Posts

Showing posts from July, 2020

RAQDA'U: WAKAR KOYA LARABCI TA SHEHU ATIKU SANKA

Image
I’anatul Bulada’I Bil Manzumatur Rakda’i [1] إعانة البلداء بالمنظومة الرقطاء SHEHU ABUBAKAR ATIKU SANKA  daya ne daga Manyan Malamai kuma waliyya Sufaye da ya rayu a birnin Kano tsakanin shekarun 1909 ko 1905 zuwa 1974, yana da Rubuce rubbuce dadama a fannonin Ilmi na Addini da kuma dubban Almajirai. Wannan Wakar dai Shehi ya tsarata ne saboda koyar da kalmomin Larabci ga Balidai kamar yadda ya kirata daI'ANATUL BULADA'I BIL MANZUMATIR ARRAQDA'I Fassarar wannan SHINE (Taimakon Balidai da waka mai rodi-rodi) Asalin Kalmar Raqda’u tana nufin Micijiya mai rodi rodin KALOLIN Fari da Baki a jikinta. Ya sanyawa wannan waka ne saboda a cikinta akwai baki akwai fari maana Jan baki da Fassara kamar yadda zaa gani kuma shehin zai fada a karshen kasidar baiti na 100 inda yake cewa: (FA KULLU MA FIHA DA FASSARARSA                   INDAI KA DUBA SAI KASAN SUNANSA) wannan kasida da wasu zasu fito nan gaba insha Allahu a Littafin Diwanin wakokin Hausa na Shehi Atiku mai suna: Bara