Posts

Showing posts from September, 2018

TARIHIN SHEIKH UBA SUFYAN

Image
TARIHIN SHEIKH UBA SUFYAN NASABARSA: Babban Sufi Waliyyi Masanin Allah Sheikh Sufyan, anai masa lakabi da Abu Nazeer, ko Kaabar Sharifai, wanda akafi sani da Uba Sufyan Dorayi dan Muhammadul Auwal Dan Sufyan. Asalin kakanninsa yana kaiwa ga daya daga cikin malamai da Shehu Usman dan fodiyo ya aiko Kano lokacin Jihadi, Akwai wani daga kakanninsa mai suna Jakadan Dutse wanda gidansa Shahararre ne a unguwar Mandawari ana kiransa Gidan Dan Maje, wanda wani gidane da aka sani da harkar sarauta har kan kakansa Jakadan Kutama. Mahaifin Shehu Uba Sufyan yayi kaura daga Mandawari bayan daya dandana karatu, inda ya koma orayi babba inda anan aka haqifi Shehu Uba Sufyan. HAIHUWARSA DA TASOWARSA An haifi Sheikh Uba Sufyan a Hijrar ta 1359 wajejen shekara 1934 miladiyya, a Dorayi Babba dake birnin Kano Nigeria, Ya taso a hannun mahaifinsa day a fara nuna masa hanyar Ilmi da Tarbiyya, ya sauke Alkurani yana shekara 10 ya karanci sashin ilmai na Fiqhu da Larabci a hannun mahaifinsa kafin y