Sheykh Sharif Muhammad Al-Fasi Hafidut Tijani

Sheykh Sharif Muhammad Al-Fasi (الشيخ الشريف محمد الفاسي حفيد التجاني)yana daya daga malamai Tijjanwa kuma Sharifai da suka shigo Kano suka yada darikar Tijaniya,kafin ya wuce suka fa’idantar da malamai ta hanyar Ijaza, kuma daya daga cikin muridan Sheikh Qutb al-Abd Lawi. Ya shahara da lakabin Sidi Muhammad Hafidut-Tijani wato Jikan Tijjani wanda kamar jikan Sheu Tijani ne amma ba haka bane. Tarihi bi ajiye mana abubuwa mai yawa a rauwarsa ba illa nan da can wanda une zamu tattara mu fada a wannan makala.
Shigowarsa Kano: Tarihi ya nuna cewa Sidi Muhammad ya shigo Kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Abbas (yayi mulki 1903-1919) ya kuma zauna a Unguwar Dandalin Turawa kafin daga bisani ya tashi ya koma garin Lokoja inda ya rayu har ya rasu a can. Amma John Paden shi yana cewa ne Sidi Muhammad shine mutumin garin Fas na farko da yazo Kano, kuma yazo ne zamanin Sarkin Kano Alu Mai Sango (yayi mulki 1894-1903) wato yazo ne tun kafin zuwan Turawa, wanda wannan raayin zaifi zama daidai domin kuwa Malam Salga kansa ya rasu a 1938 wanda kuwa an san tun faron zuwan Turawa ma ansha gwagwarmaya. A zamansa na Kano ne Malami Muhammadu Salga ya hadu dashi har ya kaddamar dashi Tijjaniya, Maulana Shehu Abubakar Atiku yana cewa cikin tarihin Shehu Muhammadu Salga mai suna: تحصيل الوطر بترجمة الشيخ محمد سلغ بن عمر
[Malam Salga] ya karbi darikar Tijjaniya da Taqdimi a hannun babban waliyyikuma Sharifi Hasaniyyi shahararre, wato wanda akafi sani da lakabinsa wato hafidut-Tijani anda aka binne a Lakwaja, shine Sharif Muhammad ain binnewa a lakwaja…”
Wannan magana tana nuna cewa shine ya fara bawa Malam Salga Takdimi.
Silsilolinsa na Tijjaniya Shehu Atiku ya fadi cewa Salsalar Sidi Muhammad da Malaman Kanosuka karba a hannunsa itace: daga gareshi [Sidi Muhammad] daga Qutb Abd Lawi daga Qutb Al-Tamasini daga Shehu Tijjani RTA Amma wasu masu binkice kamar Roman Loimier sunce ya karba daga Babansa ne Shikuma daga Shehu Tijjani RTA abinda har yanzu bamu gani ba a salsalolin nasa amma dai abinda nake gani shine abinda muka samu a garin Lokoja din na salsalar zuriar Sharif Malam Muhammadu Zangina itace: Sharif Zangina Daga Shehinsa Malaminsa Mal Abdussalam Abubakr Shawai Katsina daga Sidi Muhammad Al-Fasi daga Baffansa Abdulkarim daga Muhammadu Al-Arabi daga Sayyadi Muhammadul Kabir Dan Shehu Tijani daga Shehu Tijani RTA wanan silsila Sidi Muhammad ya rubutwa Malam Abdussalam amma kan ya bashi ya rasu, don haka sadda aka aika kayansa Fas bayan rasuwarsa sai shi baffansa Sahrif Abdulakrim yace a dawo da ita yayi zartar da ita gareshi.
wannan Salsala tana da ban shaawa ta fuska biyu, ta farko kasancewar Sayyadi Muhammadu Kabir a cikinta wanda shine babban dan Shehu Tijjani, wanda nidai ban taba ganin salsala a yankin mu ba data ke komawa kansa, saboda shi sayyadi Muhammadul Kabir bai jima sosai bayan Shehu Tihhani rta ba saboda yaki daya tashi tsakanin Turkawa da Gwamnansu Bay Hussain Basha da sharifai mutanen Fas har takai shi shehu Kabir ya jagoranci runduna aka gwabza yaki har aka kashe shi da shi da mutanen da sukai saura su 300 da yan kadan. Don haa galibin salsalolin Tijaniya na yayan Shehu suke komawa kan dan uwansa wato Shehu Muhammadul Habib. Abu na biyu shine wannan na nuna cewa eh lallai yan da alaka ta jini da su yayan Shehu Tijani koda ba kai tsaye ba, me yiwuwa wannan ce tasa su Roman Loimier sukace haka, sannan wannan ne yasa ake masa lakabi da Jikan Tijjani. Maulana sharif Ibrahim Saleh yayi ishara da kokari su Sidi Muhammad a hirar da yayi da Roman Loimeir inda yake cewa, cewa akwai wasu almajiran Shehu Aliyu amasini da suka zo Nigeria suka yada darika musamman a yankin Lokoja. Sidi Muhammad ya samu almajirai da suka karba a hannunsa da dama a Lokoja kamar Malam Abdussalam Shawai wanda shima ance ya karbi Darikar ne a hannun Sidi Muhammad a 1917 sda kuma shi sharif Malam Zangina (ya rasu a 1966).
Daga karamominsa: Farfesa M.D. Sulaiman na sashin Tarihi Jami’ar Bayero ya kawo wani labari mai ban mamaki da ya rawaita daga Alhaji Sharif Ali Danladi Zangina cikin a Littafinsa (The Hausa In Lokoja 1860-1966) bada labarin cewa wata rana malam Abdussalam ya je wajen Sarkin Zaria Kwasau wanda yana cikin Sarakunan da Turawa suka kaisu Lokoja bayan cinye kasar Hausa a 1903. Malam Abdussalam sai yace bari naje wajen Sidi Muhammad, sai sarki Kwasau ya tambayeshi kamar yana kaskanta shaanin Sidi Muhammad yace “shin wai malami ne cikakke ma da zakaje har ka iya daukar Karatu wajensa. Shidai Malam Abussalam baice komai ba sai ya tashi tsam ya fita, yana isa gidan Sidi Muhammad suka gaisa sai ya ce dashi “ai koda yake dai ni ba cikakken Malami bane kamar yadda Kwasau yake tsammani ba, amma tabbas Allah ya sanyani mai kaifin Basira ne tunina dan karami na. Koda Malam Abdussalam suka sake haduwa da Kwasau ya fada masa sai Kwasau yai mamaki ya tashi da kafa ya tafi wajen Sidi Muhammad ya bashi hakuri. Amma ba wannan ne abin mamakin ba, wanda ya biy yafi wannan: wato sadda Kwasau ya tashi ya tafi wajensa yana da Janaba a jikinsa, da suka gaisa ya bashi hakuri yana mamaki sai yace
Babu komai kar ka damu, ai kasan bayin Allah wasu lokutan ubangiji na nuna musu sirrikansa zai iya basu iko ma su gane mai janaba a jikinsa, zasu ga janabar a jikinsa tamkar irin ruwan dake jikin dan tsako da aka kyankyashe yanzu yanzu, matukar mutum bai wankan janaba ba to zasui ta ganinsa da wannan ruwan irin najikin da dan tsako
Malam Abdussalam ya rasu a 1352/1933. Wafatinsa
Bamu da wani bayani na cewa ga shekarar da Sidi Muhammad ya rasu, amma Farfesa M.D. Sulaiman yana cewa lokacin da Sidi Muhammad ya rasu ya rasu ne a zamani Sarkin Lokoja Muhammadu Maikarfi wanda yayi mulki ne tsakanin 1916 zuwa 1921 ne. Wannan na nuna ya rasu a wannan dan sakanin ne. Bayan rasuwarsa arkin ya hada iyalinsa da littafansa da duka kayansa da passport nasa aka aika dasu Fas Morocco. Ala kulli halin dai Kabarin Sharif Sidi Muhammad Hafid-Atiijani yana nan a Lokoja kusa da Kabarin Sarkin Lokoja Muhammadu Maikarfi kamar yadda ake gani a hoton kasa wanda ance Sarkin yayi wasiyya a binne shi kusada amininsa.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY