Tarihin Wafatin Annabi saw 3



MANZON YA FARA RASHIN LAFIYA:

Ya gabata garemu cewa sadda Manzon (SAW) ya dawo daga Hajji, sai yaji ciwon kai iri na matafiya bayan 'yan kwanaki ya warke, sai kuma cikin watan safar wajejen 29 – ko 28 ya fara rashin lafiyar da yayo wafati a cikinta.
A farkon rashin lafiyar sa Manzon (SAW) ya fara da ciwon kai, kuma ya zamo yana ciratuwa daga dakin waccan matar tasa, zuwa waccan, daga karshe rashin lafiyar sa tayi tsanani a dakin Maimunatu bintil Haris, sai ya tara matansa ya nemi izininsu kan yayi jiyyarsa a dakin S. Aisha (RTA). Sai suka yarda da Shugaban Adalai SAW.
MUTANEN MADINA AL-ANSAR DA TSORON RABUWARSU DA MANZON (SAW):
An rawaito sa'adda Manzon Allah (SAW) yake rashin lafiya har ya kasa fitowa sallah, sai mutan Madina wato Ansaru suka taru a cikin masallacin Manzon (SAW), suna masu tausayawa da kuma tsananin tsoron ace Annabi (SAW) ya bar duniya. Saboda haka Abbasu dan Abdulmuttalib (RA) ya shigo ya sanar da Manzon Allah (SAW) abinda suke ciki, nan take Annabi (SAW) ya fito kansa a sunkuye ya dafa S. Ali da Fadlu, Abbasu kuma a gabansa, har sai da ya isa bakin Minbarinsa ya zauna, sannan mutane suka zauna suka nutsu sai ya godewa Allah ya yabeshi, sannan yace "yaku mutane labari ya isar min cewa ku kuna tsoron mutuwar Annabinku, shin an wanzar da wani Annabi gabanin zuwana? Balle ni a wanzar dani a cikin ku? To kusani nifa mai haduwa ne da Ubangijina, haka kuma masu haduwane dani, saboda haka ina yi muku nasiha da muhajirai na farko da alheri…. Ina yi mumu nasiha da Ansaru da alheri domin sune wadanda suka tanadi gida da imani gareku, ku kyautata musu, ba sune suka raba yayan itacensu daku ba? Ba sune suka yalwata muku a cikin gidansu ba ba sune suka zabeku akansu ba?! suka baku abubuwansu koda suna da bukata?! Sai Sahabbai suka rushed a kuka, daganan mazon Allah (saw) ya koma gida.
SAYYADI ABUBAKAR YANA JAGORANTAR SALLAH:
Sa'adda rashin lafiyar Manzon (SAW) ta karu, fita ta gagara gareshi zuwa jan sallah sai yace "Ku umarci Ababakar yayi sallah da mutane". Sai Sayyada Aisha tace "Ya Annabin Allah Abubakar mutum ne mai tsaushin zuciya sai Annabi (SAW) ya sake cewa "ko umarci Ababakar yayi sallah da mutane", sai Aisha ya sake fadin abinda ta fada da farko sai yace "kudai'yan uwan Yusifa ne, nace ku umarci Abubakar yayi sallah da mutane, wato yana nufin sun cika jayayya kamar 'yan uwan Annabi Yusuf, ita kuma Aisha (RA) tana sone a janye jagorancin sallah daga mahafinta gudun kada mutane su fitunu da shi, kuma tasan mutane basu son duk wanda akace yau ya tsaya mahallin Manzo saw, amma Annabi (SAW) ya dage sai shi.
To daga nan Sayyadina Abubakar ya cigaba da jagorantar sallah har tsawon kwana hudu, wato zuwa ranar da Manzon Allah (SAW) yayi wafati, inda ya jagoranci salloli goma sha bakwai 17.
An rawaito daga Sayyada Aisha (RTA), cewa Manzon (SAW) ya shigo dakinta lokacin yana dafe da kafadar Fadlu da Sayyadi Ali (RTA) koda ya shiga sai ciwon ya rufeshi, sai yace "ku kwarara min ruwa salka bakwai daga rijiyoyi daban-daban".
Aisha tace sai muka zaunar dashi akan wata kwarya ta Sayyada Hafsat (RTA) muka kwarara masa wannan ruwa har sai da ya dinga dago mana hannu yana cewa (yaisa ya isa) daga nan sai yaji sauki, sai ya fito ya zauna a kan matattakalar minbari yace da mutane ku matso gareni, sai mutane suka taru sai yace "Allah ya la'anci Yahudawa da Nasara don sun riki kabarurrukan Annabawansu gumaken da ake bautawa.
A ranar Alhamis kafin wafati da kana 4 Manzon (SAW) yace da Sahabbansa ko kawo min takarda da alkalami in rubuta muku wani abu da bazaku bata ba a bayansa" a lokacin ciwo ya kama Manzon (SAW) sosai a cikin dakin kuma akwai mutane, daga cikinsu akwai Sayyada Umar dan Khaddab sai yace "ciwo ne yake rinjayarsa, kuma akwai Alkur'ani a wurinku littafin Allah ya isheku, to sai wadanda suke dakin sukayi sabani a tsakaninsu wasu na akawo wasu suna cewa a'a. koda jayayya ta yawata sai Manzon (SAW) yace ku tashi kubani wuri".
A wannan rana Manzon (SAW) yai wasiyya da cewa kada a bar Bayahude ko Nasara ko Mushriki a Jazirar Larabawa.
Manzon (SAW) ya zamo kafin yasa S. Abubakar sallah yana  fitowa sallah duk kuwa da irin tsananin ciwonsa, har sai da wannan rana tazo inda karshen sallarsa da mutane itace sallar magriba inda ya karanta suratul Mursalati. Bukhari ne ya rawaito daga ummil Fadli

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY