Silsilolin Darikar Tijaniya a Nigeria: jiya da yau.
Silsilolin Darikar Tijaniya a Nigeria: jiaya da yau.
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai.
Gabatarwa:
Alhamdulillahi, wassalatu wassalam ala
rasulillah wa alihi wa sahbihi wasallam.
Bayan haka,
dalilin da yasa nai wannan rubutu shine tunatar da yan uwana Tijanawa gameda
wani sashi na tarihin Darikar Tijaniaya a kasar Hausa musamman nan arewacin
Nigeria, ta fuskar bada labarin hanyoyin zuwan Tijaniya da silsiloli na wannan
darika, saboda lokaci ya tura ana mantawa da wasu manyan malamai da suka fara
kawo Tijaniya kasar da kuma baiwa wannan darika gudunmawa ta bangarori da dama,
har takai in akai maganarsu sai kaga matasan mu duk basu sansu ba, har takai ma
ana neman kaskanta lamarin wadannan silsiloli ko amfani da wasu don dakile
wadancan na farko. Don haka naga yakamata a takaice na rubuta wannan rubutu don
fadakarwa.
Silsila a
addini:
Silsila a
larabci tana nufin sarka mai awarwaro da ake hada hancin zobe da zobe ya tashi
sarka dga nan sai aka aro Kalmar akabawa duuk wata hanyar da aka ciro wani
zance ko lamari daga wani zuwa wani, wato mutanen da aka ciro abin ta hannunsu
daga farko zuwa karshe. Silsila takan zamo mai tsayi ko gajeruwa wadda a ilmin
hadisi idan an ciro ta silsila mai tsayi ana kiran hanyar Nāzil mai sauka, idan
gajeruwa ce ace da hadisin ‘āliy wato madaukaki. Daga nan aka gane idan
silsilata akwai mutum 5 ta wancan akwai mutun 8 to tawa tafi daraja a galibi,
saboda kusancina da mai maganar yafi kusa daf da daf. Amma nau’in mazajen dake
cikin kowace silsila ka iya bada gudunmawa wajen fifita hadisi kan wani koda
kuwa wancan yanada gajertar mazaje.
Zuwan
Tijaniya kasar Hausa:
Akwai
sabani da kuma rashin tabbas cikin cewa ga sadda Tijaniya tazo Nigeria, wasu na
ganin Sheikh Umar Al Futi shine ya kawo Tijaniya sa’adda yazo Arewacin kasar
nan ya zauna a Borno ya karaso kasar Hausa yya zauna a sokoto tareda Shehu
Muhammadu Bello, har ma takai ya auri yarsa bayan ya auri yar shehun Borno.
Hakanan ya shigo Kano ya assasa zawiya a cikin
lungunan unguwar Koki. Wanann ya faru a
tsakani shekarun 1831 zuwa 1839 wato lokacin da Shehu Umar Al Futi ya zauna
shekaru 7 zuwa 8 a kasar Hausa. Kuma shekaru 15 kacal da wafatin Shehu Tijani. A
wannan lokaci ne Tijaniya ta shigo, Shehu Umar Futi yu yada ta har aka rika
tunanin ma Shehu Muhammad Bello ya karbi Tijaniya ma.
Umar AL FUTI Omar Tall |
A wata
riwayar ana ganin Tijaniya ma tazo ta hannun wasu da ba’a san ko su waye ba, tun
zamanin Sarkin Kano Ibrahim Dabo 1819-1846 saboda kamar yadda Babban Malami na
Madabo yake fada cewa kakanninsu tun zamanin Dabo duk Mukaddamai ne na Tijaniya,
wannan na nuna mai yiwuwa Tijaniya shigo tun kan zuwan Shehu Umar Futi.
Silsilar
Tijaniya:
Silsilar
Tijaniya itace hanyar da aka karbo Darikar daga hannun Shehu Tijani har tazo
kanmu yau, kuma wadannan silsiloli sunada yawa amma akwai masu shuhura sosai,
akwai wadanda suka kebanta da wasu garuruwa ko Shehunai gwargwadon Alakarsu da
Almajiran Shehu Tijani, don haka zamuga Shehunan Nigeria silsilarsu ta fara ne
da silsilar Shehu Umarul Futi kamar yadda zamu gani a bayanin wadannan hanyoyi,
koda yake dai bamu sami silsilarsa day a bayar ba kai tsaye ga wani a Nigeria said
a ta biyo ta hannun almajiransa kamar su Alfa Nuhu da yazo daga baya.
Silsilolin
Tijaniya kafin zuwan Faidah:
Zan ambaci
kadan daga silsiloin dana samu ana amfani dasu kafin zuwan faidhar Shehu
Ibrahim Niasse. Saboda sunada yawa amma dai zan zabi wasu na kawo don misali.
Silsilar
Umarul Futy (sanadi Hashimiyi)
Ana kiran
wannan sanadi da Silsilatuz zahabi wato sanadi na zinare, Wannan
silsila a iya cewa shine sanadin da yake a hannun malamai da shehunanmu kafin
zuwan Faidah, domin kuwa shine sanadin Maulanamu Sheikh Muhd Salga, shi kuma
daga Sheikh Alfa Hashim Al-Futy, shikuma daga Sheikh Saidul Futy shikuma daga
Shehu Umarul Futy, Shikuma daga Shehu Muhammadul Ghali shikuma daga Maulan Abul
Abbasi Ahmadu Tijani RTA shi kuma daga Shugaban kowa da kowa sayyadul wujudi
Muhammadu saw.
Wannan
sanadi ne Maulana Shehu Atiku ya wake shia kasidarsa mai suna: طرائق الوصول إلى حضرة الرسول
Amma wannan
ba shine sanadi na farko da Malam Salga yake dashi ba, domin kuwa yana da
sanadinsa na farko daga shehinsa dake Dandalin Turawa mai suna Sharif Muhammad
b. Sheikh, wanda shi kuma ya karba daga Mahaifinsa, shi kuma ya karba kai tsaye
daga Shehu Tijani. Wannan sanadi koda ban samu wani da yake bada darika dashi
ba amma dai sanadi ne madaukaki kwarai kasancewarsa shima tsakaninsa da shehu
Tijani mutum biyu ne rak. Haka da wat salsalar ta hannun wani sharifin Morocco
mai suna Sheikh Maula Abdurrahman wanda akace yazo Kano a wajejen karshen
zamanin Sarki Abbas 1910, Sannan da wata silsilar daga Sharif Ujdud wanda shima
an sani yazo kasar nan a zamanin Sarkin Kano Abbas din dai, kuma yai wafati a
hanyar sa ta zuwa Katsina har yanzu Kabarinsa na nan a Garin Bichi.
Sanadin Sheikh
Ben Omar
Wanann
sanadi yana komawa kan Sayyadi Ali Tamasini ne shima kuma yazo da hanyoyi mabambamta,
saboda shi Sayyadi Tamasini shine ya tarbiyyanci ko ya jagoranci yayan Shehu
Tijani rta bayan ya kwasosu daga Fas zuwa Aina Maḍi, amma dai sanadinsa da nasan malamanmu
suna yawan bayar dashi kafin zuwan faidha shine:
1. Ben Omar (Ban Amar)
2. Daga mahaifinsa sayyadi Muhammadul Kabir
3. daga Mahaifinsa sayyadi Muhammadul Bashir
4. Daga Al-Qutb al’abd Lawi,
5. Daga Al-Qutb Ali At-Tamāsīni
6. daga Shehu Tijani rta.
Shehu Ibrahim Niasse da Sheikh Ben Omar
Shi Sheikh
Ban Amar yazo Kano ne a 17 Rabīʿ II 1368/16 February 1949. A hannunsa
Shehunanmu suka karba, Ban Amar shine wanda Shehu Ibrahim ya dauki hoto dashi
yana zaune shehu Ibrahim na tsaye a gefensa Sai kuma:
Sanadin
Sheikh Alfa Nuhu
sanadi Na
biyun kuma da yaake koma kan sheu Tamāsīni wanda shehu Atiku yayi ishara dashi
ne a littafinsa alfaidil Hami’I, wanda Malaminsa Sheikh Alfa Nuhu ya bashi wanda yafi kowanne
sanadi karancin Mutane, wato daga:
1. Alfa Nuhu daga
2. Daga
Sheikh Yusuf Baba
3. Daga Ali Tamasini
4. Daga Shehu Tijani rta.
Shi kuma
Alfa Nuhu yazo Kano ne a wajejen hijra ta 1353 wato wajejen 1933 zuwa 1934. kuma Malaman Kano sun amfanu dashi kamar Malam
Salga ya karbi Ismul aazam a hannunsa. Haka Shehu Atiku ya karbi izini mutlaq a
hannunsa kuma yabashi asraru da wannan silsila da muka ambata. (Duba faidil
hami’I shafi na 118-119) abin lura anan shine har yanzu ban sami wata silsila
madaukakiyar sanadi sama da wannan ba saboda mutum biyu ne kawai tsakanin mai
ita da shehu Tijani.
Sanadin
Sheikh Ahmad Hamahullahu
Wannan
sanadi daga Maulana Shehu Abubakar Mijinyawa yake, na sameshi da rubutun
hannunsa mai albarka kamar haka cikin Izinin day a bawa Almajirinsa Alhaji
Ibrahim Musa Gashash ta:
1. S Abubakar Mijinyawa
2. Daga Abdullahi Bin Jibril,
3. Daga Sharif Hamr bin Ibrahim ash
shanjidi,
4. Daga Qutbin zamaninsa masanin Allah Sayyidi
Ahmad Hamahullah,
5. Daga Masanin Allah Sheikh Tahir Bū
Taibah At Tilmisānī,
6. Daga masanin Allah Abdul Wahhab Binil
Ahmar Attaiziyu,
7. Daga Maulana Shehu Tijani rta.
Wannan
sisilar ta Mutanen yammacin Africa ce, akwai wata makamanciyarta data biyo takan
sayyidi Muhammadul Hafiz Ash-shankiti, wanda ya fara yada Tijjaniya a Africa ta
yamma.
Akwai wani
sanadin na Shehu Usman Alami wanda ya zo Kano tun zamanin sarkin Kano Usman Dan
Tsoho wajejen 1923 itama tana komawa Kan Shehu Sukairaj ne.
Sanadin Darikar Tijaniya bayan Zuwan Faidah:
Sanadin
Shehu Ibrahim (sanadi sukairajiyyi)
Bayan
bayyanar Faidar Maulana Shehu Ibrahim Niasse wanda zuwansa na farko Kano a
wantan Yuni 1945 ta zamo wani lokaci ne na juyin juya hali a Tijaniya a duniya,
Shehu yazo da sabbin tunani na cigaba bayan kasancewarsa sahibul faidah da
Shehu Tijani yayi albishirin bayyanar ta. Shehu yazo da sabon sanadi da yake bi
takan sayyadi Ahmad Sukairaj kuma malaman mu kaf suka karba ya zamo sanadi
asasi da ake bawa kowa darika akansa.
Wannan
sanadi ga yadda yake:
1. Daga Shehu Ibrahim Niasse
2. Shikuma daga Sheikh Ahmad Sukairaj
Al-iayashi
3. Daga masanin Allah Qutb Al-Abd Lawi
4. Daga Qutb Ali Tamāsīnī
5. Daga Shehu Tijani rta
Sheikh Sukairaj tareda sarakunan Makka
Wannan
sanadi shine mutane sukafi sani, amma bayan sa akwai wasu da Shehu yazo dasu kamar
sanadin shehu Abdullahi zuwa kan Muhammadul Alawi, mu bar wannan haka tunda
hadafinmu shine marhalar kawai da kuma jagoranta Shehu Ibrahim Niasse.
ABIN LURA
Abinda
yakamata mu fahimta daga wadannan salsaloli shine dukkansu suna komawa kan mai
darika ne Shehu Tijani, amma a ciki zamuga wata tafi wata tsayi, sannan akwai
guda daya da take bi ta hannun yayan Shehu Tijani wasu kuma ta hannun
Almajiransa. Koda yake ban kawo wadda take tana kaiwa har kan sayyadi Muhammadul
Habib ko Muhammadul Kabir ba saboda bamu cika amfani da ita ba a Nigeria.
ME YASA AKA SAMU KHILAFA BIYU: ALGERIA DA MOROCCO?
Abune
sananne an haifi shehu Tijania a Aina Maḍi dake Jihar Agwat ta Algeria amma ya kafa zawiyarsa a garin Fas na
Kasar Morocco, duk da a baya babu kasashen da ake kira Algeria ko Morocco saidai
yankuna, kuma muna ganin Khalifofin Shehu Tijani a Algeria da Morocco wato Aina
Maḍi da ake mata kirari da
ASIMATUL TARIQAH TIJANIYA da kuma FAS inda Kabarin Shehu Tijani yake. Tambaya
anan yaya aka samun khalifanci biyu ko ma uku? Domin kuwa akwai wata khilafar a
garin Tamasina dake algeria, To ku biyo ni kuji yadda akai.
Kwashe
iyalin S. Tijani bayan wafatinsa:
Kafin
wafatin shehu Tijani ya bada wasiyyar cewa Khalifansa shine Sayyadi Aliyut
Tamasini haka kuma yana umartarsa daya kwashe duk iyalinsa ya maidasu Aina Maḍi yana cewa “yayana babu yadda zai
dace dasu sai Sahara. Bayan dogon ja in ja da Mutanen Fas da Sayydi Tamasini da
Maula Sulaiman sarkin Fas Sayyadi Ali Tamasini ya dauke duk iyalin Shehu Tijani
ya maidasu Aina Maḍi ya zamo banda Kabarin Shehu babu
kowa a Fas sai Almajiransa da khalifofinsa na Fas. Wannan ya sanya sai dai
yayan Shehu Tijani da jikokinsa suzo ziyara fas su fita kamar kowa, amma bayan
yancin kan Morocco daga Faransa wani daga zuriar Shehu Tijani wajejen 1911 ya
dawo ya zauna a Fas shine daga nan aka samu Khalifancin yayansa na biyu a Fas
bayan Aina Maḍi dake Algeria.
A can kuma Algeria din Sayyadi Ali Tamasini shine ya
zamo babban Khalifan da yake jagorantar rayuwar Tarbiya yayan shehu Tijani har
yayi wafati, sannan har yau zuriarsa sune suke wannan Khalifanci, shiyasa suma
suna ganin khalifanscu sama yake da kowanne, khalifansu na yanzu sunansa
Sayyidi Muhammadul Id Attijaneey, sai dai tunda akwai zawiayr Yayan Shehu
Tijani wadda sayyadi Muhammadul Habib ya zamo Khalifa na farko bayan dawo dasu
Aina Madhi ya sanya wannan ta zamo khalifanci babba na Duniya kuma kowa yake
kallonta a haka saboda yadda yayan shehu suka sha gwagwarmaya da Turawa da
yaransu har takai an kashe babban dan Shehu Tijani wato Muhammadul Kabir, an
kama Jikan Shehu S Ahmad Ammar an kaishi har Faransa aka tsare shi, sheikh Ben
Amar ma haka aka kama shi bayan zuwansa Nigeria da wasu kasashen Africa a
1950s.
Wannan Khalifa na yanzu da yazo Nigeria wato Sayyadi
Ali Bel Arabi jikane na Ahmad Ammar dan Sayyadi Muhammadul Habib dan Shehu
Tijani.
A wanna gaba ne nake so na nunwa yan uwa Tijanwa cewa
ba wani uzuri da zaisa wani Batijjane ya kokarin kaucewa Khalifanci wadannan
yaya na Shehu Tijani, saboda yana da wata silsila a hannunsa ba tasu ba, haka
kuskure ne babba, domin duk masu silsilar da take hannun kowane Batijjane ta
biyo ta kansu ne ko takan sayyadi Ali Tamasini wanda shine Khalifan Shehu
Tijani na farko, kuma ya zamo jagoran daya sanya yayan Shehu Tijani kan kafa
Khilafa ta mahaifinsu da zata zamo uwa ga kowane Khalifa a Duniya.
Faiḍah babban reshen Tijaniya a yau:
Wannan nukda da nake son taunawa tanada matukar muhimmanci
garemu Tijanawa musamman yan faira, saboda kasancewarmu munyi nasha nasha a
cikin wannan Faira ne ya zamo bama hango cewa akwai Tijanawa wadanda bayan
FAIRA ba, kuma bamu da labarin wasu shiyasa har in ance ga Tijanawa bay an
faira ba sai kaga muna mamaki, to musani cewa tabbas yau babu wani reshe mafi
girma a Tijaniya sama da Faiḍa Ibrahimiyya, saboda yadda jagoranta
ya zamo gagara badau a duniyar sufanci da ilmi da wayewa, amma bayan faira
akwai wasu bangarorin Tijaniya da suke bada gudunmawa wajen yada wannan darika,
daga ciki akwai:
1. Bangaren
Sheikh Umarul Futy:
Bangarene babba da wata rana zamu ware lokaci mui
Magana akansa daban, amma kamar yadda na fada shine ya yada darikar Tijaniya a
Africa ta yamma fiye da kowa cikin karni na 19, ciki harda kasar Hausa, kuma
mun kawo muku silsilarsa, kuam har yau akwai Tijaniya Umariya a duniya musamman
a kasashen Mali da Guine da Senegal, a Nigeria ma akwaisu musamman a Elleman
Tijani dake kasar Hadejia.
2. Bangaren
Haj Malik Sy:
Sheikh Malik Sy shehi ne na Tijaniya day a kafa
bangarensa na Tijaniya an haifeshi a 1885 a arewacin Senegal ya rasu a 1922 a
kuma har yanzu akwai mabiyansa masu tarin yawa a Senegal da makotanta haka yana
da mabiya a kasashen ketare hard a Amurka wanda sunada foundation mai suna
(Islamic Tijaniya Foundation of America ITFA).
3. Tijaniya
Hamawiyya:
Shi wannan bangare munyi bayani kan sisilarsa a baya
wato mabiya Sheikh Ahmad Hamahullahu an haifeshi a wani gari da ake kira Tishit
a gabashin Murtania wajejen 1882 Hamahullah waliyyine mai ban mamaki kuma yayi
yaki da turawan faransa har takai sun kamashi sun daureshi a Faransa daga baya
zuwa kasar Kwadebuwa wato Ivory cost har yanzu kuma suna da mabiya a kasashen
Murtania da makotanta, shehu Atiku yana Tawassuli dashi a wata kasidarsa yana
cewa:
بسيدي أحمد حماه الله ** سيدنا أحمد يا الله
Shima
insah Allah wata rana zamu ware rubutu na musamman kan wannan Malami.
Wadannan sune mafi shahara cikin manyan bangarorin
Tijaniya daba yan faira ba kuma silsilarsu take wanzuwa har yau har gobe.
Abinda ya rage mana mu sani tunda muna da bangarori to
ya zamo mun san kowane bangare kuma mu girmama kowace nasaba kasancewarta nasab
ceTijaniya, duk almajirai ne na Shehu Tijani kuma shi sukewa aiki. Shiyasa ma
da aka tambayi Sheu Atiku gameda Tijanawa dab a yan faira ba sai yace Tijanawa
ne amma sun rasa wani alheri mai yawa da ShehubIbrahim yazo dashi.
Ina ganin wannan bayanin da nayi ya ishemu ishara,
amma dai zan jaddada kira na ga yan uwana Tijanawa mu san cewa Shehu Tijani ya
zamo mana a matakin farko, kuma duk daga yadda ka fito ko daga salsalar Tijaniyarka
take ka sani Shehu Tijani shine bango kuma baka neman izinin kowa wajen zuwa
wajensa ko Khalifofinsa.
Allah ya datar damu
Dan uwanku
Tahir LAWAN Mu’az Attijaneey
Zangon bare bari Birnin Kano
Litinin 14 ga Jumada Sani 1443. 17 Junairu 2022
NB: Za’a ci gaba da gyara wannan makala gwargwadon
yadda aka samu gyararrakin malamanmu.
Jazakhallahu khairan, Allah ya saka da mafificin alkhairi.
ReplyDeleteAmeeeen Nagode kwarai da gaske.
Delete