WAFATIN ANNABI SAW (12)



WAYE KARSHEN TABA JIKIN MANZON (SAW)?


S'adda aka zo binne Manzon (SAW) an sanya shi anyi komai kafin a tura kasar sai MUGIRATU DAN SHU'UBAH (RTA) ya saki zobensa ya fada cikin ramin, sai yace zobena – zobena!!! Sai akace dashi dauke abinka, sai ya sunkuya ya dauka ya kuma taba jikin Manzon (SAW) yace yauwa!!! Dama nayi haka e don na zama karshen wanda ya taba Manzon (SAW).
Amma S. Ali (KRW) yace Kusam dan Abbas ne karshen wanda ya taba Annabi (SAW). WALLAHU A'ALAMU.
To anan dai aka binne Manzon (SAW) da tsakar daren ranar laraba.
An karbo daga Aisha (RTA) tace "bamu san ana binne Manzon (SAW) ba sai da mukaji karar digogi da tsakar daren ranar laraba. ALLAHU AKBAR.
An rawaito cewa cewa wani Balaraben kauye ya halarci binne Manzo (SAW) sai yace:
هلا دفنتم رسول الله في سفط
 
من الألوة احوى ملبسا ذهبا
  
أو في سحيق من المسك الذكى ولم
 
ترضوا لجنب رسول الله متربا
  
خير البرية اتقاها وأكرمها
 
عند الإله إذا ما ينسبون أبا
  

Yana cewa "me zai hana ku binne Manzo (SAW) a cikin wani rami na lu'ulu'u yana sanye da tufafin zinare, ko kuma ku binne shi a cikin garin turaren miski tsantsa, kada ku yarda kasa ta taba jikin Manzo (SAW) domin – shine mafificin halitta, kuma mafi tsoron Allanta kuma mafi girmanta a wajen Allah, sa'ada ake dangantasu da iyayensu".
Koda S. Abubakar yayi wadannan kalamai sai yace "Allah ya sakamaka, kuma ina fata Allah yaji kanka da abinda ka fada dinnan, amma sai dai wannan hayan binnewar itace wadda muka sani. Bayan da aka gama binne Manzo (SAW) sai S. Bilalu ya yayyafa ruwa akan kabarin, ya fara daga wurin kansa zuwa kafa.

WAKAR S. FADIMA AKAN WAFATIN MAHAIFINTA:
Sa'adda aka gama binne Manzo (SAW) sai S. fadima (RTA) tazo ta damki kasar kabarin Manzo (SAW) ta zuba a idonta da kanta ta kuka sosai, sannan ta fara zubo baitukan babakin cikin data shiga sakamakon rabuwa da mahaifinta tana mai cewa:
ما ذا على من شم تربة أحمد * أن لا يشم مدى الزمان غواليا
صبتعلى مصائب لو أنــها * صبت على الأيام عدن لياليا.
Abinda take fada a baitin karshi shine "an zuba min musibun da da za'a zubawa rane ku su, sai su juye su koma dare, saboda bala'in musibun", ta sake cewa:
أمسى لخدى للدموع رسوم * أسفا عليك وفي الفؤاد كلوم.
والصبر يحسن في المواطن كلها * إلا عليك فإنه مذمــوع.
لا عتب في جزئي عليك لو أنه * كان البكاء لمقلتى يــدوم.
Ma'anar baitun a dunkule "shatin zubar hawaye ya wanzu akan kundukuki na, saboda bakin cikin rabuwa dakai, gashi kuwa miki ya wanzu a zuciyata.  Shi hakuri abune da yake yin kyau a kowane muhalli, sai dai a wajen rabuwa dakaci hakuri abin zargine, saboda haka babu zargi (agareni) cikin firgirtata, saboda rabuwa dakai, koda kuwa kukan zai dauwama a cikin kwayan idona.
Tun daga rannan ba'a sake ganin S. Fadima cikin fara'a ba har tayi wafati bayan wafatin Manzon (SAW) da wata, shida.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY