Posts

Showing posts from January, 2023

Sheykh Sharif Muhammad Al-Fasi Hafidut Tijani

Image
Sheykh Sharif Muhammad Al-Fasi (الشيخ الشريف محمد الفاسي حفيد التجاني)yana daya daga malamai Tijjanwa kuma Sharifai da suka shigo Kano suka yada darikar Tijaniya,kafin ya wuce suka fa’idantar da malamai ta hanyar Ijaza, kuma daya daga cikin muridan Sheikh Qutb al-Abd Lawi. Ya shahara da lakabin Sidi Muhammad Hafidut-Tijani wato Jikan Tijjani wanda kamar jikan Sheu Tijani ne amma ba haka bane. Tarihi bi ajiye mana abubuwa mai yawa a rauwarsa ba illa nan da can wanda une zamu tattara mu fada a wannan makala. Shigowarsa Kano: Tarihi ya nuna cewa Sidi Muhammad ya shigo Kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Abbas (yayi mulki 1903-1919) ya kuma zauna a Unguwar Dandalin Turawa kafin daga bisani ya tashi ya koma garin Lokoja inda ya rayu har ya rasu a can. Amma John Paden shi yana cewa ne Sidi Muhammad shine mutumin garin Fas na farko da yazo Kano, kuma yazo ne zamanin Sarkin Kano Alu Mai Sango (yayi mulki 1894-1903) wato yazo ne tun kafin zuwan Turawa, wanda wannan raayin zaifi zama daid...