RAQDA'U: WAKAR KOYA LARABCI TA SHEHU ATIKU SANKA
I’anatul Bulada’I Bil Manzumatur Rakda’i[1]
إعانة البلداء بالمنظومة الرقطاء
SHEHU ABUBAKAR ATIKU SANKA daya ne daga Manyan Malamai kuma waliyya Sufaye da ya rayu a birnin Kano tsakanin shekarun 1909 ko 1905 zuwa 1974, yana da Rubuce rubbuce dadama a fannonin Ilmi na Addini da kuma dubban Almajirai.
Wannan Wakar dai Shehi ya tsarata ne
saboda koyar da kalmomin Larabci ga Balidai kamar yadda ya kirata daI'ANATUL BULADA'I BIL MANZUMATIR ARRAQDA'I Fassarar wannan SHINE (Taimakon Balidai da waka mai rodi-rodi) Asalin Kalmar Raqda’u
tana nufin Micijiya mai rodi rodin KALOLIN Fari da Baki a jikinta. Ya sanyawa wannan
waka ne saboda a cikinta akwai baki akwai fari maana Jan baki da Fassara kamar
yadda zaa gani kuma shehin zai fada a karshen kasidar baiti na 100 inda yake cewa:
(FA KULLU MA FIHA DA FASSARARSA
INDAI KA DUBA SAI KASAN SUNANSA)
wannan kasida da wasu zasu fito nan gaba insha Allahu a Littafin Diwanin wakokin Hausa na Shehi Atiku mai suna: Bara ga Tijjani .
Ga Wakar:
1 Alhamdulillahi mugode Allah *
Mu’iununa mataimakinmu jallah
2 Summassalatu da muwo salati
* Ala rasulillahi zissalati
3 Sannan salami da’imiy jamili *
Alaihi m’a ashbin lahu wa’ali
4 Waba’adu bayan wanga yagabata *
Yarabbana ka bani tau butaka
5 Aya akhliy ya dan’uwa khaliyliy *
Maqaunacina, sayyadi jaliyliy
6 Haka: riqe kasiyadatan kasiydah *
Muiynatan, maitaimako mufiydah
7 Mai fa’idah ga dukka dan bahaushe *
Zi’ujmatin baubawa bai da harshe
8 Ya’alamu yasan mataquuli mai kace
Yaquulu yace al’sasu tarkace
9 Inkila in ance wamal insanu *
Yace mutum wa ’yan’uwa ikhwanu
10 Wa’alam sanii, summah fadhan kiyaye
Unzur kaduba wakshinfan kayaye
11 imshi tafi latardha kar kayarda *
Fihamilhu wadrah dauki jeka yadda
12 Kursiy Kujera, inkace Sariru *
Cene Gado, ce mai gani basiru
13 Wabi’itu na sayar sharaitu na saya *
Waji’itu nazo wahidun guda xaya
14 Mashaitu na tafi ka ce aqaltu
Ai naciy na qoshi, kace shabi’itu
15 Baddu agwagwa wal’awizizu dinya *
Wa’inturid miknasatu ce tsintsiya
16 Walburru Alkama, wa Gero Dukhnu *
Urzu shinkafa wa mayi samnu
17 Zurratu dawa, inturid nukhalah *
Dusa akance mata la muhaalah[2]
18 Wa kasuwa suuqu wa’ammalmassjidu * Ce ne masallaci wa kun tajtahidu[3]
19 Dhifda’u kwado jam’uhu dhafadi’u *
Dhabbu damo wa fiygi la munazi’u[4]
20 Kududdufa sune akance Biraku *
Wa’in tasha[5] kace da tarko sharaku
21 Abun Uba, Umun Uwace Jaddu *
Kaka wa Bawane sunkace Abdu
22 Wal bahru kogi Nahru qorama *
Wajam’uhu Anharu babu gardama
23 Kum tashi kenan wajlis ka zauna *
Washarab kasha wamdhigan ka tauna
24 Wakful kakulle waftahan ka bude *
Wadkhul shigone summa hid kabude
25 Kuflu Mukulli summa ismu sarka[6] *
Salsalatun walhaqqu gaskiya rika
26 Daru Gida Babun akance Kofa *
Walbaitu Daki watfulan ka tofa
27 Khaidu Zare ne summa Nasju saka *
Sa’altaniy ka tambayeni kaka
28 Ta’ala yaka warji’an ka koma
Watrukhu barshi summa khuz ka kama
29 wal Filu Giwa summa Zi’ibu Kura *
Arnabu Zomo walgubaru Qura
30 Sunan Biri shine sukance Kirdu *
Suna na Fata shi sukan ce jildu
31 Wa Damisa shine sukance Namiru *
Wal asadu zaki sayyidun mustahirun[7]
32 Fa’in turid Gazalu ce Barewa *
Wa hirratun walkiddu kaji kyanwa
33 Wakra’a karanta, waktuban rubuta *
Wamsah ka shafe wastarih ka huta
34 Wasma’a kaji summa-bsiran ka gani
Kul ka fadi summa-a’adini ka bani
35 Wattinu Baure summa Tibnu Kaikayi *
Ukalu ko muce dashi dabaibayi
36 Gurabu ku muce dashi Hankaka *
Wa’inturid ismul Ataani Jaka
37 Wa Akrabu sunanta ai Kunama
* Wal-lahmu ku muce dashi ai Nama
38 Wan-Nakhalu ko itaciyar Dabino *
Wallabnu indanaa[8] mukance Nono
39 Wa sullamun muce dashi Kuranga *
Jidaru ku mu ce dashi Katanga
40 wan-Nuru haske summa Shamsu Rana *
Ahsasu Bukkokin gida na zana
41 Dariku ko sunansa gunmu hanya *
Wad-Dumu ko muce dashi Giginya
42 Yadanu ko muce dasu fa hannuwa *
Wal Uznaani ce dashu ai kunnuwa
43 Harshe na baki ce dashi Lisanu *
Idanaduna ku ce dasu Ainanu
44 Sannan Hakora ce dasu Asnanu *
kafafuwa ka ce dasu Rijlanu
45 Badnu ciki Hanji kace Misraanu *
Duwaiwaya ce masu Ilyatanu
46 Wuka Sikkinu summa Musa aska *
Saifu Takobi summa Rihu Iska
47 Naru wuta Dukhanu ko Hayaki *
Wa’inturid kace da harbu yaki
48 Suldanu Sarki, wal Amiru Hakimi *
Shurdiyyu Dogari Shuja’u Jarimi
49 Sunan takarda sukance Kirdasu *
Wa gatari shine sukance Fa’asu
50 Sunan Magirbi sukance Ma’awilu *
Mai tambaya shine sukance Sa’ilu
51 Warrumhu Mashi summa sahmu Kibiya *
Waddalwu Guga summa hablu Igiya
52 Almakashi shine sukance mikasu *
Da kugiya itace sukance Shassu
53 Turmin daka sunasa Almihraasu *
kararrawa sunanta ai Aljarasu
54 Faifan rufi shine sukance dabaku *
Gumin jiki shine sukance Araku
55 Miyau na baki sai suce Lu’abu *
Dam’u hawaye ce da kyaure Babu
56 Kaskon wuta muce dashi Kanunu *
Kaya na aiki duk suce Maa’uunu
57 Da Gizo gizo sunansa Ankabutu *
Amma fa Kifi shi sukance Huutu
58 Wa’inturid Buzuzu ce masa ju’alu *
Kadangare shine sukance Waralu
59 Timsahu ko shine mukancewa kado *
Nailofariy[9] shi ne mukan cewa Bado
60 Yamamatu shine mukace Hasbiya *
Hirba’u ko muce dashi Hawainiya
61 Sunan tsaka munafika Alwazagu *
Wa Hayyatun Macijiya mai ladagu[10]
62 Jemage ko suce dashi Wadwadu *
Da Majina ta hanci ko Mukhadu
53 Kudan zuma shine sukance Nahlu *
Ruwansa ko shine sukance Asalu
64 Tulun ruwa shine sukance Kullatu *
Sunan Mafici indahum Mirwahatu
65 Walbardu sanyi summa harru zafi *
Lihafu ko muce dashi Mayafi
66 Guda dayan Tantabara Hamamatun *
Su tara shara sai suce Kumamatu
67 Da kaguwa sunansa Assardanu *
Cittar ahu kuzbartil ikhwanu
68 Da Bushiya itace sukance Kunfazu *
Wa Beguwa Duldulu ismuha khuzu[11]
69 Da rataye suce dashi kiladatu
Su basukur suce dasu Darrajatu
70 Tafarnuwa itace sukance Suumu
Ammafa Barci shi sukance Naumu
71 Wa kuwwatun itace mukance Taga
Dur haulahu daurassa zaka zaga
72 Kamisu Riga inkace Ridaa’u
Abin rufa Samaniya Sama’u
73 Wa’inturid Wando kace sirwaalu
Marairayi kace dashi Girbaalu
74 Abin nadi kace dashi Amaamah
Ai Rawani fakun bihi allamah
75 Wa’indahum Kare sukance kalbu
Da zuciya ita ko sukance qalbu
76 Wa’indahum littafine kitabu
Wa Girgije suce dashi Sahabu
77 Wal-Lauhu Allo kalami Al-Kalamu
Dawatu Tawwada wa Tuta Alamu
78 Jam’i na Hula sai muce Kalanisu
Sutara Al-kyabbu suce Baranisu
79 In sukace Namlatu ce Tururuwa
Wal maa’u inkajishi ce dasu Ruwa
80 In sukace Hasiyru ce Tabarma
In sukace Ni’aalu ce Takalma
81 Wal Kidru ko shi mukance Tukunya
In sun kance Misjatu ce Fartanya
82 Wa’indahum Sanhu sukance kuffatu
Rufaniya itace sukance subratu
83 Jam ‘in Duwatsu indahum Ahjaaru
Itatuwa ko indahum Ashjaaru
84 Wa inturid ismul Hisani Doki
Wa’inturid ismul Himari Jaki
85 Dajajatu Kaza wa Dikun Zakara
Wal fa’aru Bera, inturid kasbu kara
86 Tarko na bera shi sukance Fakkhu
Ammafa Bargo shi sukance mukhkhu
87 Sunnan kuda indahum Zubabu
Jam’in tufafi indahumu Siyabu
88 Wal-Kabshu rago summa dha’anu Tunkiya
Bakaratu Saniya wa Ma’azu Akuya
89 Dangin abinci sai suce Da’amu
Dangin Miyaye sai suce Idamu
90 Tandu na kwalli sai suce muk’halatu
Da Kwarkwata itace sukance Kamlatu
91 Jinsi na Rakumi sukance iblu
gudansa ko shine sukance Jamalu
92 Jinsi na Tsuntsuwa sukance Dairu
Wa Rijiya itace sukance bi’iru
93 Misbahu ko shine mukance Fitila
La tat’aban ya dan’uwa bar wahala
94 Turabu Turbaya wa ammar Ramlu
Kul Rairayi wa hankali kul Aklu
95 Tillu tudu wa jam’uhu Tilaalu
Sunan Kufaifai indahum Adlalu
96 Tammat bihamdullahi tai kamala
Ya rabbi na rokeka dan jalalah
97 An tahafazan Nazimaha ya Rabbi
Wanfa’a biha kari’iha ya hasbi[12]
98 Aya akhiy ya dan uwana fajtahid
Fiy hifziha an darshiha fala tahid[13]
99 Fa’innaha nafi’atun gareka
Cikinta ba lugga da ka tsareka
100 Fakullu maa fiyha da fassarassa
Indai ka duba sai kasan sunanasa
101 Na roki Allah dan ya taimakeni
Domin Ma’aiki Musdafa ya bani
102 Iko da budi dan in kara tsari
Mafi da wannan ko kamar na fari
103 Dani nufina tai kamar dari uku
Baitinta ko kuma da goma sha uku
104 Lakinna ashgaluzzamani sun yawa
Sun nannadeni sun rike min hannuwa
105 Sai na takaita dan kasaratar himamu
Famin hunaka kullu minnil kalamu[14]
106 Mai tambaya ga wanda ya waketa
Ko tambaya ga ambaton sunansa
107 Atiku shi yayi ta dan Bulda’u
Sunanata in an tambaya Rakda’u
108 Anyi tane dan taimakon Baliydi
Da hardaceta sai yadham Jaliydi
109 Summasalatu muyi salati jumla
Ma’assalami ai ga Manzon Allah
110 Wa’alihi wassahabihi ajama’ina
Wa taabi’ihimu wa muslimina.
[1] Fassarar wannan (Taimakon Balidai da waka mai rodi-rodi) Asalin Kalmar Raqda’u tana nufin Micijiya mai rodi rodin fari da baki a jikinta. Ya sanyawa wannan waka ne saboda a cikinta akwai baki akwai fari maana Jan baki da Fassara kamar yadda zaa gani kuma shehin zai fada a karshen kasidar baiti na 100.
[2] La muhalah= ba makawa
[3] Kun tajtahidu = ka zamo mai kokari
[4] La munazi’u= ba mai jayayya
[5] Wa’in tasha=idan kaso
[6] Summa ismu saka= sannan sunan sarka salsalatun
[7] Sayyidun mushtahiru=shararren Shugaba (na namun Dawa)
[8] Indana= a wajenmu. Abinda yasa shehi yace haka saboda Labanu a wasu bangarorin Larabawa suna amfani dashi ne a matsayin Madara kawai, saboda ba kowa yake amfani da Nono irin namu na kasar Hausa ba.
[9] A turance shine suke cewa Nymphaea (النيلوفر)
[10] Ladagu= Sara.
[11] Khuzu= ku rike.
[12] Fassarar baitin shine: ka kiyaye mai tsara wakar, sannan ka amfanar da mai karantata
[13] Fala Tahid=kada ka kauce
[14] Anan Alakalamina ya tsaya
Ma sha Allah. Allah Ya jikan Malam da rahama.
ReplyDeleteAllah ya saka da alkhairi...muna kira ga sayyidi da ayi mana pdf format na wannan qasida me albarka a yaɗa ta don amfanuwar Al'umma baki ɗaya.....Allah ya qara wa sayyidi Atiku yarda
ReplyDelete