MU KOYI LARABCI
RUKUNAN MAGANA A LARABCI (Part of Speech in Arabic)
Zance ko Magana a larabci bata fita daga daya daga cikin abubuwa uku:
1. SUNA-ISM- Noun
2. AIKI- FI;IL-Verb
3. HARAFI -HARF- Compound Letters
Sabanin a harshen Turanci da yake da bangarori Takwas shi Larabci ya hade wasu yankuna cikinm wasu, misali Siffatau Adjectives suna karkashin Suna, da makamantan haka.Yanzu bari mu dauki kowane daya muga yaya suke:
SUNA
Suna shine wata kalma da bata bukatar sai an hadata da wata don ta bada maana, ko muce duk Kalmar da ake kiran wani Mutum ko Wuri ko Aiki da ko wani abu da ita, Misali:
SUNAYEN MUTANE: محمد، زيد حبيب طويل
SUNAYEN WURARE: مكة مدينة كنو أبوجل أمريكا نيجيريا
SUNAYEN WASU ABUBUWA: الريح الفرح الحزن
TA YAYA ZAMU GANE SUNA?
Shi suna yana da wasu alamomi kamar 4 da ake gane shi dasu kamar haka:
1. Shigar Tanwini ca karshensa wato a samu faduwar fatha ko ruf’a ko kisra: Misali: محمدٌ محمدًا محمدٍ
2. Shigar HAFDHA wato KISRA a karshen Suna, misali kace: ذهبت إلى البيتِ Msabanin FI’ILI shi bai karbar kisra HARFI kuma shi bai canjawa sam.
3. Shigar ALIF da LAM na Maarifa a farkonsa: البيت الكبير الحق
4. Shi suna yana karbar Harafai da suke sa ayi masa Kisra kamar misalign da muka bayar a lamba ta 3.
5. Wasu masana larabci sun kara da cewa shi kadai ne a rukunan zance yake karbar YA TA KIRA ياء النداء، misali kai kira kace
يا إبراهيم يا نوح يا داوود.
Bari mu dakata anan sai sati na gaba.
Am ismun
ReplyDeleteWal fiilun
Wal Harfun..