Posts

Showing posts from November, 2018
Image
RADDI AKAN LITTAFIN: AS-SU’ALATUN NAJERIYYA “ANAS AN-NASHWAN” (TAMBAYOYIN NAJERIYA) ***** SHEIKH HAMDULLAH HAFIZ AS-SAFTIY  ( 1 ) GABATARWA BismilLahir Rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah.. Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Manzon Allah, da Alayensa da Sahabbansa, da wadanda suka shiryu da shiriyar da ya zo da ita. Bayan haka: A duk sanda muhimman kalmomin Musulunci suka cakude da juna, to kuwa rarrabe su ta hanyar bayyana ma’anoninsu na ainihi ya zamo wajibin da ba zai iya lamuntar wani jinkiri, ko nawa ba; kuma haka zai kasance ne da zimmar yaye duhu da rudanin da suka hana fahimtar ma’anoninsu tun farko.. A irin wannan yanayi, ya kamata mu aminta da cewa tunanin mutane a kasashen Musulmai ya gurb’ata da wasu cututtuka, an damalmala abubuwa, an kuma kasa rarrabe zare da abawa, manufar wadanda suka yi hakan kuma ita ce: kawo karshen cigaban Musulunci, da raba al’umma da hakkokinta gami da arzikin da Allah ya yi mata. Lallai bayyana magani da kum...