WAFATIN SHEHU IBRAHIM NIASSE DA ABUBUWAN DA YA BARI
بسم الله الرحمن الرحيم
الحمد لله رب العالمين، والصلاة والسلام
على أشرف الأنبياء والمرسلين سيدنا محمد وعلى آله وصحابته والتابعين ومن تبعهم
بإحسان إلى يوم الدين.
1.0. GABATARWA
Maulana
Shehu Ibrahim Niasse ya rayu ne baki daya cikin Hidimtawa manzonAllah SAW da
kuma kokarin Tarbiyyar Alumma kan Sunnarsa. Hakan ne yasa Shehu ya zamo hoto ne
da kowa zai iya Kallo yai koyi dashi, kamar yadda saadda ya koma ga Allah ya
bar abubuwa da daman gaske wadanda har yanzu ake ta sherhi akansu, don haka
wannan makala zata kalli shin wai da Shehu yai wafati wadanne abubuwa ne
suka wanzu nasa.
1.1. WAFATIN SHEHU IBRAHIM
Maulana
Shehu Ibrahim Niasse yayi rashin lafiya da ta sanya ya tafi jinya a wani
Asibiti a Birnin London na kasar Birtaniya, wadanda suka sahibci Shehu A wannan
Tafiya akwai babban Jikansa Sayyidi Imam Hasan Cisse wanda kuma ya zamo
Khalifarsa. Sayyidi Hasan ya bada Labarin yadda ya dauki wani darasi a lokacin
jinyar Shehu da yayi wanda yaga Lallai sai ya isar wa da duk Almajirin Maulana
Shehu Ibrahim Niasse, wannan ba wani abu bane kuwa illa Tsaida Farillai dake
Kansa na Sallah da kuma duk wani Wurdi nasa Shehu Bai fasa ba duk da radadin
ciwo.
Daga
wadanda suka je dubiya akwai Shehu Mahmood Salga shimaya bamu Labarin Yadda
suka tarar da Maulana Shehu Ibrahim Niasse a cikin ciwo amma da lokacin Sallah
yayi sai Shehu ya Miko Hannu a miko masa Dutse da zai shafa yai Taimama yasa
sayyid Imam Hasan Cisse ya fuskantardashi Kibla saboda Taazzarar da yin Alwala
da tashi yaiwa Shehu. A wannan gaba ne wani Malamin dan kasar Misra (Egypt) mai
suna Sheikh MuhammadMahmood Sawwaf yake cewa cikin Hakkin Shehu
“Shehu
Ibrahim Nyass shine babban Shehun wannan yanki bari shine yake tsayawa da
karfinsa a gaban duk wani motsi na kungiyoyi masu kalubalantar musulunci…kuma
mutane da dama Sun Musulunta a Hannunsa”
Maulana
Shehu Ibrahim Niasse awananan Hali ya koma ga Allah Ranar 15 ga Rajab 1395.
July 1975. Duk duniya ta gigiza da rashin wannan gwarzo da afirka ta jima bata
ga kamarsa ba. Kuma aka dauko gawarsa mai girma zuwa Senegal aka binne shi a
Madinarsa ta Kaulach.
1.2. ABUBUWAN DA MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE YA BARI
Maulana
Shehu Ibrahim Niasse kamar Sauran waliyyai yai wafati yabar abubuwa da dama,
wadanda bazamu iya ganesu baki daya ba amma zamu iya kallon abubuwannan ta
fuska uku:
1.
koyarwarsa a addini a aikace. 2. Koyarwasa a rubuce. 3. Zuriarsa da Almajiransa.
2.0.
koyarwarsa a addini. Bazan tsawaita anan ba, tunda abinda Maulana Shehu Ibrahim
Niasse yake maimaitawa dayane cewa a dabiantu da Sifofi na Annabi saw da koyi
da sunnarsa, ya ishemu isharaabinda Malaminnan Na Misra ya fada akansa, kamar
yadda aikin da Shehu yayi a lokacin Rashin Lafiyarsa ya ishemu Ishara don haka
Shehu Ya yankewa kowa Hanzari cikin Riko da Adiini da Shariar Annabi saw ta
hanyar aikatasu har numfashinsa na karshe, Shehu yana cewa cikin diwanin kan
Manufarsa a addini:
وأمة
قصدي فيهم أن أسوقهم**
إلى حضرة البر الرحيم إلهنا
“Ni
alumma manufata cikinsu na korasu zuwa Halarar Allah mai jin kai” hakana Shehu
ya fadi awata hara da akai dashi a Hijaz (Saudiyya) cewa shi Manufofinsa a
daawa sune:
Kiran
wadanda ba Musulmi ba su shiiga addini
Wayar
da kan Musulmi har tafiyarsu a Allah ta dore su kara imani kan
wanda suke dashi
Yada
Luggar Alkurani wato Larabci.
Zurfafa
jin yan uwantaka ta Musulunci a zukatan Bayi
Taimakekeniya
tare da kungiyoyin Musulunci na Duniya
Yakar
yan Baranda Yan MUSHAN (missionaries) na Kiristanci da Yahudanci.
2.1
To anan sai mui duba tsakani mugani shin da shehu ya bar maa wannan abu bayan
yai wafati kowa ya dora a inda Shehu ya bari ko kuwa an shga wasu abubuwa
daban? Shi kuwaShehu daya zaga duniya ya yada addini cewa yayi yayi ne don mu
yan baya mu dauki misali ya zamo mana sample ne kamar yadda yake cewa:
علوت البحار الزاخرات وإنني **
علوت القرى
والمدن بلح الجبالا
أروم رضى الباري لنصرة دينه **
وأبرز للجيل الجديد
مـــــــــــــــــــــــــــــــثالا
2.2. KOYARWAR
SHEHU A RUBUCE
A
gurguje ina nufi Talifan da ya bari, sashin masu binkice sun tabbatar da cewa
Shehu ya rubuta abinda bai gaza Littafi 70 ba
Daga
wadannan Littafai bari nai bayanin Biyu ko uku a takaice don muga irin abinda
suka kunsa:
2.3.
RAF’UL
MALAAM…
shi
wannan Littafi ya kunshi koyar da Sallah ne kamar yadda Manzon Allah SAW ya
koyar da kafa hujjoji da hadisai ingattatu, kuma asali ance Shehu ya wallafa
shi ne lokacin da aka samu sabani tsakanin Malamai a garin Kano kan Mas’alar
(KABALU) har takai ana kafirta masu dora hannu a kirji in suna Sallah, kuma
daga wannan littafi rigima ta kare.
2.4 TABSIRATUL ANAM FI ANNAL ILMA HUWAL IMAM
.
Shehu ya
wallafashi kan nusar da Musulmi cewa lallai fa Ilmi shine jagora, don haka ne ma
muke kiran Littafin TAALIMIN SHEHU, shehu ya kawo ayoyi da hadisai da
labarai dake nuna dole kowane musulmi ya tashi ya nemi Ilmi.
2.5.
SABILUSSALAM FI IBQA’IL MAQAM. Shehu ya wallafashi ne lokacin da mai fatawa na
Saudi ya bada fatawa kan a cire maqam Ibrahim daga inda yake, shehu yace dole
abarshi domin aikin Annabi saawda Sahabbai kamar s Umar ya tabbatar dashi anan.
Wannan littafi na nuna bin kwakwkwafin Sunna da shehu yake dashi da kuma
matsayinsa a duniyar musulunci wanda aka dawo akabi raayin shehu tilas.
2.6.NUJUMUL
HUDA… wannan littafi yazo ne
airin wannan lokaci da muke ciki yanzu inda akesamun masu cin mutunci ko Tauye
darajar Annabi saw, ance ansamu wani ne daya fifita wasu akan Manzin Allah saw,
Maulana Shehu Ibrahim Niasseban wani jinkiri ba ya dau Alkalmi da takarda ya
wallafa littafinnan don kare Darajar Annabi saw tare da nuna cewa babu wani
mutum a gaban Annabi saw.
3.0.
ZURI’AR SHEHU DA ALMAJIRANSA
3.1.
Daga abun da Shehu ya bari yabar Zuria da dama da kuma Almajirai da ba san
adadinsu ba.
Mun
samu labari Shehu ya bar yaya sama da 70 wadanda akasarinsu Mahaddata Alqurani
ne da Masu riko da Sunna. Daga ciki zan so na ambaci Khalifa Sayyidi Abdullahi
Niasse da Sheikh Ahmad Tijani da Sheikh Muhammadun Nazeer Sayyidiu Maamoon
Sayyidi Baba Lameen, wadanda duniya ta crawa Hula.
3.2.
A mata koda Shehu bai haifi kowa ba sai Sayyidah Maryam to wannan ya isa,
dalili kuwabayan ta haddace Alqurani tana da shekaru 15 afagen ilmi kuwa koda a
mata na duniya da suke takama da yancin mata da cewa sun cimma wani abu to basu
kere Sayyidah Maryam ba, saboda yadda ta dora kan hanyar Shehu cikin koyar da
Alqurani ga dubban daruruwan yara tare da Larabci sannan in sun tasa a tura su
kasashen waje don karo ilmi na addini dana zamani mai zurfi a kasashen Larabawa
da Turawa. Kai takai matsayin da Sayyidah Maryam ta shiga alaqar diplomasiyya
tsakanin Senegal da Iran lokacin da suka sami matsala kuma ta warware da
taimakawar Sayyidah Maryam haka kuma Senegal da Sudan sun sami matsala har aka
rufe embassy dinsu a Dakar da Khartoom, amma ta shiga tsakani ta gana da
Shugaban Sudan AL BASHEER tasa aka bude musu embassy dinsu.
Haka
ga mu muma anan Mun sami Sayyida Ummu Hanee wadda take jangorar Bayi kan hanyar
mahaifinta a garin Kano dama nigeria baki daya>
3.3.
Ta fuskar Almajirai zan maimaita abinda na fada wata muhadara ta a wannan
dandaline na cewar wata Jaridar Murtaniya ta Kaddara Almajirai da mabiya Shehu
da Miliyan Arba’in da shida.
3.4.
koda shehu bai bar Almajirai ba akace ya bar Manyan da duniya ta jinjina musu irinsu
Shehunan Kano Sanannu S. Atiku Sanka S Tijjani Usman Shehu Mai Hula S
Sani Kafinga da su sharif Ibrahim Saleh Wanda yau a fagen Hadsi baya da Tamka a
duniya, ko irinsu Sheikh Barham Mahmood Job wanda ya zamo tamkar inuwa ne ga
Shehu yana binsa ko ina kuma ya kwasa daga kwaranyensa ya zamo shugaban
Kungiyar Malamai ta Afrika to ai ya ishemu ishara kuma sun ishemu Fitilar
Haskawa cikin tafiyar mu a Allah.
Da
wadannan Kalmomi nake cewea Allah kasa mu amfana da abinda Shehu Ya bari duniya
da Lahira.
Wassalam Naku
Tahir
Lawan Muaz Atijaneey
08060306021-08099475470
dlmuaz.ara@buk.edu.ng
Bourda
Comments
Post a Comment