Fassarar Manahilur Rashad na Maulana Shehu Atiku Sanka:




Amsar tambaya ta Biyu:

Hakika adadin nan na Fatiha 99 shine karshen adadi cikin Karanta Fatiha ta yadda ba a karawa sama da haka don Hanin da Shehu Tijani yayi na cika ta Darin, don haka mai yin zikirinta ya iya yin kafa daya akan wannan niyya, ko uku kobiyar ko bakwaihardai takai 99 banda sama da haka da sharadin karantawa witri, amma Salatul fatihi ya iya karantawa takai 111 ko fiye da haka da sharadin yinta wutiri.


Hasilin magana dai su Fatiha da Salatul Fatih basu da adadi ayyananne ko lokaci ayyananne, bari kawai da gwargwadon iko, sai kuma tsarki na ruwa (alwala) sharadin cikin karata su,

Shehunmu Alhaji Ibrahim Inyass RTA ya fada a amsarsa data gabata
"Amma maqsadinnan na Salatil fatihi bashi da waqati muayyani ko adadi muayyani baridai gwargwadon iko, Tsarki (alwala) sharadin cikinnta kamar wuridin fatiha dion itama sharadin yanke, amma Salatul fatihi kawai (bada niyyar auradut tarbiyati ko ismul aazami) ba sharadi bace saida tsarki, bari ya iya karantawa a kowane hali." intaha.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY