RADDI AKAN LITTAFIN:
AS-SU’ALATUN NAJERIYYA
“ANAS AN-NASHWAN”
(TAMBAYOYIN NAJERIYA)

*****

SHEIKH HAMDULLAH HAFIZ AS-SAFTIY

 ( 1 ) GABATARWA

BismilLahir Rahmanir Rahim

Godiya ta tabbata ga Allah.. Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Manzon Allah, da Alayensa da Sahabbansa, da wadanda suka shiryu da shiriyar da ya zo da ita.
Bayan haka:

A duk sanda muhimman kalmomin Musulunci suka cakude da juna, to kuwa rarrabe su ta hanyar bayyana ma’anoninsu na ainihi ya zamo wajibin da ba zai iya lamuntar wani jinkiri, ko nawa ba; kuma haka zai kasance ne da zimmar yaye duhu da rudanin da suka hana fahimtar ma’anoninsu tun farko..

A irin wannan yanayi, ya kamata mu aminta da cewa tunanin mutane a kasashen Musulmai ya gurb’ata da wasu cututtuka, an damalmala abubuwa, an kuma kasa rarrabe zare da abawa, manufar wadanda suka yi hakan kuma ita ce: kawo karshen cigaban Musulunci, da raba al’umma da hakkokinta gami da arzikin da Allah ya yi mata.

Lallai bayyana magani da kuma kokarin yin amfani da shi, a irin wannan yanayi ba zai wadatar ba, dole sai an yi kokarin tsaftace wannan yanayin daga kwayoyin cuta da su ne suke yada wannan garnakakar annoba da take yi wa samuwar al’umma barazana tun daga tushe.

Lallai Allah ya jarabci kasashen Musulmai –kai da ma duniya baki daya- a wannan zamanin da kungiyoyin da suke kafirta Musulmai, da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka yadu a ko’ina a fadin duniya, suna shekar da jini, suna kuma rarrabu mutuwa ga kowa da kowa, suna kuma shigar da tsoro gami da razani a cikin zukatan fararen hulan da ba su ji ba, ba su gani ba, sun daga tutar “Hawarijawa”, har dai suka b’ata wa Musulunci suna, suka kuma lullub’e shi da karai-rayi da kage da kuma b’atar da mutane, suna kuma yin hakan ne da nufin b’ata masa suna a wasu lokuta, a wasu lokutan kuma jahilci ne ya tsunduma su a cikin wannan rami.

Har yanzu wadannan kungiyoyi ba su daina yada karai-rayi akan Musulunci da Musulmai ba, sun kamu da cutar ganin bambancinsu da sauran mutane, suna yi wa sauran Musulmai girman-kai da gani-gani; suna raya cewa su ne kadai masu addini da imani, wai kuma su ne masu jahadi, kuma wai su ne za su sami tsira a ranar alkiyama.. Babu shakka maganar Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ce ta tabbata a kansu, inda yake cewa: ((Idan wani mutum ya ce: Mutane sun halaka, to kuwa lallai shi ne yafi su halaka..)) [Muslim ya ruwaito].

Wadannan kungiyoyi sun yi duk abin da za su iya wajen jawo matasa Musulmai, suna amfani da su wajen zartar da manufofinsu da suka tsara, suna yaudararsu da sunan Musulunci, sun kuma fake da kishi gami da son da matasan suke yi wa addini. Babban abin da yake kawo masu cikas a wannan aika-aika nasu shi ne: cibiyoyin addini da suke da tarihi mai kyau wajen hidimta wa ilmomin addinin Musulunci, saboda haka sai suka yi ta kokarin sanya wa mutane shakku akansu, suna masu kawar da zukatan mutane ga barinsu ta hanyar b’ata masu suna, sun kuma yi hakan ne domin su sami daman cin-karensu-ba- babbaka wajen yaudarar al’umma da sunan addini, duk wani mai hankali ya san irin soke-soken da cibiyar addinin Musulunci ta AL AZHAR ta fuskanta a hannun wadannan mutane masu gurb’atattun manhajoji, a wasu lokuta su jefe ta da ci-baya da kauyanci, ko kuma su ce: ai ta yi nesa da manhajin “Salaf”, ko kuma su ce: ai malaman gwamnati ne a wasu lokuta!..

Babu shakka wasu masu ajenda da maslahohi na kwadayi a cikin kasashenmu –na ciki da na waje- sun taimaka wa wadannan kungiyoyin, har ya zamo suna da malamansu na musamman da suke komawa zuwa gare su, manufarsu kuma ita ce: bai wa abu mafita, ba wai bayyana yanda yake a ainihin Shari’a ba, da kuma jingina aika-aikansu da Nassi, ba wai auna shi da Nassi ba, a dalilin haka sai gurb’ataccen Fikhu ya fara bayyana a cikin al’umma, kai abin ma har ya kai ga sanya magana a bakin Alkur’ani Mai girma da Hadisan masu daraja, maganar da ba su taba furta irinta ba, sai muka ga litattafai da wadannan kungiyoyin suka buga suna yawo, suna gurb’ata fahimtar al’umma game da addini, suna kuma zab’an Nassoshin Shari’a domin su lullub’e laifukkansu, suna yin haka ne da zaton cewa malaman al’umma ba za su bankado wannan makircin nasu ba, sai dai ina.. abin ba kaman yanda suka zata ba ne..

Da ikon Allah Madaukakin Sarki, a wannan silsilar za mu rusa wadannan fahimtoci masu rusa al’umma, za mu kuma yi haka domin yin nasiha saboda Allah da Manzonsa da sauran Musulmai, mun fara da yin raddi akan wani dan karamin littafi da “Mu’assatut -Turasil Ilmiy” ta buga da sunan “AS SU’ALATUN NAJERIYYA” (wato: TAMBAYOYIN NAJERIYA), Littafin ya kunshi amsoshin tambayoyi ne guda hudu, da suka tab’o muhimman mas’aloli guda hudu da wadannan kungiyoyi suke amfani da su wajen tallata karkatattun karantarwarsu ga matasa, da nufin jawo su cikinsu, wadannan mas’aloli su ne: kafirta Musulmin da yake zaune a kasashen da ba na Musulmai ba, da Mas’alar yin garkuwa da mutane “at-Tatarrus”, da mas’alar kafirta wanda ya amshi katin zama dan kasa a kasar da ba ta Musulmai ba, da kuma kai wa makarantun yara hari, da tayar da bama-bamai a cikinsu saboda suna karantar da wasu darussa da suka sab’a wa addinin Musulunci a ganinsu..

Wanda ya amsa wadannan tambayoyi wani ne da suka yi masa lakabi da: fadhilatus Sheikh al-Mujahid Abu Malik al-Tamimiy (Anas an-Nashwan), a amsoshin nasa ya cakuda abubuwan da ba a cakuda su, ya kuma kawo abubuwan da ba su da wani suna a wurin masu hankali in ba hauka ba, domin ya jingina muminai da karfici, a gefe daya kuma ya jingina masu laifi ‘yan ta’adda da jahadi, ya hada wa bayi kashi, yana kuma kira zuwa ga hanyar zalunci da b’arna.

Na tattaro amsoshi da raddi akan wannan karai-rayi nasa ne daga maganganun malamai, kuma shugabannin addini, saboda haka nawa a nan kawai bai wuce nakalto mafi darajar abin da suka tabbatar ba, ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya sanya amfani da karb’uwa a cikinsa.. lallai Allah shi ne majib’incin al’amurranmu, madalla da majib’incin al’amurra Allah, wala haula wala kuwwata illa bilLah, WasallalLahu alai Sayyidina Muhammadu wa ala alihi wa sahbihi wa sallam.

******

Tarjama: Saleh Kaura

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY