Bukukwan Idi a Musulici

Bukukwan Idi a Musulici

الأعياد في الإسلام

Da Alkalamin:

Tahir Lawan Muaz Attjaneey.

Gabatarwa:

Da sunan Allah, muna gode Allah bisa Niimominsa wadda daga cikinsu kamala Ramadan da yin Sallah Lafiya, Muna salati ga Shugaban Annabawa da Manzonni Annabi Muhammadu Da Alayensa da Sahabbansa, Allah ka yarda da Khatimin Wilaya Ahmadu dan Muhammadu Tijani da Sahabbansa da Khalifofinsa Musamman Shehin Shenanmu Maulan Sheikh Ibrahim Niasse.

Kamar yadda aka bada wannan maudu’I na Bukukuwan Idi  A Musulinci  wadda wannan Mu’assasah ta AL-Suff Foundation ta shirya a matsayin goron Sallah ga yan uwa insha Allah inaso na tabo wannan abu ta kan wadannan nukudodi kamar haka:

a.   Maanar Kalmar idi a Lugga

b.   Idin Addinai da al’ummatai

c.   Idi A Musulince

1.  Idi da Shariah ta Shar’anta da yadda ake yinsu.

2.  Idi da Ba shariah ce ta shar’anta ba amma akeyi a musulinci.

d.   Wasanni a ranekun Idi.

e.   kammalawa

Da fatan Allah yasa mu dace.

 

a.   MAANAR IDI A LUGGA:

Kalmar idi (عيد) kalma c eta Larabci wadda asalin tushenta haruffa ne uku wati (ع، و، د) (a, w, d.) amma saboda wani dalili na ilmin SARFU tasaka (W) takoma (Y) wannan ba muhalline na shimfida bayanin hakan ba, amma dai maanar tushen (a, w, d.) duk maanarsa zakaga tana zagawa kan DAWOWA ko MAIMAITUWA,

Sannan ana yiwa Kalmar Jam’I da A’yād (أعياد) shine dalilin da yasaka masu bada maudu’in suka kira wanna n topic da (الأعياد في الإسلام) wato bukukwan sallah a Musulinci.

Bisa abinda ya gabata zakaga cewa kusan kowane Kamus na Larabci zai fassara maka maanar Idi ne da cewa: “Dukkan wata munasaba ta addini ko al’ada ko tarihi muhimmi da take maimaituwa ga mutane sawa’un ta farin ciki ce ko bakin ciki, sannan sawa’un tana maimaituwa a duk shekara ne ko duk wata ko duk sati ko nmakamancin haka na wani lokaci abin ayyanawa”.

b.   IDIN ADDINAI DA AL’UMMATAI

Kowane addini ko yanada raneku daya zamo an ayyanasu a matsayin idi domin tunawa da wani abu muhimmi day a faru a addinin ko domin yin wata ibada acikinsa. Hakama al’umma da kabilu sunada wadannan Raneku na bukukuwa dake zagowa duk shekara ko makamancin haka.

Misalin idi a addinin Yahudu idin da suke kira (Yom Kippur) wato ranar gafara (عيد يوم الغفران)  suna cewa a ranar ne Annabi Musa ya saukko daga Dutsen Sina karo na biyu dauke da alluna na attaura. A addinin Kirista kuwa mu bada misali da idin (Easter) ana kiransa (عيد الفصح أو عيد القيامة) wanda shine mafi girman Idinsu da sukeyinsa bayan azumin kwana arba’in, suna cewa a ranar ne Annabi Isah AS ya tashi daga cikin matattu bayan kwana uku da gicciye shi.

A al’adu kuwa zamuga cewa akwai manyan Idi kamar Idin Mutanen Farisa (IRAN a yanzu da wasu sassa a kewayenta) wanda ake Kira Idin Nairuz, wanda shine ranar farkon shekarar FARISIYYA wadda take dogaro da rana SHAMSIYYA kum itace mafi daidaituwar kalanda a duniya baki daya, suna yenta ne ranar 20, 21 ko 22 GA watan Maris na kowace shekara wanda shine ranar da dare da rana ke zama daidai wato (ليلة الاعتدال الربيعي) a turance (March equinox). Ana wannan biki har yau kasashen Iran da Turkey da makamantansu.

A Hausa ma Huasawa nada raneku makamancin wannan kamar Bikin kalamkuwa da gudanar da shi ne shekara-shekara da kaka bayan an kawar da amfanin gona.

c.    IDI A MUSULINCI

Akwai bukukuwa da akeyi a cikin da’ira ta addinin musulinci da dama wadanda zamu iya kasasu zuwa gida biyu: na farko idi da aka shar’anta shi da Nassi, na biyu kuma idi da baa sharanta shi da Nassi ba amma musulmi na yinsu. Don haka bari mu dauki kowanne mui bayanansu daya bayan daya:

1.  IDI DA AKA SHAR’ANTA DA NASSI

Wannan bangare yanada idi uku wato Idin Sallah Karama (عيد الفِطْر) da Idin Sallah Babba sallar Layya (عيد الأضحى: العيد الكبير) da Idin Jumaa wadannan iduka guda uku da babu sabani tsakanin Al’ummar Musulmi cikin cewa sune bukukwan Musulinci na manya da Nassi yazo dasu Annabi saw ya aikata su a rayuwarsa, an rawaito hadidisi daga Sayyadina Anas rta wanda Abu Dawuda ya rawaito shi yana cewa:

قَدِمَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم الْمَدِينَةَ وَلَهُمْ يَوْمَانِ يَلْعَبُونَ فِيهِمَا فَقَالَ: «مَا هَذَانِ الْيَوْمَانِ قَالُوا: كُنَّا نَلْعَبُ فِيهِمَا فِي الْجَاهِلِيَّةِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: إِنَّ اللَّهَ قَدْ أَبْدَلَكُمْ بِهِمَا خَيْرًا مِنْهُمَا يَوْمَ الأَضْحَى وَيَوْمَ الْفِطْر.

“Manzo saw ya iso madina don hijra sai ya tarar suna da kwanaki biyu na al’ada da suke wasanni a cikinsu sai ya tam,bayesu meye wadannan raneku? Sai sukace “mun zamo muna wasanninmu na al’ada a cikinsu ne a Jahiliyya. Sai Annabi saw yace “to Allah ya canja muku raneku biyu ranar Idin Layya da Idul Fitr”

A Alkurani mai girma Allah yayi Ishara ga Sallar Layya da fadinsa:

﴿ فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ ﴾ kai salla ga ubanginka ka soke (abin Layyarka).

Sannan Bukhari da Muslim sun Rawaito daga ibn Abbsin yana  cewa:

شهدتُ العيد مع رسول الله صلى الله عليه وسلم وأبي بكرٍ وعُمر وعثمان رضي الله عنهم فكلُّهم كانوا يصلُّون قبل الخطبة

Na halarci sallar Idi biyu da Annabi saw hakanan Abubakr hakanan Umar hakanan Usman duk sun kasance suna salla kafin suyi hudbar idi.

Akwai abubuwa da dama a babin sallar odi na nassosi dake nuna yadda ake yinsu da sunnonin yin Kabbara a cikinsu kafin tafiya idi zuwa hanyar idin da kabbarorin bayan sallolo biyar na ranenkun AYYAMUT TASHREEQ wato kwana ukun bayan sallah babba da zakkar Fidda kai ta karamar Sallah da dai sauransu wanda duk an bayaninsu a littafan fiqhu.

To meye hikma cikin shar’anta wadannan idi? Allah swt da kansa ya bamu amsar wannan tambaya inda yake cewa

لكل أمة جعلنا منسكا هم ناسكوه

Kowace al’umma mun sanya mata waje da lokaci Ibadarta

An fassara Kalmar MANSAKAN da IDI kamar yadda yazo a tafsiril Bagawi hakanan an fassara tad a ayyukan bauta na Hajji.

A kebance zamuga hikmar Idin Sallah karama yazo ne bayan kamala bauta ta Ramadan da Bayi sukai wadda cikinta allah yai musu garabasa BONUS na rahamarsa to karshe dole wanda aka yiwa kyautayi ya fito ya girmama wanda yayi masa wannan kyauta ta hanyar Kabbara (ولتكبروا الله على ما هداكم) da gaishehi ayi , sannan wani bangare wannan biki zai kara sakawa mutane farin ciki da saukaka musu nauyin ibadar da akayi  tsawon wat guda anayi, wato abinda Bahaushe ke cewa A SAMI SARARAWA DA SHAKATAWA.

Idin Babbar sallah kuwa dama yana damfare da aikin hajji ne da kuma kwanaki 10 da allah yai rantsuwa dasu a Alkurani (وليال عشر). Suma wannan ibadu da sashin musulmi sukai ne ake ciketa da Sallah domin godewa Allh bisa Niimar Shiryrawa.

Idi na uku shine Idin Jumaa shima ana sanya shi idi wanda yake maimaituwa duk sati saboda afadin Annabi saw cikin hadisin da Ibn Majah ya rawaito shi yana cewa:

إن هذا يوم عيد جعله الله للمسلمين فمن جاء الجمعة فليغتسل.

“Hakika wannan rana ran ace ta idi da Allah ya sanyawa Musulmi wanda duk Jumaa tazo to yayi wanka.”

2.  IDI DA BAA SHAR’ANTA BA A NASSI

Bayan wadancan idi uku da mukai Magana akansu akwai wasu idi da dama da akeyi a musulunce suma, amma babu Nassi Sarihi dayayi umarni a yisu saidai anayinsu ne saboda tunawa da wasu abubuwa manya amusulinci, wadannan bukukuwa akwai sabanin Malamai ciki wasun Hanasu suna ganinsu a matsayin Bid’ah wasu kuma na kallon su a matsayin Halal matukar babu Nassi day a hana ko ya tsayar da bukukuwa akan waancan na baya.

Daga wadannan Bukukuwa zamu bada misali ne da guda biyu kawai:

Bikin Maulidin Annabi saw don tuna rana da watan Haihuwar Jagoran Annabawa  Muhammadu dan Abdullahi Alkuashiyy. Musulmai tsawon tarihi suna yinsa tun daga kamawar watan Rabiul Auwal na Hijra har karshensa. wadda wannan mas’ala ce da Alkaluman Malamai sukai tumbudi akanta tsawon daruruwan Shekaru kuma galibin malamai sun tafi kan cewa bid’ah ce mai kyau. Musulmai na taruwa su karanta tarihin Rayuwar ANNABI SAW da dabi’unsa sui yabo da wakokin yabo gareshi da sahabbai da alayensa su kuma yi abinci da yawaita ciyarwa da sadakoki don nuna farin cikin samuwar wanda yazo da addinin baki daya.

idin Maulidi a garin Makka shekara ta 823 karkashin Jagorancin Ibnil Jazary

Imamul Jazari Shugaban Makarantan Zamaninsa yana cewa:
"Haihuwar Annabi saw ta zamo a wuri da ake kira Shi'ib (wato Zaza) wuri ne sananne da yai tawaturi a garin Makka, mutanen Makka suna fitowa duk Ranar Maulidi sui biki mai girma fiye da bikin da suke da Sallar idi.
Na ziyarci wannan gida kuma na nemi albarkarsa shekarar da nai hajji wato hijra 792 kuma naga albarkar gidan da bazata kidayu ba.
Sannan na sake maimaita ziyararsa a shekara 823 lokacin danai zama Garin Makkah, a lokacin gidan da aka haifi Annabi ya rurrushe sai na sanya aka gyara shi, a ka kuma aka karanta littafina na Maulidi " ATTAARIF BIL MAULID SHAREEF" Jamaa da basu kirgu ba suka zo suka saurari littafin. Wannan Rana dai abar bada labari ce."

Daga Littafinsa ATTAARIF BIL MAULID SHAREEF" shafi na23.

Hoton gidan da aka haifi Annabi saw a Makka

Bikin Isra’ain Annabi saw wanda riwayoyi suka nuna anyishi a 27 ga watan Rajab ne A tsakanin shera ta 11 ko 12 bayan aike. Wasu kuma suna ganin anyi a watan Rabiul Auwal ko Ramadan ma bisa sabanin riwaya. Musulmi suna taruwa shima domin raya daren Isra’I don tunawa da wannan Rana da Allah ya girma Manzo saw a cikinta da zuwa halararsa da ganin zatinsa da kuma karbo sallah da ta zamo ginshikin Addinin baki daya.

d.   WASANNI A RANEKUN IDI

To tunda mun bayanin cewa idi na zuwa ne domin sararawa da shakatawa saboda dabiar rai tason hakan anan zamui bayanin halaccin wasannin kida da rawa da suka dace da Al’adun mutane matukar basu keta haddin sharia ba acikin wadannan raneku na idi, kuma zamu kawo hadisi daya ne tal daga sahihul Bukhari wanda ya rawaito daga uwar Muminai Aisha rta tana cewa:

 

دَخَلَ عَلَيَّ رَسولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ وعِندِي جارِيَتانِ تُغَنِّيانِ بغِناءِ بُعاثَ، فاضْطَجَعَ علَى الفِراشِ، وحَوَّلَ وجْهَهُ، ودَخَلَ أبو بَكْرٍ، فانْتَهَرَنِي وقالَ: مِزْمارَةُ الشَّيْطانِ عِنْدَ النبيِّ صَلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ، فأقْبَلَ عليه رَسولُ اللَّهِ عليه السَّلامُ فقالَ: دَعْهُما، فَلَمَّا غَفَلَ غَمَزْتُهُما فَخَرَجَتا، وكانَ يَومَ عِيدٍ، يَلْعَبُ السُّودانُ بالدَّرَقِ والحِرابِ، فَإِمَّا سَأَلْتُ النبيَّ صَلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ، وإمَّا قالَ: تَشْتَهِينَ تَنْظُرِينَ؟ فَقُلتُ: نَعَمْ، فأقامَنِي وراءَهُ، خَدِّي علَى خَدِّهِ، وهو يقولُ: دُونَكُمْ يا بَنِي أرْفِدَةَ حتَّى إذا مَلِلْتُ، قالَ: حَسْبُكِ؟ قُلتُ: نَعَمْ، قالَ: فاذْهَبِي.

“Manzon Allah saw ya shigo dakina a lokacin wasu yan mata biyu suan tare dani suna waka da wakar ranar Buas (ranace ta yaki tsakanin kabilun Aus da Khazraj) sai Manzo saw ya kwanta akan shimfida ya juya fuskarsa (a wata riwayar ya lullube uskarsa) sai Abubakr ya shigo sai ya hantare ni yace “Gogen shaidan a dakin Annabi saw?” dajin haka sai Annabi saw ya juyo ya bude fuskarsa yace rabu dasu (ai yau ranar Idi ce) da Annabi yak au da kai sai Abubakr ya zunguri yan matan nan sai suka fice, to ranar ranar Id ice Bakaken fata yan HABASHA suna wasanni a filin Masallacin Annabi saw da Garkuwa da Mashi, Aisha tace kodai nice na tambayi Annabi saw ko shine yace dani ko kina so ki kalli was an nasu? Sai Annabi saw ya tsayar dani a bayansa (kamar ya goyata) na rika lekowa ina kallon wasan har kumatuna yana taba kumatunsa, yana cewa “to kunga fa yayan Arfadata” (kamar Annabi saw yana cewa ku kalli yadda yayan arfadatu suke nasu wasan, ance lakabin habashawa ne) Aisha tace har saida na gaji si Annabi saw yace “kin gaji k?” nace eh!! Sai yace to tafi abinki.

Wannan Hadisi baya bukatar ai masa dogon sharhi bisa wanna maudui, ya nuna halaccin wasannin idi da hanyoyi iri daban daban da sukai daidai da al’ada ta jamaa kamar yadda a kasar Hausa muke hawan sallah.

A wata riwayar ma ance sayydi Umar yayi kokarin hanasu ya debo dutse zai jefesu ya koresu sai Shugaba saw yace dashi “ka rabu dasu Umar domin su yayan Arfadau ne”

 

e.   KAMMALAWA:

Bayan wanna gajeren bayani gameda Bukukuwan Idi a muulinci zamu gane cewa Addinin Musulini kamar sauran addinai da suka gabata yanada Bukukuwa da ake gabatarwa, sannan zamu gane cewa adddini ya bada dama a shakata da wasanni da yan kide kide da raye raye da basu keta haddin shariah ba don nuna farin ciki kasacewar dabi’ar rain a Dan Adam Allah ya Halicceta da son shakatawa musamman bayan yin wani aiki mai wahala.

Sannan idi akwai wanda aki ittifaqi kan halaccinsa da wanda akai sabani, hakan na nufin ba dama ga wani ya tsangwami wani don yayi bikin Maulidi ko Isra’I ko Ashura da makamntansu tunda dai mas’alace ta sabani kuma kowa da hujjarsa mai karfi.

Da fatan Allah maimaita mana Salloli masu yawa cikin Lafiya da yalwar arziki ya yaye musibu da ake fama dasu da suka hanamu sakat a wannan lokaci na Idil Fitr na bana wato Cutar Corona da makamantanta.

Wassalm alaikum

Dan uwanku

Tahir Lawan Muaz Attijaneey

dlmuaz.ara@buk.edu.ng

25 May 2020


 

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY