GABATARWA: Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) mai rayawa mai kashewa, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban kowa wanda yake cewa "Rayuwata da mutuwa ta alheri ce a gareku", da alayensa da Sahabbasa baki daya. Bayan haka, hakika tarihin wafatin Manzon (SAW) tarihi ne mai matukar sosa ran dukkan wani Musulumi masoyin Annabi (SAW) badan komai ba sai don irin matukar kauna da Manzon (SAW) ya nunawa Alummarsa da hanyoyi daban – daban wanda hakan tasa Allah (SWT) ya yabeshi da fadinsa. "عزيز عليه ما عنتم حريص عليكم بالمؤمنين رؤوف رحيم". Shi yasa a duk lokacin da ake karanta kissan wafatin Manzon (SAW) zaka ga duk wanda ke saurara jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karye, idonsa kamar yayi kuka wasu ma suna zubar da hawaye tsikar jiki tana tashi wanda hakan yana karawa musulmi so da kauna da kishin Annabi (SAW), saboda haka ne ma na rubuta wadannan 'yan takardu don fito da tarihin wafatin Manzon (SAW) cikin harshen hausa da kowa ka iya dauka ya kara
Comments
Post a Comment