Amsar tambaya ta 28 Wanda ya riski jamaa a zikirin Jumaa to ya iya shiga zikirin kai tsaye ba tare day a karanta wani abu da vake bude ikri dashi ba,amma in yaso ya karantawa, wannan duk yazo a cikin Littafan Fikhun Darika. Amma wanda ya zamo Masbuki ne shi sai kuma ya tashi ya manta bai ciko abinda ya kubce masa ba to wannan in ya tuna a kusa to ya zo da abinda ya manta din, in kuwa bai tuna ba har said a lokaci yai tsawo har Alwalarsa ta warware to yafari sabuwa. In kuma awoyi masu tsayi sun shude masa yana kan tsarkinsa yazo da abinda ake binsa din kawaiamma mafi kyau ya sake sabuwar waifar. Wassalam.