Shehu Ibrahim Inyass a Siyasar Duniya: Ziyarar Shehu a Kasar Sin (China)
DAGA RAHOTON KAFAR YADA LABARAI TA KASAR SIN. Wannan rahoto da zan fassarashi yayi bayanin ziyara Shehu ne zuwa kasar Sin wato China a 1963 Kuma kafar Gwamnatin China ta Labarai ta buga Shehu yayi ishara ga wanan ziyara a Diwaninsa da yake cewa: ببيروت أنحو الصين بالشرق خادماً رسول إله العرش وهو تعالى لبكين من كانتون بالصين نائياً وكولخ تدعو قد أبنت الرحالا Nayi binkice na gano wannan Labari da aka ajiyeshi a wani littafin adana tsofaffin Lbarai na Duniya, mai taken: Daily Report, Foreign Radio Broadcasts , wanda hukumar leken asirin Amurka ta United States Central Intelligence Agency (CIA) ta bugashi dauke da 208-1963wato na kunshe da Labaran abubuwan da suka faru a duniya na ranar 24 ga watan October na 1963 kuma Radiyoyi da Jaridu suka buga. ...