WAFATIN ANNABI SAW (9)
LABARAN
WAFATIN MANZO (SAW) YA WATSU:
Koda
labarin wafatin Manzon (SAW) ya watsu cikin Madina, sai kowa ya rude, masu kuka
na faman yinsa ba kakkautawa, wasu sun kasa zama ko tsayuwa saboda rudi wasu koma
sun zamo tamkar kurame bebaye basa iya magana kuma basa fahimtar me ake cewa.
S. Usman
yana daga cikin irin wanda suka zamo kamar bebaye. S. Umar kuwa sai ya zare
takobi yace "sai na sare kan duk wanda ya sake cewa Manzon (SAW) Allah ya
rasu kadai ya tafi ne izuwa ubangijinsa kamar yadda Annabi Musa (AS) ya tafi, kuma
zai dawo. An karbo daga Abu Zu'aibul Huzaiy cewa Sa'adda ya shigo birnin Madina
sai ya tarar da ita ta cika da kuka da hargowa, kai kace hargowar Alhazai ce, sai
na tambaya lafiya sai akace ai Manzon (SAW) ne yayi wafati…".
Sa'adda
labarin ya iske S. Abubakar gidansa dake
"Sunh" sai gashi yazo koda isowarsa sai ya shige kai tsaye cikin gidan
Annabi. Ya shiga daki inda Annabi (SAW) ke kwance, ga mata sun kewaye shi sunata
faman kuka, sai duk suke rufe fuska kunsu in banda 'yarsa wato (Aisha), sai ya bude
mayafin da aka rufe fuskar Manzon (SAW) ya sumbace shi, sannan yayi kuka yace fansarka
uwata da ubana ya Rasulallahi hakika mutuwar da Allah ya rubuta a kanka ka
dandaneta, sannan ba zaka sake dan dana wata ba har abada. Sannan ya mayar da
mayafin ya rufe Manzon (SAW) ya fito.
Koda
fitowarsa sai ya tarar da S. Umar yana yiwa
mutane magana, kamar yadda muka fada a baya ya zare takobi. Sai S. Abubakar yace
dashi saurara min yakai Umar yi shiru, sai Umar yaki yai shiru, koda Abubakar yaga
haka sai ya koma can gefe daya yayi kiran mutane, sai suka taho suka bar S. Umar shi kadai, sai S. Abubakar ya godewa
Allah yayabe shi, sannan yace "yaku mutane duk wanda yake bautawa Muhammadu
to yau Muhammad ya rasu, wanda yake bautawa Allah to Allah rayayyene baya mutuwa,
sannan S. Abubakar ya karanta fadin Allah:
ﭽ ﭳ ﭴ
ﭵ ﭶ ﭷ
ﭸ ﭹ ﭺ ﭻﭼ ﭽ
ﭾ ﭿ ﮀ
ﮁ ﮂ ﮃﮄ ﮅ
ﮆ ﮇ ﮈ
ﮉ ﮊ ﮋ
ﮌﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﭼ آل عمران: ١٤٤
A dunkule
abinda ayar take nufi shine Muhammadu bai zamo ba sai dai Manzo ne daga cikin manzanni
da suka shude ga baninsa, shin idan ya mutu ko aka kasheshi, sai kujuya (ga barin
addini), abisa duga-duganku, to (kusani) duk wanda ya juya akan duga-duginsa to
bazai cuci Allah da komai ba, Allah ta'ala zai sakawa masu godewa".
Koda
mutane sukaji wanna ayar sai suka tabbatar dai cewa Annabi (SAW) fa ya koma ga
Ubangijisa, sai S. Umar yace wallahi dani da mutane kamar bamu taba karanta
wannan ayar ba, sai a rannan take sai naji gwiwata tayi sanyi, naji kamar kafata
bazata daukeni ba sai da na fadi a kasa, na tabbatar cewa Manzon (SAW) lallai
ya rasu.
Bayan
da kowa ya tabbatar da wafatin Manzon (SAW) sai kuma aka shiga maganar khalifanci
wato waye zai khalifanci Annabi (SAW) wanda in sha Allahu zanyi bayaninsa anan
gaba, amma yanzu zan shiga magana akan binne shi tukunna.
Comments
Post a Comment