HANYAR MAGABATA WAJEN YIN TAWASSULI
بسم الله الرحمن الرحيم
ZAWIYAR TIJANIYA FACEBOOK ONLINE LECTURE
BY :TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah tsira da amincinsa ga fiyayyen
wanda akai tsani
dashi izuwa gareshi. Bayan haka, shi Tawassuli Masala ce da malamai suka gama bayanai akanta duk da
sabanin da suke dashi kanta. Amma Magana a zahiri shine TAWASSULI daya ce daga
hanyoyin addua da kuma fuskantar
Allah taala. Don haka wannan na nufin komai akace cikin tawassuli Allah kawai ne manufar kuma
kansa abin ke komawa shi wanda
akai tawassuli dashi kamar kawai hanya ce ko tsani.
MEYE TAWASSULI?
Tawassuli kalma ce ta Larabci da aka samo ta daga WASILAH maana
hanya ko Tsani.
A shariah kuma ana nufin rokon Allah da fuskantarsa ta hanyar wani, kamar Annabawa Waliyyai ko Malaiku
ko wuraretsarkaka ko aiki na
gari. DALLAN TAWASSULI Dalilan tawassuli a ALqurani fadin Allah taala
يايا الذين ءامنوا اتقوا الله وابتغوا إليه الوسيلة
يايا الذين ءامنوا اتقوا الله وابتغوا إليه الوسيلة
Maana: Yaku wanda sukai imani kuji tsoron Allah ku nemi Tsanantuwa
zuwa gareshi.
A wannan aya Allahyai amfani da Lafazin Tsanantuwa ne a dunkule wato bai ware da me zaai
wasilar ba don haka hadisai suka zo da dama kan fassara abinda ake wasilar dashi. Wanda
anan nuqdat aka samu sabanin
Malamai.amma zance mafi inganci da Shahara shine ana yin tawassuli da MUTANE kamar Annabawa
da makamantansu, dalilinsa kuwa shine:
Tawassulin Annabi Adam Alaihissalam da ANNABI MUHAMMADU SAW kan a halicce shi cikin
hadsin da HAKIMU ya rawaita a MUSTADRAK da SUYUDI a Al-KHASA’IS da BAIHAKI a DALA’ILUBN
NUBUWWAhH cewaANNABI Adam AS sadda ya ci itaciya sai yace YA ALLAH na roke ka don MUHAMMADU
ka gafarta min saiAllah
yaceya akia kasan shi alhali ban halicce shi ba? Sai Adam AS yace saddaka halicce ni ka busa min rai
sai na daga kaina sai naga an
rubuta a makyangyamar Al’arshi (لاإله الا الله محمد رسول الله ) sai nasan ba zaka raba
sunanka ba sai ga sunan wanda yafi soyuwa zuwa gareka,sai Allah yace Kayi gaskiya Adam
shine maf soyuwar halitta gareni kuma da ka rokeni dashi na gafarta maka, badon Shi ba da
banhalicce ka ba
Haka nan akwai Hadisin Usman dan Hanif day ace wani makaho yazo wurin Annabi SAW
yace ya rasulallah bani da ido bani da dan Jagora sai Annabi saw yace kaje waje alwalar can
kai alwa;la kai Sallah rakaa 2
sai kace Allah ina rokon ka ina fuskantarka da annabinka Muhammad SAW Annabin RahamaYa
Muhammadu ina fuskantar Allah dakai don ya yaye min ganina Allah ka bashi cetona… Usman yace
wallahi bamu waste ba kuma ba
aja zance ba sai gashi ya dawo kamar bai taba Makanta ba. Haim Tirmizi Zahabi Nisa’I duk sun
rawaito shi ko makamancinsa.
Haka hadisin
da idan anyi Fari Zamanin Sayyidi Umar bn Khattab yakan hau Minbari yace Ya Allah muna
tawassuli da Manzon ka sai ka shayar damu, ya Allah muna tawassuli da Abbasu bn Abdul muttalib
Baffan Manzonka SAW YA Allah ka bamu ruwa.saimkuma kaga anyi ruwa. BUKHARI ya rawaici
wannan Hadisi
.
To wadannan Hadisai suna nuna halaccin tawassuli da ZATI na mutum
Sai kuma
tawassuli da ayyuka anan akwai hadisin da Manzon Allah saw ya bada labarin mutaneuku da
suka shiga kogo suka fake amma dutse ya rufe su a karshe suka yanke shawarar sui tawassuli
da ayyukansu don neman tsira
han kuwa akai suna kamala tawassuli dutsen ya goce daga bakin kofar kogo suka fito.
To akwai Tawassulin Sahabbai da sukai da wasu asar na Manzo saw kamar Rigar sad a take wajen
Saayidah Asma’u yar S. Abubakar wadda duk saadda wani bashi da Lafiya sai ta
dauko tat a jika ta
a ruwa abawa mara lafiya nan take sai ya warke. Muslim ya rawaici wannan hadisi.
Haka na akwai kissar Utbiy wanda yace yana zaune a bakin Raudar Annabi SAW sai nwani
balaraben Kauye yazo yace Assalamu alaika ya rasulallahi, naji Allah yana cewa “DA DAISU
SUN ZO MAKA SUKA NEMI
GAFARAR ALLAH KUMA MANZO YA NEMA MASU GAFAR DA SUN SAMI ALLAH MAI KARBAR TUBANSU NE MAI JINKAI GARESU” To ni
nazo maka ina neman gafarar
zunubina ina neman ceto dakai zuwa ubangiji. Sannan yai wasu baituka uku na waka ya tafi.
Utbiy yace sai bacci ya kwasheni sai naga Manzo saw yace ya Utbiy Riski balaraben cen kai
masha bushara an masa Gafara.
GWannan sahabbai kenan, wanda ke biye musu ma akan haka suka tashi
imam Ahmad bn
Hanbal yay Hajji sau 5 uku a kafa 2 a kana bin hawa sai ya bata a hanya wata hajjinsa, sai ya rika
cewa ya Bayin Allah ku Shiryar
dani bai gushe ba har said a ya gane hanya.
Ibn Taimiyya ma bai
musun tawassuli da Annabi ba duk da yayi inkarin tawassuli da wanin Annabi Domin da kansa
ya kawo hadisin usman bn hanif dican da mika kawo a fatawiy nasa juz’I na 3 yace akwai hadisi
da yake karfafa hakan, haka
ya kawo kisar utbiy a juz’I na daya. Kamar yadda ya tabbatar da cewa imamu Ahmad bn hanbal
yafada a MANSAK nasa daya rubutawa abokinsa MARUZIY cewa shi yana TAWASSULI da Annabi saw a adduarsa.
Izzud din
bn Abdissalam Sultanil Ulamai yana cewa bai halatta ai tawassuli ba sai da Annabi saw
amma Imam Shaukani yai masa Taaqibi ya nuna halaccin yi da ayyukaa na gari kamar Sallah zikri
salati azumi ko manyan bayin
Allah matukar mai yin tawassulin bai kudure cewa wanda yai tawassulin dashi yana da Tasiri
ba banda Allah.
SHUBHAH DA WARWARE TA
Akwai wata shubuha da masu inkarin Tawassuli suke amfani da ita cewa baa Tawassuli da Annabi bayan Rayuwarsa, tunda ya rasusuka kafa hujja da hadisin S UMAR na tawassulinsa da S. Abbas wanda bai yi da Annabi ba wai tunda yai wafati.
Akwai wata shubuha da masu inkarin Tawassuli suke amfani da ita cewa baa Tawassuli da Annabi bayan Rayuwarsa, tunda ya rasusuka kafa hujja da hadisin S UMAR na tawassulinsa da S. Abbas wanda bai yi da Annabi ba wai tunda yai wafati.
WARWARA: Sam babu dalli dake nuna baz ai tawasssuli da Annabi ko waninsa ba bayn ya
bar gidan Duniya saboda
hadisan dake nuna Tawassuli da Annabi bayan wafatinsa kamar Kissar Utbiy da Balaraben Kauye da
Tawassulin Imam Ahmad bn Hanbal day ace yana yi da Annabisaw.bugu da kari shi Annabi SAWda
rayuwarsa da wafatinsa duk
dayane kuma Alheri ne garemu kamar yadda Aka karbo daga Anas bin Malik (RTA) yace
Annabi (SAW) yace:- "Rayuwata alherice a gareku mutuwata ma alheri ce a gare". (har sau uku), sai
duk kowa yai shiru, can sai S. Umar bin Khattab yace "yaya haka zata kasance ya
Rasullahi? Sai Manzon (SAW) yace rayuwata alheri ce a gareku; ana saukar min
da wahayi daga sama
sai in baku labarin abin da aka halatta muku da abin da ya haramta gareku, mutuwata
alheri ce a gareku, ana bijiro min da aikinku duk ranar alhamis idan na alheri ne na gode Allah
yasa haka idan na zunubi ne sai in nema muku gafarar zunuban ku.
A karshe Ka’idar da zamu sanya a zukatanmu itace:
1.
Tawassuli ba mas’ala ce ta Imani
ko Tauhidi ba, balle a kafirta mai yi ko wanda baya yi, Mas’alace ta Fiqhu kamar Sabanin
FAKIHAI kan mas’alolin
Fiqhu.
2.
shi mai tawassuli bai yi tawassuli
da abinda
yaitawassuli dashi ba sai don kaunarsa da abin da kuma imani da yayi cewa wannan abun yanada Girma da
Daraja gun Allah.
3.
In ka kudurce cewa wanda kai
tawassuli dashi yana da iko ba Allah ne ba to anan kayi Shirka.
4.
shi Tawassuli ba abune na dole a
addua baa a shi dai wata hanya c eta kari nacewa, Domin Asali cikin addua shine kana
kiran Allah zai amsa maka.
5. Magabata tun daga sahabbai suna yin tawassuli da Annabawa da kuma tsarkakan abubuwada ayyuka.
Wassalam Dan uwanku
Tahir Lawan Muaz Attijaneey
2014-12-28
Tahir Lawan Muaz Attijaneey
2014-12-28
6 ga Rabiul Auwal 1436 H.
Comments
Post a Comment