Posts

Showing posts from May, 2020

Wakar Karangiya. Malam Mudi Sipikin Darma

Image
1. Da ƙunci da ƙinci ga ƙaƙanci ƙulafuci Ƙaranci ƙalancewa ƙanƙanta ƙuriciya   2. Da ƙima da ƙyama ga ƙiyama da ƙanƙamo Akwai kuma ƙamama ƙazama ƙurus ɗaya.   3. Da ƙauri akwai ƙwauri da ƙwauro da ƙwarzaba Da ƙwara da ƙwaro ƙwarƙwara ƙwai da ƙoƙiya   4. Da ƙirji da ƙin ji ga ƙirinjijiya ka ji Ƙagewa akwai ƙage ƙaranga ƙarangiya   5. Da ƙeya da ƙyuya ƙi da ƙauna ƙalamusai Ƙwalewa da ƙyalewa ƙalewa ƙalauniya   6. Da yin ƙyanƙyasa kuma ƙeƙasasshe ƙasa-ƙasa Ƙasashe akwai ƙas-ƙas ƙasa ƙansuwa ƙaya.   7. Da ƙwarya akwai ƙarya ƙaraya ƙara-ƙara Ƙirare da ƙarewa da ƙaro ƙaya-ƙaya.   8. Da ƙanzo akwai ƙozo da ƙwazo da ƙwarnafi Da ƙarfi akwai ƙarfe ƙarau ƙulla tankiya.   9. Da ƙiri da ƙira ƙirƙira kuma ƙoƙori Da ƙari da ƙarewa ƙurewa ƙalauniya.   10. Da ƙaura akwai ƙaura ƙwarewa da ƙwarzana Ƙagewa akwai ƙage da ƙuna da ƙugiya.   11. Da ƙeta da ƙato har da ƙoto da ƙatuwa Da ƙarti da ƙullutai da ƙulu ka tambaya.  ...

Wakar Yabon Shehu Ibrahim Na Kaulaha Daga Mudi Sipikin

Image
Ya Ta’ala taimake ni, In yi waka mai tunani, Hikima Allah ka ba ni, Dan uwana zo ka ji ni, Bisa wakar girmamawa. Ba munafinci gare ni, Girmamawa babu raini, Zuciya babu zanni, Babu sauran yin tunani, Sai hakikar gastawa. Ibrahim Imamu, Shehu bai damu da samu, Gun aminci za ya kai mu, Roki Allah ya tsaremu, Ba bata ko karkacewa. Shehu marhabin da kai, Mun yiwo lale da kai, Mun amince mu da kai, Ga mu yau mun hada kai, Mun taho dan gasgataw. Shehu na gode zuwanka, Na ji dadi da na san ka, Kuma tilas in yabeka, Don ko na san dabi’arka, Wadda kowa ke yabawa. Shehu du, du wanda ya bika, Kuma in ya gasgataka, Shehu zai san taimakonka, Zai wusuli babu shakka, Har ya san hanyar wucewa. Shi ya sa na zo gareka, Don in san hanya wurinka, In zamo almajirinka, Yanzu ni dai babu shakka, Na zamo mai gasgatawa. Shehu duk ko wane hali, Na tsaya bisa wanga kauli, Wanda duk ya wuce wusuli, Shi ko ya wuce jidali, ...

Bukukwan Idi a Musulici

Image
Bukukwan Idi a Musulici الأعياد في الإسلام Da Alkalamin: Tahir Lawan Muaz Attjaneey. Gabatarwa : Da sunan Allah, muna gode Allah bisa Niimominsa wadda daga cikinsu kamala Ramadan da yin Sallah Lafiya, Muna salati ga Shugaban Annabawa da Manzonni Annabi Muhammadu Da Alayensa da Sahabbansa, Allah ka yarda da Khatimin Wilaya Ahmadu dan Muhammadu Tijani da Sahabbansa da Khalifofinsa Musamman Shehin Shenanmu Maulan Sheikh Ibrahim Niasse. Kamar yadda aka bada wannan maudu’I na Bukukuwan Idi   A Musulinci   wadda wannan Mu’assasah ta AL-Suff Foundation ta shirya a matsayin goron Sallah ga yan uwa insha Allah inaso na tabo wannan abu ta kan wadannan nukudodi kamar haka: a.    Maanar Kalmar idi a Lugga b.    Idin Addinai da al’ummatai c.    Idi A Musulince 1.   Idi da Shariah ta Shar’anta da yadda ake yinsu. 2.   Idi da Ba shariah ce ta shar’anta ba amma akeyi a musulinci. d.    Wasanni a ranekun Idi. e.  ...