WAFATIN ANNABI SAW (10)


بئر غرس التي غسل الرسول من ماءها




((YIWA MANZON (SAW) WANKA)):
Bayan da akayiwa S. Abubakar mubaya'a ya zamo Khalifa, sai Ahlin Annabi (SAW) ,suka kifu wurin hada Annabi da yi masa wanka, wadanda suka yiwa Manzon (SAW) wanka sune, S. Ali Karramallahu wajhahu, da S. Abbas bn Abdulmuttalib da dansa Fadlu bin Abbas da kuma Kusamu bn Abbas shima da Usamatu bin Zaid bn Harisata baran Manzon (SAW) da Shukranu shima baran Manzon (SAW) wadanan sune suka wanke Manzon (SAW) sai kuma wani mutumin Madina wai shi Aus bin Khauliyyun.
S. Ali shine ya jingina Manzon (SAW) a kirjinsa, Abbasu kuma da kansa Kusamu da Fadlu suna jujjuya Annabi (SAW), su kuma Shukranu da Usamatu dan Zaidu suna zuba ruwa S. Ali yana cudawa, sun yiwa Annabi wanka ne da tufafinsa ba tare da sun tube suba S. ali yana fada sa'ar da suke yin wannan wanka "mamakin abinda ya tsarkakeka halin rayuwa da halin mutuwa!!!". Domin ba'a ga ko mai daga abinda ake gani a jikin matattuba a tare da Manzon (SAW).
An rawaito daga S. Aisha (RTA) tace lokacin da sukayi niyyar wanke Manzon (SAW) sai sukayi sukace "wallahi bamu sani ba zamu tube Manzon (SAW) kamar yadda muke tube mamatanmu ne ko kuma zamu barshi a cikin tufafinsa ne, wanke shi a haka? Da sukayi wannan sabani sai Allah ya jefa musu bacci, har sai da kowanne daga cikinsu ya zamo habarsa yana kan kirjinsa, sannan wani mai magana yai musu magana daga gefen daki, basu sai kowaye ba yana cewa "ku wanke Annabi kayansa yana jikinsa", sai suka tashi suka wanke shi da kayansa a jikinsa, suna zuba ruwa suna cudawa ta samon rigar.
LIKAFANIN MANZON (SAW):
          Da aka kammala wanke Manzon (SAW) sai akayi masa likkafani cikin tufafi uku, tufafi biyu sakar wani gari mai suna (SUHAR) a Yamen. Sunan tufafin (SUHARIAYYA), sai cikon na ukun wani mai suna BURD HIBRATIN. Shi an zura Manzon (SAW) a cikinsa ne kamar yadda aka rawaito haka daga Ja'afarussadiq shi kuma daga babansa Muhammadul Bakir shi kuma daga babansa Adi Zaind Abidina dan S. Husain dan S. Ali (RTA) jami'an.

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY