WAFATIN ANNABI SAW (8)





RANAR WAFATI LITININ 12/R/AUWAL/11:
An rawaito daga Anas bn Malik (RTA) yace ranar litinin da Asuba musulmi suna tsaka da sallar Asuba, sai Manzon (SAW) ya bude labulen dakin S. Aisha ya kallesu sunyi sahu ga S. Abubakar yana limanci sai yai murmushi, anan ma S. Abubakar sai yayi niyyar ya shige cikin sahu yana zaton Manzon (SAW) yayai masa ishara cewa ya cigaba mutane, kuma saboda farin cikin ganin Manzon (SAW) sun kusa su fitinu a cikin sallarsu, sai yayi musu nuni su cigaba da sallah, sai Manzon (SAW) ya saki labule, lokacin wata sallar bai zoba sai da yayi wafati.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas (RA) yace " a wannan rana Aliyu dan Abi Dalib ya fito daga wurin Annabi (SAW), sai mutane suka ce dashi 'yaya jikin Manzon (SAW) ya kwana ya Abal Hasan sai yace "ya kwana da sauki ALHAMDULILLAHI", sai Abbasu dan Abdulmuttalib ya kama hannun S. Ali yace "…. Ya Abi …. Na rantse da Allah na gane mutuwa a fuskar Manzon (SAW) kamar yadda nake ganeta a fuskan ki yayan bani Abdulmuddalib, kazo muje wurin Manzon (SAW) mu tambayeshi idan lamarin nan (khalifanci) a cikin mu yake musani, idan a cikin wanin mu yake mu shugabantar dashi, sai S. Ali yace "ni dai wallahi bazan ba domin in muka tambaye shi ya hanamu to babu wanda zai bamu a bayansa har abada.
ANNABI YANA ASWAKI DAF DA WAFATINSA:
An rawaito daga S. Ashia (RTA) tace "yana daga ni'imar Allah agare ni, Manzon (SAW) yayi wafati a dakina; a ranata, kuma a tsakanin haba ta da kirji na, kuma Allah (SWT) ya hada yawuna da yawunsa a karshen rayuwarsa, domin Abdurrahman bn Abibakar ya shigo gareni – Dan uwanta – a hannunsa akwai asuwaki, ni kuma na jingina Manzon (SAW) a kirjina, sai naga yana ta kallon hannun Abdurrahman, sai nagane yana so, sai nace doshi na kabar maka? (to a lokacin Manzon (SAW) ko magana baya iya yi) sai yayi nuni da kansa (Na'am) sai na karbar masa gudab daya na bashi, sai yayi masa tauri ya kasa taunashi, sai nace na tauna maka sai yace (da kansa) na'am, sai na karba na tattaunashi yayi laushi sai ya karba yayi asuwakin da ban taba ganin yayi mai kyansa ba, anan kuwa dashi kuma akwai wata 'yar kwarya da ruwa a ciki sai ya dinga saka hannunsa a ciki yana shafawa a goshinsa yana cewa:
"لا إله إلا الله أن للموت سكرات".
Ma'ana "La'ila illallah hakika mutuwa akwai daci".
Can sai Manzon (SAW) ya daga kallonsa zuwa rufin daki ya daga hannunsa sama, Aisha tace sai naga lebensa yana motsawa sai na sa kunnena naji me yake cewa sai naji yana cewa".
"مع الذين أنعم الله عليهم من النبيئين والصديقين والشهداء والصالحين، اللهم اغفر لي وارحمني وألحقني بالرفيق الأعلى، اللهم، الرفيق الأعلى الرفيق الأعلى الرفيق الأعلى".                           
Daga nan sai hannunsa yayi luu!! Yai kasa ya hadu da Ubangijinsa, inna lillahi wa'inna ilahi raji'un!!!.
Wannan wafati ya faru da tsakar hantsin ranar litinin sha biyu ga Rabi'ul Auwal shekara ta 11 bayan hijra, yana da shekara sittin da uku dai-dai. Hijirar masihiyya tana da shekara 633 A.D.

ZAMU CIGABA...

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY