Posts

Manahilur Rashad Tare da Sheikh Abubakar Atiq Sanka

Image
Amsar Tambaya ta Goma sha Biyu 12 Abin nema ga Mukaddami a kan kansa Shine yasan hukumcin tsarkin Kari da Dauda da hukumcin Alwala da sallah da abinda zai gyara su da hukumcin wurdi da Wazifa da abinda ke batasu, da abinda ake musu Jabaru dashi ya siffanta da sashin dabio'i masu girma kamar yadda yake a littafai da suke bayanin haka a muhallansu. Sannan Idan akai masa izini cikin Lakkana wurdi toabin nema agareshi: ya lakkanawa mai neman abashi Wazifa sharudda masu masu Karfi wanda in yabar daya. Dag ciki ya fita daga Darikar, ta yadda Shima in bai Lakkana masa su ba sadda ya bashi Wazifa to ya fita daga Darika, sharudan kuwa sune: 1. rashin Barinta bayan Karba, 2. Rashin Ziyarta waliyyai (wanda ba na Tijjaniya ba) 3. Rashin Hada ta da wata Darikar. Sannan ya lakkana masa sashin sharudan da in yai sako-sako da ita wurdinsa da wazifarsa zasu baci. Ya karfafa masa halartar Wazifa tare da Yan uwa a Zawiya da Salla a cikin Jamaa kamar dai yadda yake filla-filla a littafai...

WAFATIN ANNABI (12)

Image
WAKOKIN SAHABBAI CIKIN RASA'IN MANZON (SAW):   A al'adu larabawa duk sa'adda wani mutum ya rasu suna nuna mutukar bakin cikin su a cikin wake-wakensu, su kuma dinga nuna irin kyawawan halayen mamacin da martabar sa da matsayinsa, irin wannan naui na waka shi larabawa da a dibai suke kira (Rasa'u) wato yabo bayan mutuwa. To Manzon (SAW) kama sauran wanda aka yaba kafin zuwansa shima Sahabbai da 'yan uwa sun tayi masa rasa'innan, zamu kawo misalan wakoki da akayi tun a wancan lokaci, amma bazan fassara ba, sai dai kare in kawo wakar. Daga cikin wanda sukayi waka cikin haka akwai S. Abubakar inda yake cewa: ياعين بكى ولا تسأمى   وحق البكاء على السيد.    على ذي الفضائل والمكرما   ت محض الضريبة والمحتد.    على خير خندف عند البلا   ء أمسى يغيب في الملحد.    فصلى الميلك ولى العبا   دورب البلاد على أحمد.    ...

WAFATIN ANNABI SAW (12)

Image
WAYE KARSHEN TABA JIKIN MANZON (SAW)? S'adda aka zo binne Manzon (SAW) an sanya shi anyi komai kafin a tura kasar sai MUGIRATU DAN SHU'UBAH (RTA) ya saki zobensa ya fada cikin ramin, sai yace zobena – zobena!!! Sai akace dashi dauke abinka, sai ya sunkuya ya dauka ya kuma taba jikin Manzon (SAW) yace yauwa!!! Dama nayi haka e don na zama karshen wanda ya taba Manzon (SAW). Amma S. Ali (KRW) yace Kusam dan Abbas ne karshen wanda ya taba Annabi (SAW). WALLAHU A'ALAMU. To anan dai aka binne Manzon (SAW) da tsakar daren ranar laraba. An karbo daga Aisha (RTA) tace "bamu san ana binne Manzon (SAW) ba sai da mukaji karar digogi da tsakar daren ranar laraba. ALLAHU AKBAR. An rawaito cewa cewa wani Balaraben kauye ya halarci binne Manzo (SAW) sai yace: هلا دفنتم رسول الله في سفط   من الألوة احوى ملبسا ذهبا    أو في سحيق من المسك الذكى ولم   ترضوا لجنب رسول الله متربا    خير البرية اتقاها وأكرمها...