Jabal Ar-rumat
Jabalurrumat wato Dutsen Maharba
Wannan Karamin Dutse shine ake kira Jabal Ar Rumat a Uhudu dake gefen garin Madina, yadda Manzo saw ya umarci maharba hamsin su zauna akan wannan dutse su kare bayan musulmi a yakin Uhudu Kar su bar wajen Koda musulmi sun nasara ko an nasara dasu.
Yayin da Musulmi suka raraka Kafirai sai wadannan Maharba suka manta da Umarnin Annabi saw suka sauko suka shagala da diban ganimar yaki a tunaninsu yaki kare, ashe a bayan dusten akwai Khalid bn Waleed yana fakonsu, Saukar su daga Kai sai Khalid ya danno aka sanya Rundunar Musulmi a tsakiya hakan ya jawo aka sami karyewar yakin.
Babban darsi shine ka ziyarci wannan wuri kagani kayi izina da barin sabawa umarnin Annabi saw wanda tun daga wannan lokaci kuma Sahabbai basu sake irin wannan ba
Allah ya yarda dasu.
Comments
Post a Comment