KAFIRTA MUSULMI DA KA’IDOJIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA AKAN HAKA


Tareda Dr. Saleh Kaura

BAYANI NA ILIMI GAME KAFIRTA MUSULMI DA KA’IDOJIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA AKAN HAKA, DA KUMA WADANDA SUKE DA ALHAKIN SAUKAR DA WANNAN HUKUNCIN

-1-

Sayyiduna Usamat bn Zaid (Allah ya kara yarda da su) yana cewa: “Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa sallam) ya tura mu wani yakin sunkuru, sai kuwa gari ya waye mana a al-Hurukat –sunan wuri ne- a yankin Juhaina, nan na cin ma wani mutum, sai ya ce: “La’ilaha illalLah”, sai kuwa na soke shi, sai na ji na damuwa a zuciyata, sai na fada wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa sallam), sai ya ce: ((Yanzu bayan ya ce “La’ilaha illalLahu” din ne ka kashe shi?!)) sai na ce, ya RasulalLahi, ya fadi hakan ne saboda tsoron takobi, sai (SallalLahu alaiHi wa sallam) ya ce: ((Shin ka tsaga zuciyarsa don sanin shin ya fadi ko bai fadi ba?!)) Ya cigaba da maimaita wannan magana, har sai da na yi burin ina ma a ce a ranar na Musulnta” [Muslim, Abu Dawud, Ibn Majah, Imam Ahmad].

Kafirta Musulmi ba karamin hatsari yake da shi ba, a nan mun ga yanda Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa sallam) ya sanya sahabinsa a gaba yana yi masa fada; sakamakon kashe wani mayaki da ya fadi kalmar shahada a fagen daga, wannan kalma ita ce take rarrabe tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba, Imam an-Nawawi ya yi karin-haske akan wannan hadisin da cewa: “Allah ya daura mana yin hukunci da zahirin abin da ya bayyana ne, da kuma abin da aka furta da harshe.. shi kuwa sanin abin da yake cikin zukata, abu ne da ya wuce ikonmu.

Saboda haka, saurin kafirta Musulmi da ya yadu a wannan zamani namu, babban dalili ne da yake nuna yaduwar jahilci da son zuciya, kaman yanda Imam al-Ghazali yake fadi cewa: “Babu mutanen da suke gaggawar kafirta Musulmi sai jahilai”. [al-Iktisad fil I’itikad, shafi: 143].

Sheikh Muhammad Abduhu yana cewa: “Allah bai bai wa halifa, ko alkali, ko mufti, ko sheikhul Islam, wani iko akan akidun mutane, ko tabbatar da hukunce-hukunce ba.. saboda haka sam bai kamata wani ya yi da’awar cewa shi ne yake da iko akan imanin wani, ko a cikin bautar da yake yi wa Ubangijinsa ba, ko ya tirsasa masa bin hanyar da yake tunani… a Musulunci babu baba-kere akan al’amurran fahimtar addini, in ba ikon yin wa’azi mai kyau, da kira zuwa ga alhairi, da kuma tsoratarwa ga barin sharri ba, wannan kuwa iko ne da Musulunci ya bai wa har mafi kankantan Musulmai; domin ya fadakar da wadanda suke sama da shi, daidai da yanda ya bai wa shugaban al’umma; domin ya fadakar da na kasa da shi… Musulmi -komin matsayinsa a cikin addini- ba shi wa wani iko akan wani Musulmi -komin kankantarsa a cikin addini- in ba hakkin gabatar da nasiha da shiryatarwa ba.. A cikin ka’idojin hukunce-hukuncen addini da suka shahara a tsakanin Musulmai, akwai ka’idar da take cewa: Idan wani mutum ya furta wata magana da za ta iya zama kafirci ta hanyoyi dari, za kuma ta iya zama imani ta hanya daya kacal, to, za a dauki hanya dayan nan ta imani, sam bai halatta a dauke ta a matsayin kafirci ba.” [al-A’amalul Kamilah lil Imam Muhammad Abduhu, 3/283, 289, Muhammad Imara].

Kafirta Musulmi yana nufin fitar da mutumin da ya yi imani da Allah, da kuma sakon da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa sallam) ya zo da shi, kana kuma ya yi imani da mala’iku da littattafan da Allah ya saukar, ya kuma yi imani da ranar lahira, ya kuma yi imani da kaddara ta alhairi da ta sharri, daga cikin da’irar Musulunci, hakan yana kasancewa ne idan mutum ya rungumi wani abu na kafirci, ko ya bayyana wani abu da babu yanda za a yi Musulmi ya yi shi sai kafiri, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((Lallai fushin Allah yana kan wadanda suke furta maganganu na kafirci bayan sun riga sun yi imani, sai dai wanda aka tilasta masa furta kalmar kafircin, alhalin kuwa zuciyarsa ta gama natsuwa da imani da Allah, to wannan kam ba shi cikin fushin Allah…..)) [an-Nahli: 106].

Saboda haka, abin da ake nufi da kafirci a shari’ar Musulunci shi ne: Musun abin da kowa ya sani cewa yana cikin addinin da Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa sallam) ya zo da shi, kaman mutum ya musa samuwar Allah Madaukakin Sarki, ko ya musa Annabtar Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa sallam), ko ya furta cewa zina ba haramun ba ne, da makamantan haka.

Shi saukar da hukuncin kafirci a kan wani mas’ala ce ta fikhu, ma’ana hukunci ne na shari’a da ake sifanta ayyukan mutumin da shari’a ta hau kansa, saboda haka alkalai da manyan masu bayar da fatawa ne suke da hurumin tabbatar da haka, ba daidaikun mutane ba, Imam al-Ghazali yana cewa: “Kafirci hukunci ne na shari’a, kaman ‘yanci da bauta; ma’anarsa halatta zubar da jinin wanda a da haramun ne a zubar masa da jini, kuma hukunci ne da cewa za a dawwama a wuta, kuma ana gane hakan ne ta hanyar nassi ko ta hanyar kiyasi da abin da yake cikin nassi” [Risalatu Faisalut Tafrikah bainal Islami wal zandaka: shafi: 256], haka ma Imam al-Sibki yana cewa: “Kafirta Musulmi hukunci ne na shari’a sakamakon musanta Allantakar Allah, ko musun kadaituwarsa, ko musun sakon da ya aiko, ko yin wata Magana, ko aiki da shari’a ta hukunta cewa hakan kafirci ne, koda ba a yi musu ba”. [al-Fatawa, 2/586].

Sai dai duk da haka, malamai masana ba su manta da fadakar da alkalai da masu bayar da fatawa ba wajen jawo hankalinsu domin su bi sannu a hankali da taka-tsakan wajen zartar da hukuncin kafirci akan wanda yake cikin addinin Musulunci; musamman ma ayoyi da hadisai masu yawa sun zo; domin su yi wannan fadakarwar, Allah Mai girma yana cewa: ((Kada ku soma ku ce wa wanda ya yi maku sallama, shi ba mumini ba ne)) [an-Nisa’i: 94], sai shari’a ta gargade su da su nesanci yin gaggawa wajen kafirta mutane, ta kuma umurce su da yin bincike mai zurfi akan mutumin da wata alama ta Musulunci ta bayyana a tare da shi, duk kuwa da cewa yana rayuwa a cikin wadanda ba Musulmai ba.

Haka ma Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa sallam) yana cewa: ((Duk mutumin da ya yi sallah irin tamu, ya kuma fuskanci alkiblarmu, ya ci yankarmu, to kuwa wannan shi ne Musulmin da zimmar Allah da ta Manzonsa suke tare da shi, kada ku soma ku keta wa Allah huruminsa a cikin zimmarsa)) [al-Bukhari, daga Hadisin al-Barra’u bn Ăzib], a wani hadisin kuma cewa ya yi : ((Duk mutumin da ya ce wa dan uwansa: ya kafiri; to kuwa lallai dayan su ya zama, idan wanda aka fada wa din haka yake, to shi kenan, in kuma ba haka yake ba, kafircin zai dawo kan wanda ya fada)) [al-Bukhari da Muslim, lafazin na Muslim ne daga Abdullahi bn Umar].

Saboda haka, dole ne mai bayar da fatawa, ko alkali su yi taka-tsantsan wajen kafirta Musulmi; ba domin komai ba, sai domin hatsarin da yake cikin yin haka, kaman yanda Ibn Hajr al-Haitami ya fadi a cikin littafin [Tuhfatul Muhtaj, 9/88].
Imam al-Ghazali ya ce: dole ne a kame ga barin kafirta duk wani Musulmi, komin sabani, matukar yana riko da kalmar “La’ilaha illalLahu Muhammadur RasululLahi” cikin gaskiya, ba kuma tare da ya warware ta ba, saboda akwai babban hatsari a tare da kafirta Musulmi, shi kuwa yin shiru game da hakan ba shi da hatsari, yin gaggawar kafirta Musulmi dabi’a ce da take tattare da wadanda jahilci ya yi masu yawa.. ku sani cewa yin kuskure wajen barin kafirai dubu, ya fi sauki akan zubar da jinin Musulmi daya…..” [Adhwa’un alaa al-Maukifush Shi’iy minas Ashabir Rasul, shafi: 10]

Malamai sun bayyana cewa babu yanda za a yi a kafirta Musulmi saboda wani laifi da ya aikata na zunubi, wannan yana cikin asalin akida a wurin Musulmai, koda kuwa zunubin da ya aikata din yana cikin manyan zunubai –muddin ba shirka ba ne, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((Lallai Allah ba ya gafarta wa wanda ya hada shi da wani a wajen bauta, sai dai yana gafarta abin da bai kai haka ba, shi ma ga wanda ya so, duk wanda ya hada Allah da wani a wajen bauta, to kuwa lallai ya aikata babban laifi)) [an-Nisa’i: 48], kai ma malamai ba sa daura kalmar kafirci akan wanda ya aikata shirka, sukan dai cewa masa fasiki, ko kuma ya sami tawaya a cikin imaninsa, muddin dai ba ya halatta yin shirkar ba ne; saboda shi asalin kafirci shi ne karyata abin da aka yi imani da shi da gangan, da kuma jin cewa hakan ne daidai har a cikin zuciyarsa, ya kuma natsu da haka, domin kaman yanda imani yake a matsayin i’itikadi, haka shi ma kafirci i’itikadi ne, ma’ana a zuciya suke; ((Lallai fushin Allah yana kan wadanda suke furta maganganu na kafirci bayan sun riga sun yi imani, sai dai wanda aka tilasta masa furta kalmar kafircin, alhalin kuwa zuciyarsa ta gama natsuwa da imani da Allah, to wannan kam ba shi cikin fushin Allah…..)) [an-Nahli: 106]; saboda haka, ko mene ne Musulmi zai aikata na sabo, ba zai kafirta ba, matukar ba yana ganin halaccin abin da ya aikatan ba ne, amma dai imanin sa zai ragu ya sami tawaya.

Saboda haka ne Imam al-Ghazali yake cewa: “Asalin abin da ake kafirta Musulmi da shi wanda babu wani kokwanto akai shi ne: duk wanda ya karyata Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa sallam), to kuwa lallai kafiri ne shi, [al-Iktisad fil I’itikad, Shafi: 134]. A littafin [Risalatu Faisalut Tafrikah bainal Islami wal zandaka: shafi: 265] ya kuma cewa: “A asali ba a kafirta mutum a cikin mas’alolin furu’a sai a mas’ala guda daya, wadda ita ce mutum ya karyata wani hukunci na addini da aka ruwaito shi daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa sallam) ta hanyar tawaturi”.

Akwai wasu ma’aunai guda uku wadanda da su ne ake kafirta Musulmi idan ya yi su: Na farko: abubuwan da yin i’itikadi da su a karan kansu kafirci ne, kaman mutum ya yi musun samuwar Allah Madaukakin Sarki, ko ya musanta wata sifa daga cikin sifofinsa wadda Allantakar Allah ba zai yiwu ba sai da ita, ko ya karyata Annabta. Na biyu: ya aikata wani aiki da babu wanda yake yi sai kafiri. Na uku: ya musanta abin da ya tabbata karara a cikin addini, saboda anan kaman ya karkata zuwa ga karyata Allah da Manzonsa ne, Imam Izzuddeen Bn Abdus-Salam, da Imam al-Karafi sun kawo wadannan ma’aunai a cikin littattafansu kawa’id, [al-Mi’iyarul Mu’urab, al-Wansharisi, 12/74].

Al-Karafi ya ce: Asalin kafirci shi ne keta hurumin Allantakar Ubangiji, ko dai ta hanyar jahiltar samuwar Allah, ko jahiltar sifofinsa madaukaka, ko kuma musa abin da yake tabbatacce ne a cikin addini. [Anwarul Buruk fi Anwa’il Furuk, 4/115]

Imam al-Nawawi yana cewa: “Ka sani cewa mazhabar ahlul hakki ita ce: ba a kafirta wani Musulmi saboda ya aikata zunubi, ba a kafirta masu bin son zuciyarsu da ‘yan bidi’a –al-Khawarij da Mu’utazila da Rawafidh dss.”

Da haka za mu iya cewa mun fahimci ma’anar kafirta Musulmi, mun kuma san wadanda suke da alhakin yin hakan, da kuma ka’idojin da shari’ar Musulunci ta shimfida kafin har a kai ga kafirta Musulmi. Sannan kuma mun ga yanda ayoyi da hadisai suka zo da suke nuna irin taka-tsantsan din da ya kamata a yi wajen yin haka.. saboda kafirta Musulmi yana iya zamo dalili na kafircin wanda ya kafirtan, sannan hakan yana nufin cewa Musulmin ya yi ridda kenan, abin da kafirta shi yana nufin halatta jininsa, wannan kuwa ba karamin abu ba ne a rayuwar mutum a matsayinsa na mutum, da kuma a rayuwar zamantakewa ta bil’adama..

Allah ya kare mana imaninmu baki daya, amin.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY