TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY




GABATARWA:
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) mai rayawa mai kashewa, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban kowa wanda yake cewa "Rayuwata da mutuwa ta alheri ce a gareku", da alayensa da Sahabbasa baki daya.
Bayan haka, hakika tarihin wafatin Manzon (SAW) tarihi ne mai matukar sosa ran dukkan wani Musulumi masoyin Annabi (SAW) badan komai ba sai don irin matukar kauna da Manzon (SAW) ya nunawa Alummarsa da hanyoyi daban – daban wanda hakan tasa Allah (SWT) ya yabeshi da fadinsa.
"عزيز عليه ما عنتم حريص عليكم بالمؤمنين رؤوف رحيم".
Shi yasa a duk lokacin da ake karanta kissan wafatin Manzon (SAW) zaka ga duk wanda ke saurara jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karye, idonsa kamar yayi kuka wasu ma suna zubar da hawaye tsikar jiki tana tashi wanda hakan yana karawa musulmi so da kauna da kishin Annabi (SAW), saboda haka ne ma na rubuta wadannan 'yan takardu don fito da tarihin wafatin Manzon (SAW) cikin harshen hausa da kowa ka iya dauka ya karanta. Bayan nayi nayi dan karamin binkice a cikin littattafan tarihin da fatan Allah ya amfane mud a abinda zamu karanta abinda nayi na kuskure Allah ya gafarta min, kuma ina neman afuwa da fatan malamai zasu gyara min. na ambaceshi.
TARIHIN WAFATIN MANZON (SAW);
 Wassalam Alaikum.

                                                          Dan uwanku Dahir Lawan
                                                          Mu'az Zangon Bare-bari,
                                        NO. 130. 08060306021.  

HAJJIN BAN KWANA:
"SHEKARA TA 10 BAYAN HIJRA":
SHIMFIDA:
Kusan na iya cewa duk wanda zai yi magana akan wafatin Manzon (SAW) ya zama wajibi gareshi ya farad a Hajjin bankwana, inda yana so maganarsa tayi ma'ana sosai, saboda haka ne nag anima ya zame min wajibi na fara da su akan Hajjin ban kwana nayi bayaninsa koda ban tsawaita ba inda zan tabo wasu daga wasiyyoyin Manzon (SAW) dukkan musulmi wadda yayi su a cikin Khudbar nan shahararriya ta ban kwana.
FITAR MANZON (SAW) ZUWA HAJJI:
Manzon (SAW) ya fara shirye-shirye zuwa aikin hajji a cikin watan Zul kada na shekara ta goma. Ranar asabar 25th ga Zul ka'ada, bayan azahar ya fita daga Madina, ya mika tare da Sahabbansa har sai da suka zo wuri da ake cewa dashi Zul hulaifa, inda anan yayi sallar la'asar raka'a biyu (wato yayi kasru kenen), ya kwana anan, washegari da azuhur yayi wankan shiga ihrami, sannan S. Aisha (RA) ta shafa masa turare a jikinsa da kansa, sannan ya sallaci azahar raka'a biyu, sannan yayi niyyar hajji da umra wato (kirani), sannan ya fito yah au taguwarsa (ALKASWA'U).
Manzon (SAW) ya mika har sai da yakai, kusa da garin Makka, inda ya kwana a wani wuri da ake kira ZI TUWA (ذي طوى) , bayan yayi sallar Asuba, yayi wanka ranar lahadi 4 ga Zul hijja, bayan yayi kwana takwas a hanya, yana shiga harami sai ya nufi Dakin Ka'aba yayi dawafi, yayi sa'ayi tsakanin safa da marwa, Manzon (SAW) ya shiga Makka ta wani wuri da ake Saniyyatul Ulya da hantsin wannan rana koda ya hango Ka'aba daga nesa sai yace:

"اللهم زده تشريفا ومهابة وبرا".
ma'ana "Allah ka kara masa girma da daukaka da biyayya".
Duk sa'adda yah au kan safa sai yace:               
"لا إله إلا الله الله أكبر لا إله إلا الله وحده أنجز وعده ونصر عبده وهزم الأحزاب وحده".                                           
"Ma'ana La'ila Illah Allahu Akbar babu Ubangiji sai Allah shi kadai ya zartar da alkawarinsa ya taimaki bawansa ya tarwatsa rundunar (kafirci) shi kadai.
Daga baya ya koma saman garin Makka a wani wuri da ake kira HUJU'UN ya sauka anan.
Ranar takwas ga Zul hijja Manzon (SAW) sai ya nufi Mina (wato ranar da ake cewa Yaumuttarwiyya) ya sallaci Azahar La'asar Magriba da Isha'I, ya kwana yayi Asuba, sannan ya dan yi saurara anan har said a rana ta hudo, sai ya matsa zuwa Arfa, inda ya tarar an kafa masa Tanti a Namirah, ya sauka a ciki, har sai da rana tayi Zawali, sai yayi umarni aka kawo masa taguwarsa (ALKASWA'I), yah au ya zo tsakiyar kwarin Arafa, inda kimanin mutum dubu dari da ishirin da hudu suka taru, wasu kuma sunce mutum dubu 90 wasu sunce dubu 44, yayi musu khudbar nan tasa shahararriya, ga kadan kada abinda yazo a cikin wanna doguwar huduba tasa data tattare asasin addinin kaf:
'Yaku mutane ku saurari zancena, domin ni ban sani ba, mai yiwuwa bazan sake haduwa daku ba, bayan wannan shekarar, a wannan wuri har abada yaku mutane hakika jininku da dukiyarku haramunne a tsakaninku kamar haramcin wuninku wannan, cikin watanku wannan, a cikin garinku wannan… kuji tsoron Allah a cikin mata, kun rikesu da amanar Allah, kun halatta farjinsu da Kalmar Allah, kuji tsoron Allah ka shaida, mumunai 'yan uwane, bai halatta ga mutum ba yaci dukiyar dan uwansa sai dai da yardar rai, ku fadaka shin na isar muku? To Allah ka shaida, kada ku dawo a bayana kafirai. Sahinku yana saran wuyan sashi, domin na barmuku abinda baza ku bata ba indai kunyi riko dashi littafin Allah, shin na isar? Allah ka saida. Yaku mutane, hakika Shaidan ya dauke kaunar a bautawa wanin Allah a kasarku wannan, amma ya yarda da abishi a cikin wanin wannan, na daga abinda kuke wulakantawa (kuke ganin ba komai bane) daga ayyukanku. Ya ku mutane hakika ubanginku dayane, hakana ubanku dayane, dukkanku daga Adamu kuke, Adam kuma daga turbaya yake wanda ya fiku girma wurin Allah shine wanda ya fiku tsoron Allah (saboda haka) babu fifiko tsakanin balarabe da wanda ba balarabe ba sai dai da tsoron Allah. Shin na isar? Allah ka shaida. Yaku mutane!!! Hakika Allah ya rabawa kowane mutum hakkinsa na rabon gado, wasiyya bata halatta ga wanda zai ci gado… yaku mutane!! Babu Annabi a bayana, kuma babu al'umma a bayanku ku fadaka ku fa bautawa Ubangijinku, ku sallaci biyar dinku, ku azumci watanku, ku hajjanci dakin Ubangijinku; kubi shuwagabanninku; sai ku shiga Aljannar Ubangijinku…". Muslim ne ya rawaito.
Wannan shine kadan daga wannan Khuduba ta shugaba Rasulullahi (SAW). Wanda yake daga muryarsa don Isarwa mutane kalamannan na Annabi shine Rabi'ata bin Umayyata bin Khalaf.
A wata riwayar akarshe Manzon (SAW) yace da Sahabbansa, za'a tambayenu game dani me zakuce? Sai sukace "zamuyi shedar ka isar mana da sakon Allah ka bada abinda aka baka, kuma kayi nasiha", sai Manzon (SAW) ya daga hannunsa sama yayi nuni dad an yatsansa yana cewa "Allah ka shaida" har sau uku. Muslim ne ya rawaito.
Annanne kuma Allah (SWT) ya saukar masa da fadinsa:
        ﭿ               .سورة المائدة 3                                              
Ma'ana:- "Ayau ne na cika muku addininku, na kuma cika ni'ima ta a gareku na kuma yarje muku addinin musulunci ya zamo addininku" (Ma'ida).
Ayar tana sauka sai S. Umar da Khaddab yayi kuka, sai Manzon (SAW) yace:- "me yasaka kuka Umar? Sai Umar yace ya Rasulallahi mun zamo kullum cikin karuwa cikin harkar addininmu, to amma yanzu ance ya cika kuma duk abinda akace ya cika to daga nan sai ya fara tawaya, sai Annabi (SAW) yace:- "kayi gaskiya".
Bayan angama khuduba sai S. Bilal yayi kiran sallah yayi ikama Manzon (SAW) ya ja mutane akayi sallar azahar, aka sake ikama yayi la'asar, sai Manzon (SAW) yah au (ALKASWA'A) ya matsa wajen Jabalur Rahmati wato (SAKHARAT) inda ya sanya gabansa ga Alkebla, bai gushe ba akan taguwar har sanda rana ta fadi, jan sama ya fara boyuwa, sai Manzon (SAW) ya matsa gaba bayan ya kutura Usamatu a bayan taguwarsa, har sai da yakai (MUZDALIFA) yayi sallar Magriba da Isha'I da kiran salla daya ikama byu daga nan Manzon (SAW) ya kwanta zuwa Asubahi ya tashi yayi sallar asuba, ya sake hawan (KASWA'A) yaje waje da ake kira (MASH'ARIL HARAM) ya fuskanci Alkibla, yayi addu'a ya kabbara Ubangiji ya yabeshi ya kadaitashi har sai da gari yayi haske sosai.
Daga nan sai ya nufi (MINA) kafin rana ta fito, a wannan karon kuma Fadlu bin Abbas ne yake bayansa a kan taguwarsa. Daga nan ya wuce zuwa AlJamratul Ula (wato wajen jifan shaidan) na farko yayi jifa da tsakwankwani 7, bayan ya gama sai ya karasa zuwa wajen soke rakuma, inda ya soke rakumi 63 da hannunsa, sannan ya bar S. Ali (KRW) ya karasa soke 37 cikon 100 kenan.
Daga nan Manzon (SAW) sai ya dawo zuwa Makka yayi azahar, bayan nan ya koma (MINA) tsawon kwanakin yanyani (AYYAMUTTASHRIQ) yana koyawa mutane aikin hajji yana wa'azi.
Bayan duk ya gama bada rukuna aikin hajji Manzon (SAW) sai ya koma zuwa birnin Madina don cigaba da shiryarwa da yada addinin Musulunci.
Saboda Manzon (SAW) yazo daf da birnin Madina; ya fara hango katangar birnin sai yace:
"الله أكبر الله أكبر الله أكبر لا إله إلا الله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شىء قدير آيبون عابدون ساجدون لربنا حامدون صدق الله وعده ونصر عبده وهزم الأحزاب وحده الله أكبر الله أكبر الله أكبر لا إله إلا الله وحده لا شريك له له"       

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي