WAFATIN ANNABI SAW (6)
SAYYADI
ABUBAKAR YANA JAGORANTAR SALLAH:
Sa'adda
rashin lafiyar Manzon (SAW) ta karu, fita ta gagara gareshi zuwa jan sallah sai
yace "Ku umarci Ababakar yayi sallah da mutane". Sai Sayyada Aisha tace
"Ya Annabin Allah Abubakar mutum ne mai tsaushin zuciya sai Annabi (SAW) ya
sake cewa "ko umarci Ababakar yayi sallah da mutane", sai Aisha ya sake
fadin abinda ta fada da farko sai yace "kudai'yan uwan Yusifa ne, nace ku
umarci Abubakar yayi sallah da mutane, wato yana nufin sun cika jayayya kamar
'yan uwan Annabi Yusuf, ita kuma Aisha (RA) tana sone a janye jagorancin sallah
daga mahafinta gudun kada mutane su fitunu da shi, kuma tasan mutane basu son
duk wanda akace yau ya tsaya mahallin Manzo saw, amma Annabi (SAW) ya dage sai
shi.
To
daga nan Sayyadina Abubakar ya cigaba da jagorantar sallah har tsawon kwana
hudu, wato zuwa ranar da Manzon Allah (SAW) yayi wafati, inda ya jagoranci
salloli goma sha bakwai 17.
An
rawaito daga Sayyada Aisha (RTA), cewa Manzon (SAW) ya shigo dakinta lokacin
yana dafe da kafadar Fadlu da Sayyadi Ali (RTA) koda ya shiga sai ciwon ya
rufeshi, sai yace "ku kwarara min ruwa salka bakwai daga rijiyoyi
daban-daban".
Aisha
tace sai muka zaunar dashi akan wata kwarya ta Sayyada Hafsat (RTA) muka
kwarara masa wannan ruwa har sai da ya dinga dago mana hannu yana cewa (yaisa ya
isa) daga nan sai yaji sauki, sai ya fito ya zauna a kan matattakalar minbari
yace da mutane ku matso gareni, sai mutane suka taru sai yace "Allah ya
la'anci Yahudawa da Nasara don sun riki kabarurrukan Annabawansu gumaken da ake
bautawa.
A
ranar Alhamis kafin wafati da kana 4 Manzon (SAW) yace da Sahabbansa ko kawo min
takarda da alkalami in rubuta muku wani abu da bazaku bata ba a bayansa" a
lokacin ciwo ya kama Manzon (SAW) sosai a cikin dakin kuma akwai mutane, daga cikinsu
akwai Sayyada Umar dan Khaddab sai yace "ciwo ne yake rinjayarsa, kuma
akwai Alkur'ani a wurinku littafin Allah ya isheku, to sai wadanda suke dakin
sukayi sabani a tsakaninsu wasu na akawo wasu suna cewa a'a. koda jayayya ta yawata
sai Manzon (SAW) yace ku tashi kubani wuri".
A
wannan rana Manzon (SAW) yai wasiyya da cewa kada a bar Bayahude ko Nasara ko Mushriki
a Jazirar Larabawa.
Manzon (SAW) ya zamo kafin yasa S. Abubakar sallah yana
fitowa sallah duk kuwa da irin tsananin
ciwonsa, har sai da wannan rana tazo inda karshen sallarsa da mutane itace
sallar magriba inda ya karanta suratul Mursalati. Bukhari ne ya rawaito daga ummil
Fadli
Comments
Post a Comment