ZAWIYOYI DA GUDUNMAWARSU WAJEN ILMANTARWA DA INGANTA RAYUWAR AL’UMMA
ZAWIYOYI DA GUDUNMAWARSU WAJEN ILMANTARWA DA INGANTA RAYUWAR AL’UMMA Tahir Lawan Muaz Attijaneey dlmuaz.ara@buk.edu.ng Gabatarwa : Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, tsaira da amincin Allah su tabbata ga shugaban talikai sayyadina Rasulillahi dan Abdukllahi da Aminatu, tare da Ahlin gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya. Bayan haka wannan maudu’I da aka bani nayi bayani akansa karkashin wannan mu’asasah ta AL-SUFF FOUNDATION yana da matukar fadi, hasali ma idan muka daukeshi gaba gaba zamuga ya kunshi bangarori biyu manya wato bayani kan zawiya sai kuma gudunmawarsu wajen ilmantarwa da inganta rayuwa, har ila yau idan muka koma zamuga cewa shin ana so ne ayi bayani akan tarihin hakan ko kuma ana so ne a kalli yadda yakamata zawiyoyi su zama a wannan zamani na karni na 21? Duk wadannan da ma wasu abubuwa na sanya abun ya zamo da fadi, amma saboda rashin lokaci mai tsawo da kuma kasancewata bana iya yawaita rubutun typing naga na takaita abin na bishi da audios...