Manahilur Rashad Tare da Sheikh Abubakar Atiq Sanka
Amsar Tambaya ta Goma sha Biyu 12
Abin nema ga Mukaddami a kan kansa Shine yasan hukumcin tsarkin Kari da Dauda da hukumcin Alwala da sallah da abinda zai gyara su da hukumcin wurdi da Wazifa da abinda ke batasu, da abinda ake musu Jabaru dashi ya siffanta da sashin dabio'i masu girma kamar yadda yake a littafai da suke bayanin haka a muhallansu.
Sannan Idan akai masa izini cikin Lakkana wurdi toabin nema agareshi: ya lakkanawa mai neman abashi Wazifa sharudda masu masu Karfi wanda in yabar daya. Dag ciki ya fita daga Darikar, ta yadda Shima in bai Lakkana masa su ba sadda ya bashi Wazifa to ya fita daga Darika, sharudan kuwa sune: 1. rashin Barinta bayan Karba, 2. Rashin Ziyarta waliyyai (wanda ba na Tijjaniya ba) 3. Rashin Hada ta da wata Darikar. Sannan ya lakkana masa sashin sharudan da in yai sako-sako da ita wurdinsa da wazifarsa zasu baci. Ya karfafa masa halartar Wazifa tare da Yan uwa a Zawiya da Salla a cikin Jamaa kamar dai yadda yake filla-filla a littafai na Darika. Duk saadda ya tsaya da wadannan to ba sai ya sanar dashi Matsayin Shehu Tijjani ba RTA Bari Yana kan Muridi yayi kokari yasan wannan a littafan Darajojin Shehu Tijjani ko wanin haka in kuma ya zamo bai San wannan ba to Jaholtarsa da Hakan bazai cutar dashi ba matukar zamowarsa Yana kudure wilayar Shehu Tijani A aransa.
Sai dai wajibi ne ga kowane Muridi. Daga Muridan Tijaniya ya kuddurce haka a cikin gaba dayan Mukaddaman shehu Tijjani ko suwaye kuwa! Kuma a ko ina suka zauna! Duk saadda ya sarayar da Martaba daga Martaba daga Martabobin MUKADDAMAI to ya afaka cikin Hadari mai girma, domin duk Mukaddami Nakibai ne na Shehu Tijani, shi kuma Shehu Na'ibi ne Na Annabi SAW don haka sarayar da darajar dayansu ko ambatonsa da abinda bai dace ba sarayarwa ne ga Martabar Shehu Tijani, sarayar da Darajar S. Tijani kuma sarayar da Darajar Kakansa ne SAW wanda shi wakilinsa ne, wanda bala'in dake cikin wannan baya buya, Allah ya kiyashemu da baiwa da Falalarsa ya tsarkake zuciyarmu daga Daudar intiqadi (suka) ga waliyyanka alfarmar shugaban Annabawansa.
Wassalam.
Comments
Post a Comment