TARIHIN SHEIKH UBA SUFYAN

TARIHIN SHEIKH UBA SUFYAN


NASABARSA:
Babban Sufi Waliyyi Masanin Allah Sheikh Sufyan, anai masa lakabi da Abu Nazeer, ko Kaabar Sharifai, wanda akafi sani da Uba Sufyan Dorayi dan Muhammadul Auwal Dan Sufyan.
Asalin kakanninsa yana kaiwa ga daya daga cikin malamai da Shehu Usman dan fodiyo ya aiko Kano lokacin Jihadi, Akwai wani daga kakanninsa mai suna Jakadan Dutse wanda gidansa Shahararre ne a unguwar Mandawari ana kiransa Gidan Dan Maje, wanda wani gidane da aka sani da harkar sarauta har kan kakansa Jakadan Kutama.
Mahaifin Shehu Uba Sufyan yayi kaura daga Mandawari bayan daya dandana karatu, inda ya koma orayi babba inda anan aka haqifi Shehu Uba Sufyan.
HAIHUWARSA DA TASOWARSA
An haifi Sheikh Uba Sufyan a Hijrar ta 1359 wajejen shekara 1934 miladiyya, a Dorayi Babba dake birnin Kano Nigeria, Ya taso a hannun mahaifinsa day a fara nuna masa hanyar Ilmi da Tarbiyya, ya sauke Alkurani yana shekara 10 ya karanci sashin ilmai na Fiqhu da Larabci a hannun mahaifinsa kafin ya rasu shehi yana dan shekara 15.
NEMAN ILMINSA DA SUFANCI
Shehi Uba Sufyan yayi karatu a hannun shehunan malamai da ama wasu yayi karatun ilmi na zahiri na Ibada wato fiqhu a Larabci  wasu kuma ya karbi ilmin sufanci da tarbiyya.
Bayan wafatin babansa yai karatu a wajen Malam Ishaq ina ya riki littafin IZIYYA a Shuara ta wakokin jahiliyya da Daliyar Ibn Nasir da Ishriniyya, sannan yayi karatun Ajuruma da Milha ta larabci da Tajridin Sahihil Bukhari duka wajen Ahmadu Rufai na Jarkasa haka nan ya karanta Makamatul Hariri,
Haka shehu yayi dalibta a wajen Mahiru Malam Hamid wanda ya shayar ashi Sufanci a karance.
Hakanan Sheikh Malam Isa shima shehu ya sha sufanci a hannunsa  dama ilmin usul na mazhabobi hudu.
Daga Bajiman Malaman da suka sanya shi a suluki na Tijaniya kuwa akwai Maulanma Shehu Abubakar Atiku Sanka, da Shehu Adamu Azare,  da Sheikh Hasan Dam.
  KOYARWARSA GA HALITTA
Shehu Uba Sufyan ya kafa Makaranta da zawiya don Tarbiyyar bayi zuwa ga Allah, akwai makaranta a yara suke karatu, wanda galibi yaynsa a almaajiransa ke kula da koyarwa cikinta. Sannan shehu yana da tsarin koyarwa ta azure da tarbiya ta Darika ga manya, sannan ga karatun Ashafa da Azumi.
Kuma dubban Almajirai sun fiuta ta karkashinsa, wana ba sai mun tsaya kirgosu ba don yawansu.
TALIFANSA
Shehi yana a Gomman Littafai da rubuce rubuce da wakoki na Larabci da wasu ma a Hausa, kadan daga ciki akwai littafinsa na TARIHIN ANNABI SAW Irshadil Mustarshidina, a sufanci kuwa akwai SIFATU AULIYA”I, da Tuhfatul Muhibbin, da Sabilul Falah, da Dalilul Al mutaqarrib ila al hadrat Alqudsiyya wanda na salatan Annabi saw ne, a wakoki kuwa yana da yabon Annabi saw da Shehu Tijjani da Marsiyar da yayiwa Shehu Ibrahim Inyass.
WAFATINSA
Shehu ya koma ga Allah ranar 29 ga Augusta 2018 daiai da 18 ga Zulhijja 1439, a wani Asibiyti dake kasar Misra. bayan rashin lafiya mai tsayi wadda bata hanashi tsayawa da duk abubuwa da aka saba ba  na shiyarwa zuwaga Allah.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY