Posts

Showing posts from January, 2018

MU KOYI LARABCI

RUKUNAN MAGANA A LARABCI (Part of Speech in Arabic) Zance ko Magana a larabci bata fita daga daya daga cikin abubuwa uku: 1. SUNA-ISM- Noun 2. AIKI- FI;IL-Verb 3. HARAFI -HARF- Compound Letters Sabanin a harshen Turanci da yake da bangarori Takwas shi Larabci ya hade wasu yankuna cikinm wasu, misali Siffatau Adjectives suna karkashin Suna, da makamantan haka.Yanzu bari mu dauki kowane daya muga yaya suke: SUNA Suna shine wata kalma da bata bukatar sai an hadata da wata don ta bada maana, ko muce duk Kalmar da ake kiran wani Mutum ko Wuri ko Aiki da ko wani abu da ita, Misali: SUNAYEN MUTANE: محمد، زيد حبيب طويل SUNAYEN WURARE: مكة مدينة كنو أبوجل أمريكا نيجيريا SUNAYEN WASU ABUBUWA: الريح الفرح الحزن TA YAYA ZAMU GANE SUNA? Shi suna yana da wasu alamomi kamar 4 da ake gane shi dasu kamar haka: 1. Shigar Tanwini ca karshensa wato a samu faduwar fatha ko ruf’a ko kisra: Misali:  محمدٌ محمدًا محمدٍ 2. Shigar HAFDHA wato KISRA a karshen Suna, misali kace: ذهبت إلى البيتِ Msab