Tarihin Wafatin Annabi saw

Daga Littafina TARIHIN Wafatin Annabi SAW:

A BIRNIN MADINA ALAMUN BAN KWANA NA MANZON (S.A.W):
Bayan dawowar Manzon (SAW) daga aikin hajjinsa na karshe, sai ya sami ciwon kai, kamar irin na wanda yayi tafiya ya dawo, saboda gajiya, sannan daga baya ya sami waraka. Dangane kuma sai alamun bankwana suka kara bayyana a fili cikin Zantuka da ayyukan Manzon (SAW), ga kadan daga wasu abubuwa da suke nuna haka. 
An karbo daga Abu Muwaihibata baran Manzon (SAW) yace Manzon (SAW) ya tasheni a wani tsakar dare yace dani 'ya Aba Muwaihibata hakika ni an umar ce ni dana nemawa ahlin makabartan nan ta Baki'a tashi mutafi". Sai na tashi na tafi tare dashi, koda yaje tsakiyar mamatan sai yace "aminci ya tabbata a gareku ya ahlin makabartar nan, abinda kuka zamo a cikin yayi muki dadi, daga abinda mutane suka zamo a cikin, fitintunu sun fuskanto kamar yankin dare bakikkirin ta karshe tana bin ta farko, ta karshen tafi ta farkon sharri", daga nan sai Manzon (SAW) ya juyo zuwa gareni yace "ya Aba Muwaihibata hakika ni ambani mubudan taskokin duniya kuma dawwama a cikinta, sannan Aljanna sai aka bani zabi tsakaninsu da haduwa da Ubangijina da Aljanna. Sai Abu Muwaihibatu sai nace yace:- "fan sarka uwata da ubana, ka karbi mubudan taskokin da dawwama a duniya tare da Aljanne. Sai Manzon (SAW) "sam wallahi ya Aba Muwaihibata na zabi haduwa da Ubangijina da Aljanna". Sannan ya nemawa Ahlin Baki'a gafara ya koma gida, daga rannan kuma ya fara ciwon ajalinsa karbo daga Sayyada Aisha (RTA) tataceanzon (SAW) ya dawo daga makabartar Baki'a ya tarar dani ina jin ciwon kai sai nace:- "wash kaina" sai yace bari dai Aisha wash!!! Kaina nidai", sannan yace:- "Me zai cukeki ace da ki mutu kafin ni, na tashi nai miki wanka na sa miki likkafani na miki sallah na binneki sai tace sai nace dashi "wallahi kamar ina kallomka in haka ta faru ka dawo – daga binneni – ka shiga dakina da wata daga matanka ku angwance". Sai Manzon (SAW) yai murmushi, daga nan sai ciwon kansa ya dinga cigaba, ahali shi yana ta zaga dakin natansa kamar yadda ya saba, har sai da ciwon ya ta'azzara sai ya nemi izinin matan da yayi jiyya a dakin Sayyada Aisha (RA), sai sukayi masa izini.
An rawaito daga Ayyub bn Bashirin yace " Manzon (SAW) ya fito kansa a sunkuye har sai da yazo kafar mimbari ya zauna akai farkon abinda ya fara yi shine ya nemawa shahidan Uhudu gafara ya yawaita addu'a agaresu, sannan yace "wani bawa daga bayin Allah, Ubangijinsu ya bashi zabi tsakanin duniya da lahira da kuma abinda yake wurin Ubangijinsa, sai ya zabi abinda yakin wurin Allah (a lokacin babu wanda ya fahimci abinda Manzon (SAW) yake nufi), sai nan da nan Sayyadi Abubakar (RTA) ya fahimta cewa Annabi dai yana nufin kansa ne, sai kawai ya kama kuma sannan yace "Bari ya Rasulallahi mu muna fansar ka da kawunanmu da yayayenmu", sai Manzon (SAW) yace "saurara ya Ababakar", sannan ya sake cewa "ku duba duk tagar dake cikin masallaci ku toshe ta sai dai tagar Abubakar, domin ni bansan wani mutum da ya fishi kyawun abokantake gareni ba, da dai na zamo zan riki majidadi (Bada daya da na riki Abubakar Badadina, sai dai kawai abota da yanuwantakar imani har Allah ya taramu baki daya a wurinsa.
An karbo daga Aisha (RTA) tace sau dayawa ina jin Manzon (SAW) yana fadin "Hakika Allah bai taba karbar ran wani annabi ba har sai ya bashi zabi". Lokacin da Manzon (SAW) yazo gargara karshen abindanaji yana cewa shine "Bari izuwa madangani Madaukaki:
"بل الرفيق الأعلى".
Anan nasan Annabi (SAW) ya zabi ya tafi, sai nace:
إذا والله لا يختارنا.
Daga abinda yake nuna kusantowar wafatin Manzon (SAW) saukar suratun Nasri domin Allah (SWT) ya gayawa Manzon (SAW) a cikinta cewa sa'adda yaga jama'a suna shiga addini jama'a jama'a bayan da suna shiga daidaiku to yayi tasbihi da neman gafarar Ubangijinsa, hakan kuwa ta faru, domin kafin tafiyar Manzon (SAW) zuwa Hajjin bankwana kabilu sun dinga zuwa kungiya kungiya suna musulunta ga kadan daga cikinsu:- jama'ar Najiran da sukazo suka musulunta 60, sai kabilar Dhimam bn sa'alabah da suka zo suka musulunta baki dayansu, sai kabilar Abdulkais, sai kabilar banu Hanifa, wadanda a cikinsu aka sami Musailamatul Kazzab, sai kabilar Daiyi'in da kabilar Kindan, da Uzhu shunu'ah da jama'ar Tujibah, da jama'ar Kabilar Sa'alaba da Banu Asad da Banu Fazarata, banu sa'ad Huzaim, banu Gassan, banu Muharibin, banu Urrata da sauransu, dukkan wadannan kabila da jama'a sun dinga zuwa daya, bayan daya suna mika wuya, koda ganin haka Manzon (SAW) ya tabbatar da kusantowar ajalinsa shi yasa ake cewa suratu Izaja'a ta kawowa Annabi (SAW) labarin zuwan wafatinsa ne.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY