WAFATN ANNABI SAW (11)
KABARIN MANZON (SAW):
Bayan daga ka kammala shirya Manzon
(SAW) sai aka fara tunanin inda za'a binne shi, sai wasu sukace abinneshi a
masallacin sa, wasu sukace a kaishi Baki'a cikin Sahabbansa, wasu sukace a inda
yake sallah, sai S. Abubakar yace "ni naji Manzon (SAW) yana cewa
"Ba'a karbar ran wani Annabi ba har sai an binneshi a inda aka karbi
ransa", saboda haka aka shata inda Annabi ke kwance aka daga shimfidar aka
haka rami anan aka binne shi.
To wajen haka ramin akwai hanyoyi biyu
da larabawa ke baka kabari, akwa SHAKKU da Lahdu, shi Shakku shine irin wanda
aka sani a kasashenmu wato uwa da 'ya. Shi kuwa Lahdu sai anyi baban wato uwa
sai ayi 'yar daga gefe ta yanda za'a tura mutun ciki baza a ganshi ba sai a
toshe kofar da tubala, galibi irin wannan anfani yinsa a wuraren da kuraye
sukafi yawa, saboda in sun tona don suci mutum bazasu tarda shiba an cusa shi
an rufe da tubali.
To
irin wannan hanya akayi wa Manzon (SAW) hakan kabari inda akayi masa Lahdu aka
jera tubala guda tara aka rufe.
An rawaito
daga Abdullahi bn Abbas (RTA) yace lokacin da sukayi nufin yiwa Manzon (SAW) hakan
kabari ya zamo a Madina akwai masu haka biyu daya shine Abu Ubaidah Amiru bnil
Jarrah shine yake yin haka irin hakan mutanen Makka wato (SHAKKU), sai Abu
Dalha Zaid bin Sahl shine Abbasu ya kirawo mutum biyu yace da daya zuwa ga Abu
Dalha, sannan yace "Allah ka zabarwa Manzon (SAW), sai wanda aka turawa
Abu Dalha ya sameshi da wuri yazo yayi wa Annabi (SAW) Lahdu.
YIWA
MANZON (SAW) SALLAH:
Angama
yiwa Manzon (SAW) wanka da likkafani ranar talata, sai aka dorashi akan gadonsa,
sai mazaje manya suka shigo suka yiwa Manzon (SAW) sallah daidaiku babu liman,
kowa tasa yakeyi da maza suka gama shiga sai mata suka biyo baya suma suka yi
sai aka shigar da yara haka akayi har kowa yayi sallah.
BINNE
MANZON (SAW):
Sayyidina
Ali da Kusam bin Abbas da Fadlu bn Abbas sune suka saukar da Manzon (SAW) cikin
kabarinsa, sai kuma Aus bn Khauliyyin.
Akwai
wata 'yar karamar katifa da Manzon (SAW) yake shimfidawa, kuma yakan sanyata,
sai baransa SHUKRANU ya dauketa ya sanya ta a kabarin aka binne da ita yace “wallahi
babu wanda zai sauke daurata bayanka har abada.”
Comments
Post a Comment