Silsilolin Darikar Tijaniya a Nigeria: jiya da yau.
Silsilolin Darikar Tijaniya a Nigeria: jiaya da yau. Da sunan Allah mai rahma mai jin kai. Gabatarwa: Alhamdulillahi, wassalatu wassalam ala rasulillah wa alihi wa sahbihi wasallam. Bayan haka, dalilin da yasa nai wannan rubutu shine tunatar da yan uwana Tijanawa gameda wani sashi na tarihin Darikar Tijaniaya a kasar Hausa musamman nan arewacin Nigeria, ta fuskar bada labarin hanyoyin zuwan Tijaniya da silsiloli na wannan darika, saboda lokaci ya tura ana mantawa da wasu manyan malamai da suka fara kawo Tijaniya kasar da kuma baiwa wannan darika gudunmawa ta bangarori da dama, har takai in akai maganarsu sai kaga matasan mu duk basu sansu ba, har takai ma ana neman kaskanta lamarin wadannan silsiloli ko amfani da wasu don dakile wadancan na farko. Don haka naga yakamata a takaice na rubuta wannan rubutu don fadakarwa. Silsila a addini: Silsila a larabci tana nufin sarka mai awarwaro da ake hada hancin zobe da zobe ya tashi sarka dga nan sai aka aro Kalmar akabawa duuk...