Shehu Ibrahim Inyass a Siyasar Duniya: Ziyarar Shehu a Kasar Sin (China)


DAGA RAHOTON KAFAR YADA LABARAI TA KASAR SIN.


Wannan rahoto da zan fassarashi yayi bayanin ziyara Shehu ne zuwa kasar Sin wato China a 1963 Kuma kafar Gwamnatin China ta Labarai ta buga Shehu yayi ishara ga wanan ziyara a Diwaninsa da yake cewa:

ببيروت أنحو الصين بالشرق خادماً

                    رسول إله العرش وهو تعالى
 
لبكين من كانتون بالصين نائياً 

                   وكولخ تدعو قد أبنت الرحالا

 Nayi binkice na gano wannan Labari da aka ajiyeshi a wani littafin adana tsofaffin Lbarai na Duniya, mai taken: Daily Report, Foreign Radio Broadcasts, wanda hukumar leken asirin Amurka ta United States Central Intelligence Agency (CIA) ta bugashi dauke da 208-1963wato na kunshe da Labaran abubuwan da suka faru a duniya na ranar 24 ga watan October na 1963 kuma Radiyoyi da Jaridu suka buga.

To a wannan Ranar ta 24 ga watan Oktoban shekara ta 1963 Shehu Ibrahim Niasse RTA yakai ziyara kasar China inda ya Gana da Jagororin Siasa na Kasar China.

A wanan littafi shafi na 249-50 an buga rahoton wata Jarida ta Gwamnatin China a wancan Lokaci mai suna CHICOM international Affairs da yake cewa:
"Sheikh Ibrahim Niasse na Kungiyar Musulinci ta Senegal da Tawagarsa sun kasance Baki na musamman a wani taron cin abincin rana da Babban dan Siyasar Kasar China Shahid Burhani kuma shugaban Kungiyar Musulmai na Kasar China ya shiya musu a birnin (Peking) Beijing."

"A wannan taro Shahid Burhani ya siffanta Sheikh Ibrahin Niasse a matsayin babban amalamin addinin Musulinci kuma dan kishin kasa wanda ya tsaya kaida fata cikin harkokin cigaban kasa. ya kara da cewa

Shehu Ibrahim ya tsaya tsayin daka wajen yakar mamaya (Imperialism) da sabbi da tsoffin salon mulkin mallaka da kare yancin kasashe da mutuncinsu da kuma ganin sun tsaya bisa kafafunsu, tareda kara dankon zumunci tsakanin Kasashen Africa dana Yankin Asia dama karfafa tsaron Duniya baki daya.

Ya kara godewa Shehu Ibrahim Niasse bisa ga goyon bayansa ga Kasar Sin wajen ganin ta dawo da yankin nan nata na Taiwan Karkashin ikonta da kuma dawo da halattaciyar Kujerar Kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya.

Burahan ya kara da cewa: Sheikh Ibrahim Niasse baiyi kasa a gwawa ba wajen farfado da kawance tsakanin Jamaar Kasar Sin dana Senegal. a koda yaushe akwai kwakwarar abokantaka tsakanin Jamaar Kasar Sin dan Africa kuma akoda yaushe jamaar Musulmin kasar Sin sun masu farin ciki da wannan dangantaka tasu da Musulmin Senegal.

Jamaar Musulmin kasar Sin a cewar Burhani suna da cikakken yancin addinininsu ba tareda tsangwama ba, tareda godewa Jamiyyar Kwamunisanci da Gwamnatin Jamaar Sin bisa wannan. wannan ziyara zata kara dankon zumunci tsakanin Mutanen Sin dana Senegal a cewarsa.



  

Anasa bangaren Sheikh Ibrahim Niasse ya dade yanada Burin ziyarar Kasar ta Sin, don ziyarar tasa zata kara dankon Zumunci tsakanin Jmaaar Sin dana Senegal dama Africa baki daya, kuma zata rusa farfagandan kasashen mulkin mallak da suke yadawa gameda kasar ta Sin, domin gashi a China naga tsohon Masallaci mai tarihi, wannan na na rusa farfagandan da kasahen turawan yamma yan Mulkin Mllaka suke yadawa gameda kasar Sin.

Shehu yace "ya goyi bayan dawowa da Kasar Sin kujerarta a Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda ya goyi bayanta wajen gwagwarmaya da kasashen masu mamaya na YAMMA (Imperialism) da kuma kokarinta na gina kasa, saboda yin hakan shine adalci.

Shehin na kasar Senegal ya kara da cewa Yana fata kasar ta Sin zata zamo gagarumar Kasa mai kokarin kawo sauyi da cigaba a duniya, domin hakan zai taimaka wajen samun yancin Kasashe masu mabambamtan jinsi a Africa.

Daga wadanda suka ahalaci wannan Taro sun hada da Haj Muhammad Ali Chang, Haj Muhammad Yahya, Idu Pin-i, mataimakin shugan Kungiyar Musulmin Sin; Chang Tiehsheng, mataimakin kungiyar zumuntar Mutanen Sin da Africa; Lee Shu, da kuma Sha Mang-pi, mataimakin shugaban Kwalejin Ilmin addinin Musulinci ta Kasar Sin da sauran Jamaar Musulmi.

A wannan safiya Sheikh Ibrahim Ibrahim Niasse da yan Tawagarsa cikin Rakiyar Burhan Shahidi sun ziyarci babban dakin taron Jamaar Kasar Sin (Great Hall of The People) wanda ake amfani dashi wajen Manyan Tarukan Zartarwa na kasar China da Majalisar dokokin Jamaar China (zaaga hoton ginin a kasa) da kuma ziyartar Masallaci.

Great Hall Of The People
Great Hall Of The People

karshen rahoton kenan

Fassara : Tahir Lawan Muaz Attijaneey

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY