Manahilur Rashad tare da Shehu Atiku Sanka
Amsar Tambaya ta 5
Dan Tijjaniyya da yake yin wasu wurdai na Zabi (Ikhtiyariyya) in ya barsu dan kansa ko kuma yai sakaci dasu to babu laifi akansa sai dai ya rasa alheri mai yawa.
Shehunmu Alhaji Ibrahim Inyass RA yana fada acikin Sashin amsoshinsa: "babu komai a akan wanda ya bar wadannan wuridai na kebance wato na Zabi sai dai alheri mai yawa ya kubce masa.
Yazo acikin littafin Al-Yawaqiyat Al Ahmadiyya wallata'ifir Rabbaniyya fil Ajwibati an baadhil as'ilati fit Tariqatit Tijaniyya na Masanin Allah Shehunmu Alhaji Ahmad Sukairij "na tambayeshi RA shin ya halatta ga mutum ya bar zikrai in shu'unansa sukai yawa kamar irinsu Almusabbiatil Ashri da Alladeefu da makamantan haka ko kuwa aa? Sai ya amsamin. "Kai sani ita Rai kosawa na daga Dabiunta, tausasawa da ita shi yafi a farkon Lamari ga wanda yake son tabbata akan wani aiki,dan haka ya wajaba akan muqaddamin da wani daga yanuwa ya nemeshi yai masa izinin wasu wuridai wanda ba lazimai ba kada ya sake ya Lazimtawa wanda akewa izinin wannan wurida (ya maida masa su na wajibi) hakanan kada shima abin yiwa izinin ya lazimtar dasu (su zama na dole) dan Hakane ma ake kiransu wuridai wanda bana lazim ba,
Naam idan mutum ya lazimtawa kansa karantasu ya maidasu a hakkinsa dole kamar BAKANCE ta yadda yaiwa Allah Swt Alkawarin bazai barsu ba to wadannan sun zamo tilas a hakkinsa ya wajaba ya lazimce su kuma ya ramasu in suka kubce masa saboda bakance da yayi.
Amma in ya karbi izininsu ne kawai dan Nemman tabarruki kawai to yana gareshi ya dawwama cikin karantasu ko kuma ya yanke yinsu wata rana, amma a sani MAFI SOYUWAR AYYUKA A WAJEN ALLAH SHINE WANDA AKA DAWWAMA AKANSA KODA KUWA YA ZAMO YA KARANTA.
Comments
Post a Comment