumratul munkirina ** Da mai intikadi cikin zuciya [2]
Wannan ma abune da yake tabbatacce a shariah, domin ya tabbata a hadisi cewa "mai zama da muatanen banza kamar mai zama ne da mai hura zuga zugi, mai zama da mutan kirki kuma kamarc mai zama ne da mai sayar da Turare" Bahaushe ma na cewa zama da Madaukin Kanwa shike kawo farin kai.
16.  Taruwa don karanta wazifa da zikirin Jumaa bayan Sallar Laasar din Ranar Jumaa, ai sharadine a hadu don yin wazifa da zikrin Jumaa a inda yake akwai yan uwa da zaku hadu kuyi tare, sannan in babu wani uzuri karbabbe.
Zikrin Jumaa A zawiyar Sheikh Tijani Usman Zangon Bare Bari Kano

17.  Kada a karanta Jauharatul Kamali saida Alwala, domin Manzo saw yana halartar duk yadda aka karanta ta tare da Sahabbansa hudu wato khalifofinsa Rashidai musamman sadda akazo karanta Jauhara ta Bakwai.
18.  Mutum ya zamo baya yankewa yan uwansa Musulmi Musamman Tijjanawa, Shehu Tijjani rta yana cewa ku ziyarci juna ku sada Zumunci cikin Allah kuyi biyayya cikin Allah gwargwadon iko.
19.  Fuskantar Alkibla da dukkan jikinsa lokacin yin zikiri ko wurdi tun daga faraway har gamawa, saidai in ana cikin da'irah ne to kaga wannan dama wasu zasu zamo suna kallon bangarori manbambamta. Sannan shi tsarin zaman zikirin zai iya zamowa da'ira ko kuma ayi layi biyu wasu na fuskantar wasu, duk da mu a nan kasashen namu munfi yin da'ira wato zagaye wato CYCLE.
20.  Sirrantawa cikin wuridi, amma lallai shi mai yin ya jiyar da kansa lafuzzan wurdin.
21.  Barin wulakantawa da wurdin kamar jinkirtashi ba tare da Uzuri ba,
22.  Tsarkin jiki dana tufafi lokacin zaman wuridin ko zikirin
23.  Sai Tsarkin wurin da zaka zauna.
24.  Rashin yin Magana lokacin yin zikirin ko wurdin sai in da wata larura da zata tilasta ai maganar shima kada ta wuce kalma daya biyu haka. Sai dai kamar amsawa iyaye shi ko ya wuce haka yana inganta.
25.  Suturce Al'aura kamar yadda yake a tsarin Sallah.
26.  Haroro lafuzan zikirin da maanoninsa ga wanda zaia iya sanin maanonin.
27.  Hararo surar Manzon Allah saw ko Shehu Tijjani rta ko khalifofinsa manya, in zai iya kai koda shehinka in ka gaza halarto a zuciyarka don himmarsa ta fizge ka zuwa halarar Shehu tijjani da Manzon Allah saw.
28.  Tsarkin kari dana dauda ko da Alwala ko Taimama sai dai wajen karanta Jauhara ita said a tsarki na Ruwa.
29.  Niyya: saboda a musulunce ayyuka basa tabbata said a Niyya, maanar niyya anan shine ka tsarkake niyyarka lokacin zikirin ka yishi saboda neman kusanci da Allah da tsarkake zuciyarka da kuma hidma ga manzon Allah saw.

Wadannan sunesharudda na Tijjaniya 29 da muka rairayo daga littafin Rimahu na Shehu Umar Futy  daya kawo sharuda 23 da Ifadatul Mureed na Shehu atiku da ya kawo 29.
A karshe Shehu Atiku ya raba sharuddan izuwa gida sharuddan inganci da barin daya ke bata wuridi kamar: tsarkin kari tsarkin dauda surce al'aura barin Magana da Niyya, sai wasu da in ka bari sun fitar dakai daga Darikar ma wato sune:rashin ziyarar waliyyai in banda na Tijjaniya sai barin wuridin bayan ya karba sai hadashi da wani wurdin. Wanda ya bar wadannan to ya yanke alakarsa da Shehu Tijjani rta. Akwai kuma sauran sharuddan sharudda ne na kamala.
Da fatan Allah ya dawwamar damu cikin wanna darika ya bamu ikon kiyaye sharuddannan ya bamu amfani da falalolin da aka tanadarwa masu bin wannan tafarki.
Wassalam

Dan uwanku
Tahir Lawan Muaz Attijaneey
08060306021
20 Rajab 1438
16-Apr-17




[1] - kawiyyi = mai karfi
[2] - zumrtul mukirina = jama’a masu inkari da musu, damai intikadi = da mai suka

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY