ZAWIYOYI DA GUDUNMAWARSU WAJEN ILMANTARWA DA INGANTA RAYUWAR AL’UMMA
ZAWIYOYI DA GUDUNMAWARSU
WAJEN ILMANTARWA DA INGANTA RAYUWAR AL’UMMA
Tahir Lawan Muaz Attijaneey
Gabatarwa:
Da sunan Allah mai rahama mai
jinkai, tsaira da amincin Allah su tabbata ga shugaban talikai sayyadina
Rasulillahi dan Abdukllahi da Aminatu, tare da Ahlin gidansa tsarkaka da
Sahabbansa baki daya.
Bayan
haka wannan maudu’I da aka bani nayi bayani akansa karkashin wannan mu’asasah
ta AL-SUFF FOUNDATION yana da matukar fadi, hasali ma idan muka daukeshi gaba
gaba zamuga ya kunshi bangarori biyu manya wato bayani kan zawiya sai kuma
gudunmawarsu wajen ilmantarwa da inganta rayuwa, har ila yau idan muka koma
zamuga cewa shin ana so ne ayi bayani akan tarihin hakan ko kuma ana so ne a
kalli yadda yakamata zawiyoyi su zama a wannan zamani na karni na 21? Duk
wadannan da ma wasu abubuwa na sanya abun ya zamo da fadi, amma saboda rashin
lokaci mai tsawo da kuma kasancewata bana iya yawaita rubutun typing naga na
takaita abin na bishi da audios da zasu karfafi gabobin sda zan tattauna su.
Saboda
haka na raba bayanina izuwa nukdodi kamar haka:
1. Maanar
zawiya
2. Takaitaccen
bayanin kan tarihin zawiya a musulinci
3. Gudunmawar
da zawiyoyin darikun sufaye suka bayar na:
a. Ilmantarwa
b. Jihadi
c. Kyautata
tsarin zamantakewa
4. Zawiyoyi
a yau ina mafita?
5. Cikawa.
1. Maanar
zawiya a lugga da isdilahi
Kalmar Zawiya
a harshen Larabci an samo ta ne daga tushen
(ز و ى) jam’insa shine zawiyat da zawaya, maanarsa
shine gefe nako loko na wani bigire., daga wanna maana aka samo suna zawiya na
isdilahi ta yadda mutane suka zamo suna ware loko a cikin gidajensu don su rika
sallah ko karatun Alkur’ani da wirdai, an rawaito daya daga makarantar
Alkur’ani da ake kira Abubakr bn Iyyashin kuma aka fi sani da SHU’UBAH daya ne
daga marawaita Alkur’ani daga makaranta 7, almajirin Asimu, sadda zai rasu sai
yar uwarsa ta fashe da kuka sai ya kalleta yace meye yasa zaki kuka? Ki duba
waccan zawiyar (yai nuni da lokon da yake karanta Alkurani ) dan uwank yayi
saukar Alkur’ani dubu 18 a cikinta.
Daga
haka sai ma’anar ta koma tsakanin sufaye da suka zamo suna kebewa don bauta a
wani wuri musamman masallatai dab a na jumaa ba suke kiransa ZAWIYA, shiyasa
sai ya zamo lafazin ya shahara a hannunsu, har ila yau sufayen nan sun zamo
masu sadaukantar da kansu ne wajen koyar da al’umma addininsu da kuma aiki da
ilmin a zahiri da badini, sannan idan jihadi ya tashi zasu mike su amsa kira daga
zawiyoyi, wannan maanar ta karshe ta sanya ak sansu a wasu kasashe da sunan
MARABIT ko Ribat, musamman a kasar Misra, amma galibi irin wadannan anfi gina
su a gefen daular musulinci don zaman kare iyakoki, kamar yadda zamuga anan
kasar Hausa Sheikh Muhammadu Bello y zauna a wurno don zaman ribadi, to sufaye
kan amfani da wadannan RIBAT a matsayin wajen bauta da kare kasar musulinci. A
wasu kasashen kuma ana kiran zawiyoyi da sunan KHANIQAH خانقاه
musamman a kasashen Farisa wadda Kalmar ma ta kahanikah an samo ta ne daga
Farisanci, su bambamcinsu da sauran shine asali an samar dasu ne a hanyoyin
sarakuna don zuwa yaki da ayyukan daula domin sarki ya tsaya da jamaa don
hutawa da cin abinci daga karshe suka zamo wurin aje mabukata da masu bauta
zahidai. A wasu kasashen kuma ana kiransu TAKAYA ko TAKIYYAH التكية التكايا musamman a kasashen Turkey zamani daular Usmaniyya wato Ottoman
Empire.
A
takaice a iya cewa Zawiya a isdilahi wurine da aka tanadeshi domin zaman masu
ibada da masu neman ilmi da mabukata da kuma ciyar dasu da kula matafiya masu
wucewa wato عابر سبيل da masu jihadi da shiryasu domin kare daular musulinci.
Da
wannan bayani zamu gane cewa zawiya wata mu’assasah ce ta addini da ilmi da
take jawo mutane ta hanyar wuridi da zikirai na darikun sufye wajen wanke musu
zukata da taimaka musu da kuma amfani dasu wajen kare musulinci, sannan bata
tsaya nan bat a shiga cikin rayuwar al’umma da bada gudunmawa mabambata.
2. Takaitaccen
Bayanin Kan Tarihin Zawiya A Musulinci
Yana da
matukar wahala a iya cewa ga lokacin da Zawiyoyi suka fara a tarihin musulinci
saboda abune daya taallaka da abubnuwa dadama kamar jihadi da bayyanar sufaye
da shehunan su, shi kuma sufanci baya yiwuwa saida wajen bauta da zaman
muridai, shi kuma sufanci ya zamo abune mai zaman kansa a musulinci daga karni
na biyu.
Don haka
ma iya cewa a dunkule tarihin zawiyoyi
ya fara ne a musulinci kamar yadda muka nunar tun farkon karni na biyu a cikin
gidaje amma zawiya da tsarinta a matsayin muasassah mai tsari tsayayye to yayi
jinkiri har wajejen karni na hudu zuwa na shida a kasashen Maghrib wato Algeria
Tunisia Morocco da sauransu. Duk da cewa dukkan ayyukan zawiya anma yinsa tun
karni na biyu a kasashen larabawa da farisa daMasar wanda daga baya kuma
tsarinta yayi karfi a kasashen na Maghrib da mukai bayani.
Tsarin
zawiya ya zamo yayi karfi ne musamman sabida alakar Sharifai musamman a magrib
da yadda suka zamo mafaka ta wadanda ake muzgunawa a siyasance, har takai
zawiyoyi suna shiga shaanin siyasa sui tasiri musamman a karnonin baya bayan
nan, misali akan hajka shine zawiyar Sunusiya a Libya da Zawiyar Tijaniya ta
Shehu Umarul Futy a kasashen Africa ta Yamma musamman Mali da Senegal da
makotansu, kamar yadda zamu gani, hak iruin yadda aka kafa daular Idisiyya ta
kakannin Shehu Tijani a Morocco karkashin tuta ta sufanci da sharifta.
3. Gudunmawar
da zawiyoyin darikun sufaye suka bayar na:
Na daya: Ilmantarwa:
Kamar
yadda aka nuna a bya cewa Sufaye sun zamar da zawiya wajen kkarantarwarsu da
koyarwarsu, wannan ya sanya dukkan zawiyoyi da aka sani a duniyar muslilnci
suka zamu wurare ne na karantarwa da daukar koyarwar Annabi saw kasancewar
sufaye masu kira zuwa ga Agyaran zuciya sun zamo sun fi maida hankali wajen
gyara halaye da koya adabu na nafsu da alakarta da mahalicci, hakan baya yiwuwa
ba tare da sanin ilmin shariah ba kamar yadda Imamul Juniad yake cewa ‘ilminmu
wannan abin daurewa ne da Alkur’ani da sunna wanda ya zamo bashi da rabo
cikinsu to baya tare da tafiyar mu’’ wannan ya sa suka dora muridai kan nemaqn
ilmin Alkurani da sunna har ya zamo manyan masana na Hadisai suka rika fita ta
karkashin wadannan zawiyoyi, kai har manyan wadanda ake cece kuce akansu cikin
sufanci duniya ta shaida malamai ne misali anan shine Babban Sufin nan Mansurul
Hallaj, wanda yayi karatu mai zurfi a wajen Junaid da Sahlu at Tusturi, da abul
hasani Annuri, shi kansa Sahlu Tustury melamine na Sunna da aka cira masa hulka
a fagen ilmin Hadisi da tafsiri, haka akwai malamai irins Ibn Khafif Ash
shirazi wanda Imam Az Zahabi yake cewa shehi ne abin koyi kuma babban masanin
fikhu, mafi girma daga wannan shine Imamul Ghazali wanda ya rayu a matsayin
maraya a hannun wani sufi day a fara kula da tarbiyyarsu a zawiyarsa kuma
munsan yadda ya zamo malami da duniya ba wai kawai ta musulinci ba har kasashen
yamma sun zamo suna cira masa hula a fagen sani a fanoni daban daban.
Daga
manyan zawiyoyi da da suka bada gudunmawa ta ilmi akwai zawiyar sayyidi
Abdulwahab Ash-shaarani a cikin karni na 10, wadda Alkali Muhyiddin yai masa
wakafinta da kula da mazauna ciki tsawon rayuwarsu sarakuna da masu kudi suka
rika bata kudi don tarbiya da koyar da addinin Allah, dubban muridai suka rika
kwarara suna kwasar ilmi na sufanci da sharia, hakan ya basu dammar yin karatu
mai zurfi da fidda masana, sun zamo suna kwana karatun Alkurani da koyar dashi
da har mai littafin Tabakat ash shafi\iyyah yake cewamutane suna jin gunji kai
kace gunjin kudan zumna saboda karatu a cikin ta dare da rana.
Bayan
wannan ga majalisu na ilmi da aka tsara, da zarar mai koyar da ilmul hadith ya
tashi mai tafsir zai zauna yana tashi mai sufanci zai zauna.
Zawiyar
shehu Tijani rta a Fas ma ta ciri tuta wajen bada ilmi ya ishemu ishara yadda
shehu yake zama ana jefo masa mas’aloli masu zurfi na ilmi yana warwarewa.
Haka
idan muka zo nan zamuga yadda zawiyar Shehu Ibrahim ta zamo cibiyar ilmi daidai
da zamani haka kuma zawiyoyin Shehu Atiku da sheu Tijani Usman da shehu Mai
hula suka zamo, wadanda suma an fitar dasu ne a kasan zawiyoyin Sheikh Malam
Abubakar Mijinyawa da Shehu Malam Muhammadu Salga. Wadannan zawiyoyi sune suka
zamo fitalar kasar Hausa a karni na 9 zuwa na 20.
Na biyu: Jihadi
Daga
gudunmawar zawiyoyi a duniyar musulinci akwai jihadi, wanda shi kuma yana
kasancewa wajen yada musulinci ko kuma kauda zalinci daga kan wadanda ake
zalinta ko kuma nemawa kasashen yanci, a duk wadannan bangarori Z\awiyoyi sun bada
gudunmawa mai girman gaske, zamu dauki kowanne bangare mu gani.
A
bangaren jihadi don yada musulinci akwai jihadi na takobi dana ruwan sanyi, a
bangaren jihadi da takobi sufaye da suke jkan ribadi sun zamona farko wajen
amsa daawar jihadi a duniyar musulinci kuma sun tsaya sun kawar da dauloli na
kafirci, don kada mui nisa bari na bada misdali da jihadi da akayi a Macina da
kafuwar Daular Takwalo ta Sayyadi Umar Alfuty a shekarun 1852 zuwa 1864 inda
sayyadi Umar ya zamo Khalifa na wannan Daula ta Tijjaniya bayan day a assasa
zawiyarsa a yankin Futa Jallon a wajejen 1840, bayan nan a hankali ya sami
karfi day a rika yada Musulinci da darikarsa ta taijjaniya har ya fara yakar
Sarakunan yankinsa da suke bautawa gumaka, bayan ya kasance yana yada ilmai na
shariah da yada musulinci a wani gari da ake kira Dankraye abubuwa da dama suka
faru da suka sanya ya dau makami ya yaki sarakunan wanda said a adadin
yakokinsa suka kai32 banda kananan da bai je bad a sun kai 50. Wanda ya fara
yaka shine wani sarki mai suna Yumba Sakho wanda kafiri ne kuma da yaga alherai
Shehu umar ya sanya gaba da neman korar sa daga yankin baki daya ko kuma ma
yakarsa da kasheshi, daga nan said a ya shejkaru 12 yana jihadi dabude garuruwa
na kafirai da mataimakansu yana yada addini har dai ya samu shahada a 1864
daidai da hijra ta 1280.
A
bangaren jihadin rowan sanyi kuwa zamuga gudunmawar Dariku da Zawiyoyi ne suka
kafa Musulinci a duk yankin Yammacin Africa, musamman a nan Nigeria inda duk
kasar Hausa ta shiga Musulinci ta hannun zawiyoyin Dariku da shehunansu da
malamansu suke kai kawo a yanki, misali manyan shehunan wangarawa da suka zo
Kano suka musiuluntar da Sarakunan Kano da jamarsa koda yake kafin zuwansu
akwai musulinci amma shima dai yazo ne ta hannun manyan masu daawa sufaye da
suke zuwa daga Arewacin Africa wato Biladil Maghrib. Hakanan zamuga zuwan
Sheikh Abdulkarim al Maghili da yadda ya kara karffar Musulinci a wannan yanki
na kasar Hausa, da yadda suka kafa zawiyoyi da dama da syuka dora aikinsu har
yau din nan.
Ta fuskar kauda zalincin sarakuna zamuga yadda
Shehu Usman dan fodio yayi wanda abune sananne ga kowa.
A
karshen wannan nukda azn cike da nemawa kasashe yanci da zawiyoyi sukai, babban
misali shine jihadin Sunusiya a Libya kamar yadda na fada a baya wadda zawiyar
wannan darika suka tunkari turawan Italia da suka mamaye kasarsu, kisser Umar
Mukhtar sananniya ce ga kowanew musulmi a fadin duniya wanda shima dan darikar
Sunusiyyah ne da ya jagorannci jihadi da
turawa.
A
banhgaren Tijjaniya zanm buga misali da gudunmawar Zawiyar Tijaniya wajen
yakart turawan Faransa da suka mamaye kasar Algeria mahaifar Maulabna shehu
Tijani rta. Jikansa Sayyadi Ahmad Ammar ya zamo jagora tare dad an uwansa
sayyadi Muhammadul Bashir aka kama a 10 February 1869 aka kaisu France aka yi
musu daurin talala.
Haka
shima sayyadi Ben Omar wanda ya ziyarci Nigeria
tun kafin bayyanar faira kuma sunb hadu da Shehu Ibrahim (har suka dau
hoto yana zaune Shehu na tsaye a
bayansa) shima ya zamo jagora na yakar Turawan faransa kuma shima an kamashi.
Na uku: Kyautata tsarin zamantakewa:
Daga
abinda zawiyoyin Sufaye suka maida hankali akansa sjhine samar da zamantakewa
mai kyau, wannan nukdah tana da alaka data baya baki daya ko muce itace hadafin
dukkan abinda ya gabata na ilmantarwa da jihadi da bada mazauni ga mabukata,
don haka bazan tsawaita kanta ba. Zawiyoyi sun kasance wuri na daidaita al\umma
da basu kariya. Daga inganta al’umma akwai samar da ayyuka ga muridai da
al’umma, zamuga irin wannan a tsarin tafiyar zawiyoyi irin na sayyid Malik Si
na Senegal, haka na zamuga yadda zawiyoyi suke da tsarin wurin saukar Muridai
da wajen abinci dad akin girka abinci dad akin karatu da dakunan khalwa da
dakunan Darwishai wato maaikatan zawiyah bandaki na wanka dana tsuguno.
4. Zawiyoyi
a yau ina mafita?
A karshe
zamu rufe da tambayar dake cewa menene zawiyoyi yakamata suyi kuma menene
gyudunmawarsu a wannan zamani na cigaba da kuma kere kere? Me yakamata zawiya
tayi don taimakawa al’umma a rayuwarsu? Yaya zawiya ya kamata ta zamo a yanzu?
Wadannan tambayoyi ne da muke bukatar doguwar tattaunawa akansu don lalubo
hanyar mafita duba dayadda zawiyoyi yau suka takaita kan abu daya kawai wato
Zikiri da Wirdi, tabbas wannan shine aikin zawiya na farko, amma dai sauran ma
basu gaza shi ko su zamo sababi ne na jawo bayi zuwa hanyar Allah. Don haka
bazan tattauna wannan ba kasancewarsa maudu’I mai zaman kansa amma bisa ishara
fadin Imam Malik dayace “ba abinda zai gyara karshen al’ummar nan said a
abinda farkonta ya gyaru” maana yanzu dole ne sai mun koma tsarin zawiyoyi
na baya da suka zamo mahada ta Addini da koyarwa da siyasa da kuma kyautat
rayuwar al’umma da haska musu hanya mai kyau sawa’un a addini ko a rayuwa ko a
siyasa, amma hakan bazai yuwu ba sai jagororin zawiyoyi sun yarda da canjin
zamani ta hanyar tallafar muridai da aljihunsu da jkokarinsu da hanyoyin
sanayya (connections) da suke dasua
duniya da cikin gida. Idan muka dauki tsari irin na kungiyar sufayen nan na
kasar Turkey wato HIZMET ta fethullah Gulen wanda sun nuna a fili sun dauko
zamani da tsarin Zawiya ta zamani duk da munada wasu mulahazozi da muke ganin
lallai yakamata da darikarmu ta Tijjaniya da take kula kwarai da bangaren
rayuwa ta ruhi.
5. Cikawa:
A karshe
inaga Zawiyoyi sun bada gudunmawa mai girma a rayuwar al’umma tun daga zamanin
yaduwar Sufanci zuwa yau din nan duk da koma baya da aka samu a bangaren
gudunmawar da Zawiyoyi suke bayarwa a cikin rayuwar al’umma ta yau da kullum.
Muna fata allah ya karemun da abinda muka gabatar baki daya.
Wassalam
Dan
uwanku
Tahir
Lawan Muaz Attijaneey
Comments
Post a Comment