RADDI AKAN LITTAFIN: AS-SU’ALATUN NAJERIYYA “ANAS AN-NASHWAN” (TAMBAYOYIN NAJERIYA) ***** SHEIKH HAMDULLAH HAFIZ AS-SAFTIY ( 1 ) GABATARWA BismilLahir Rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah.. Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Manzon Allah, da Alayensa da Sahabbansa, da wadanda suka shiryu da shiriyar da ya zo da ita. Bayan haka: A duk sanda muhimman kalmomin Musulunci suka cakude da juna, to kuwa rarrabe su ta hanyar bayyana ma’anoninsu na ainihi ya zamo wajibin da ba zai iya lamuntar wani jinkiri, ko nawa ba; kuma haka zai kasance ne da zimmar yaye duhu da rudanin da suka hana fahimtar ma’anoninsu tun farko.. A irin wannan yanayi, ya kamata mu aminta da cewa tunanin mutane a kasashen Musulmai ya gurb’ata da wasu cututtuka, an damalmala abubuwa, an kuma kasa rarrabe zare da abawa, manufar wadanda suka yi hakan kuma ita ce: kawo karshen cigaban Musulunci, da raba al’umma da hakkokinta gami da arzikin da Allah ya yi mata. Lallai bayyana magani da kum...
Posts
Showing posts from 2018
TARIHIN SHEIKH UBA SUFYAN
- Get link
- X
- Other Apps
TARIHIN SHEIKH UBA SUFYAN NASABARSA: Babban Sufi Waliyyi Masanin Allah Sheikh Sufyan, anai masa lakabi da Abu Nazeer, ko Kaabar Sharifai, wanda akafi sani da Uba Sufyan Dorayi dan Muhammadul Auwal Dan Sufyan. Asalin kakanninsa yana kaiwa ga daya daga cikin malamai da Shehu Usman dan fodiyo ya aiko Kano lokacin Jihadi, Akwai wani daga kakanninsa mai suna Jakadan Dutse wanda gidansa Shahararre ne a unguwar Mandawari ana kiransa Gidan Dan Maje, wanda wani gidane da aka sani da harkar sarauta har kan kakansa Jakadan Kutama. Mahaifin Shehu Uba Sufyan yayi kaura daga Mandawari bayan daya dandana karatu, inda ya koma orayi babba inda anan aka haqifi Shehu Uba Sufyan. HAIHUWARSA DA TASOWARSA An haifi Sheikh Uba Sufyan a Hijrar ta 1359 wajejen shekara 1934 miladiyya, a Dorayi Babba dake birnin Kano Nigeria, Ya taso a hannun mahaifinsa day a fara nuna masa hanyar Ilmi da Tarbiyya, ya sauke Alkurani yana shekara 10 ya karanci sashin ilmai na Fiqhu da Larabci a hannun mahaifinsa kafin y...
MU KOYI LARABCI
- Get link
- X
- Other Apps
RUKUNAN MAGANA A LARABCI (Part of Speech in Arabic) Zance ko Magana a larabci bata fita daga daya daga cikin abubuwa uku: 1. SUNA-ISM- Noun 2. AIKI- FI;IL-Verb 3. HARAFI -HARF- Compound Letters Sabanin a harshen Turanci da yake da bangarori Takwas shi Larabci ya hade wasu yankuna cikinm wasu, misali Siffatau Adjectives suna karkashin Suna, da makamantan haka.Yanzu bari mu dauki kowane daya muga yaya suke: SUNA Suna shine wata kalma da bata bukatar sai an hadata da wata don ta bada maana, ko muce duk Kalmar da ake kiran wani Mutum ko Wuri ko Aiki da ko wani abu da ita, Misali: SUNAYEN MUTANE: محمد، زيد حبيب طويل SUNAYEN WURARE: مكة مدينة كنو أبوجل أمريكا نيجيريا SUNAYEN WASU ABUBUWA: ال...