Sharuddan Darikar Tijjaniya; daga Sheikh Abubakar Atiku Sanka

                        IFADATUL MURID BI SHARA'ITI WURDI SHEKhINA AS-SADID





Sardi ne na sharadan dariqar tijjaniyya.

 

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da Aminci su tabbata ga manzon Allah da ahalayen sa da sahabbansa.

Bayan haka, mafi bukatuwar bayi izuwa rahamar ubangijinsa Mai girma (Abubakar Atiku) Dan malam khidir Attijjaneey mutumin katsina. Wannan wasu Dan Abu da na rubuta ne cikin Sharudan dariqar Al_ahmadiyyati shashin muridi ne ya nemi ni na rubuta masa gareshi sai Na tsutsunto ta a cikin litattafan dariqa don kusantar da  wanda suke masu farawa, na ambaceta da:

[Ba wa muridi fa'ida, da sharadan Wannan shehi namu da yake madaidaici]

Allah nake roko ya amfani wanda ya Karanta shi daga Yan uwa ya sanya shi Don Allah Don zatinsa da yake Mai girma.

Nace: kasani cewa sharadinmu na dariqar Tijjaniyya wanda kowane muridi ya lazimce masa yayi riko da ita ya wajaba ya sansu sune sharadi Ashirin da Tara 29.

NA 1~ kasancewar shehi wanda yake Lakkana zikiran Nan na dariqar tijjaniyya ya zamo a yimasa izini a cikin lankantarwa, da izini ingantacce daga wanda yake jagora abin koyi ko Kuma wanda yayimasa izini izini sahihi me inganci.

NA 2~ Wanda yake so a lankana masa zikirin wannan dariqar tijjaniyyar Nan ya zamo wofantacce daga sauran wuridan shehunai, ko Kuma ya zamto me suncewa daga gareta ya fita daga waccan ya Shiga Tamu.

NA 3~ Ba'a ziyartar wani waliyi rayayye ko mattace sai Dai Annabawa da sahabbai da tijjanawa, domin wadan Nan ya halatta ka ziyarce su saki ba kaidi.

NA 4~ Dawama kan Kula da salloli guda biyar a cikin jama'a in hakan ya yiwu.

NA 5~Dawama kan son shehi ba tare da yankewa ba Har zuwa mutuwa

NA 6~ Kada mutum ya amince da makarun ubangiji Don fadar Allah ta'ala (sun amincewa tanadin Allah ne? ba Mai amincewa makarun ubangiji sai mutane wanda suke tababu).

NA 7~ Kada zagi ya fito daga gareshi ko kiyayya ko adawa a cikin janibin shehinsa ko Kuma Shehu Tijjani r a.

NA 8~ Dawama Akan Wuridi Har Mutuwa.

NA 9~ kudircewa, shine gasgatawa da abinda ya inganta yazo daga Shehu Tijjani  na zance da aiki.

NA 10~ ka kubuta daga suka shine Sabanin kudircewa wannan ka ringa saukar abinda yake na Dariqa.

NA 11~ shi dalibi ya zamo an masa izini na lankanawa sahihi daga wanda yake me koyi Koda da wasida ne.

NA 12~ Taruwa Don wazifa da ambaton hailala bayan la'ar ranar jumma'a Yana nufin Yana shirin yin wazifa taruwa Don karanta ta in akwai Yan uwa, babu uziri ko makamancinsa.

NA 13~ Kada ya karanta jauharatul kamali Sai da tsarki na ruwa, domin Annabi s a w da halifofinsa  guda hudu suna zuwa Don karatun ta da anzo jauhara ta bakwai 7.

NA 14~ Rashin yankewa tsakaninka da Musulmi ba kamar ma yan uwansa  na cikin dariqa.

NA 15~ Rashin sasautawa da wuridi kamar jinkirta shi a lokacin sa  ba tare da uziri ba.

NA 16~ Rashin gabata ga bada wuridi ba tare da anyimaka izini ingantace ba.

NA 17~ Girmama duk wanda yake da intisabi da Shehu Tijjani musanman ma manyan manyan almajiransa ma’abota kebance kebance.

NA 18~ Fuskantar alqibla da dukkan jikinsa kamar dai sallah daga farawa da zikiri Har zuwa cikawa.

NA 19~ Sirrantawa a cikin wuridi daga Farko Har karshensa, Amma dole mutum ya ringa jiyar da kansa wuridin.

NA 20~ Zama kada yayi zikiri a kwance sai Dai idan ba zai Iya zama ba, Kuma kada yayi a tsayi sai Dai idan an shagaltar dashi ga barin zaman ne.

NA 21~ Bin iyaye.

NA 22~ Ka nisanci masu suka ga Shehi Tijjani ra sune masu kiyayya da munkirai.

NA 23~ Halarto sura Shehu Tijjani ra ko surar manzon Allah s a w da wanda zai Iya hakan lokacin karanta wuridin ko wazifa.

NA 24~ Ya Halarto abinda yake Iyawa na ma’anonin zikiri idan Yana da iko abisa fahimtar ma'anoninsa.

NA 25~ Tsarki daga Kari ko dai da ruwa ko da taimama abisa Haddin Shari'a a cikin wannan.

NA 26 Tsarkin Dauda Dana jiki da tufafi da guri kamar dai yacca aka shardanta a cikin sallah daga Farko har karshe.

NA 27~ Siturce al'aura kamar yacca akai haddi a sallah daga Farko Har karshe a Shari'anci a cikin haqqin mace Da namiji.

NA 28~ Barin magana daga fara wuridi izuwa karshensa sai Dai sa uziri, zance wanda yake kankani wanda baya cutarwa kamar kalma 1 ko 2, idan Bai fa'idantar da ishara ba sai Dai da amsawa iyaye shi ko ya wuce kalma 2 baya cutarwa.

NA 29~ Niyya, shine nufi izuwa ambaton abinda ya lazamce masa na wuridi sai ya nufi wuridin asuba ko na yamma, kawai ya nufi cewa zai yi wuridi ya isarma sa, ba makawa ga nufinsa ga wuridi tare da nufinsa tare da aikatawa kasancewar sa abun nema ne ga wuridi. 

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY