Wakar Yabon Shehu Ibrahim Na Kaulaha Daga Mudi Sipikin


Ya Ta’ala taimake ni,
In yi waka mai tunani,
Hikima Allah ka ba ni,
Dan uwana zo ka ji ni,
Bisa wakar girmamawa.

Ba munafinci gare ni,
Girmamawa babu raini,
Zuciya babu zanni,
Babu sauran yin tunani,
Sai hakikar gastawa.

Ibrahim Imamu,
Shehu bai damu da samu,
Gun aminci za ya kai mu,
Roki Allah ya tsaremu,
Ba bata ko karkacewa.

Shehu marhabin da kai,
Mun yiwo lale da kai,
Mun amince mu da kai,
Ga mu yau mun hada kai,
Mun taho dan gasgataw.

Shehu na gode zuwanka,
Na ji dadi da na san ka,
Kuma tilas in yabeka,
Don ko na san dabi’arka,
Wadda kowa ke yabawa.

Shehu du, du wanda ya bika,
Kuma in ya gasgataka,
Shehu zai san taimakonka,
Zai wusuli babu shakka,
Har ya san hanyar wucewa.

Shi ya sa na zo gareka,
Don in san hanya wurinka,
In zamo almajirinka,
Yanzu ni dai babu shakka,
Na zamo mai gasgatawa.

Shehu duk ko wane hali,
Na tsaya bisa wanga kauli,
Wanda duk ya wuce wusuli,
Shi ko ya wuce jidali,
Sai hakikar gasgatwa.

Jahili zai ta’ajibi,
Wanda bai fahimci gaibi,
Kar a bai wa mahajubi,
Wanda ba ya inkilabi,
Sai ya je hanya bacewa.

Shehu kai ka sha da mu,
Kai ka ke sadad da mu,
Shehu kai ne ma ka jamu,
Muka gane sha’animmu,
Muka zo gun rabukewa.

Shehu mu ka bamu jari,
Allah sa ka ma da hairi,
Mai yawa kullum da kari,
Badini har zahiri,
Mun bi hanya mai wucewa.

Kwarjini da murmushi,
Munga lalle ba kamar shi,
Ga shi ko ba ya fushi,
Dan’uwana je ka gan shi,
Dan ka huta tambayawa.

Shehu ya yarda da kowa,
Ba shi ce ga wane nawa,
Ba shi kosawa da kowa,
Ba wulakanci ga kowa,
Sai fa kauna mai dadewa.

Shehu lallai babu dama,
Kai aboki jeka dama,
Mika hannunka na dama,
In ko ka ki kai nadama,
Can a ranar tara kowa.

Shehu dai bay a kasala,
Ya tsaya sha’ani na Allah,
Ba riyasa babu zilla,
Ba shi san mai tauye salla,
Ka ji sandar dogarawa.

Duk wuya ya jure dari,
Ya shi go daji da sarari,
Ga shi dama mai kuzari,
Ko a kas ya fika suari,
Gaskiya ba ta bacewa.

Masu zargi sun ji kunya,
Da abin ya kai nihaya,
To, ina wai masu karya,
Yanzu duk sun ja da baya,
Sun ga ba halin tsayawa.

Jahilai ne masu zargi,
Masu neman bata dangi,
Da na zauna sai na hangi,
Shan azabar masu wargi,
Can a ranar tara kowa.

Shehu ni nazo wajenka,
Ba ni son wanda ya ki ka,
Duk batuna na wajenka,
Wallai ni na gasgataka,
Har zuwa ranar tsayawa.

Shehu ba ya son nifaka,
Ya yi nisa kan dakika,
Ba shi zance sai hakika,
Kaito ni da wagga waka,
Zan yi harshen Larabawa.

Shehu ni na ba ka kaina,
Zan yi bauta kan amana,
Babu tawili da kidina,
Zahiri har badini na,
Sai hakikar gasgatawa.

Shehu ni dai na yi laifi,
Duk jikina babu karfi,
Yanzu babu abin da ya fi,
Sai ka yafa min mayafi,
Har zuwa ranar tsayawa.

Rabbi Allah ka dade shi,
Kara yarda a gare shi,
Rabbu sanya ni im bi shi,
In zamo mai karsashi,
Bias bauta mai dadewa.

Gani ni na roki Jalla,
Nai salati mai kamala,
Gun masoyi mai jalala,
Har Sahabbai duk da Ala,
Nai salami ba tukewa.

Ka yi yarda ga Imami,
Shehuna kudubin Hitami,
Kai kabuli ga nizami,
Rabbi kyauta min hitami,
Sad da rayi ke tukewa.

Ka ji waka ba lulafa,
Daga Mudi mai nazafa,
Wanda baya sansarefa,
In kace to unguwa fa,
Can a Darma don tunawa.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY