ALMUNTAKIMU: daga Shehu Ibrahim Niasse
WASIKAR BARRANTA DA MASU KETA SHARIA
DAGA MAULANMU SHEKH IBRAHIM INYASS AL KAULAKHI
Da
sunnan Allah Mai rahama mai jinqai mai tsananin kamu mabuwayi wanda ya gagari
kowa mai girma, tsira da aminci bias Manzo Shugaba bawa wanda yake cewa: “Ya Fadimatu
bazan miki komai ba daga Ubangiji.”
Bayan gode masa da abinda ya dace sallamata
ta isa izuwa danmu AHMAD CIYAMU da MALIK SO izuwa ma duk wanda ya tsaya kan
wannan takarda na daga wand yake da’awar nasabtuwa izuwa garemu, abinda wannan
ke wajabtawa shine sanarwa da cewa mutum biyu basa tare dani kuma su bakomai
bane acikin lamarin wannan Dariqa, Majzubi da baiyi suluki ba, da saliki da
baiyi jazba ba in har suka wanzu akan halinsu, kuma suka tsaya ga barin
tafiyarsu. Kuma ni sha’ani na kamar yadda kuka sani duk mai son ya kasance tare
dani acikin hali to yabi hanyata a cikin zantuka da ayyuka ta hanyar bin umarni
da nisantar abubuwan hanawa, a zahiri da badini da kuma kishirwa da shaukantuwa
izuwa saduwa (WUSULI) da kuma yardarm da Allah da Manzonsa, Amma wanda yake
jingina kansa damu kuma yake haikewa wani abu na savawa shari’a mai tsarki mai
girma ta hanyar kutsawa abubuwan haramtawa da barin abubuwan umarni to ina
shaidawa Allah ina shaida muku cewa ni na barranta dashi. Ya Allah babu ruwana
da abinda wadannan mutane ke aikatawa “wadannan da suke savawa umarnin sa su
tsautu kafin fitina ta samesu ko kuma azaba abar sawa radadi” “ku tuba izuwa ga
Allah yaku muminai baki daya”.
Abinda kuka fada kuma na cewa muridina
jakace dake cike da asraru na halarori hakane, sai dai waye muridina daga
cikinku? Shiyafi wahala daga jar zaiba a wurinku. Inko lamarin nan ya kasance
kamar yadda kuka fada dinnan ne to ya kusata na dauke izni daga kan dukkan
mukaddamin da ake kutsawa abubuwan haramtawa a halararsa kuma bai tsaya da
abinda ya wajaba akansa ba, inko ya gaza to yaiyo hijra izuwa ga Allah da kuma
Manzonsa da kuma garemu. Kuma wallahi
babu anbinda ya tsaida sairin wadannan mutane har suka koma suna izuwa debe
kewa da fararru sai dai tsawon lokacin su da sukai batare damu ba, domin anan
wurinmu akwai matasa kanana da suka mance dandanon sha’awa, kai takai acikinsu
akwai wadanda ya mance matarsa bai zuwa mata saida izini da takurawa. Haka
Dalibaina suke ba sabanin haka ba.
Komawa
ga Allah dole ne da tuba da bin umarni da nisantar abun hani da gudun duniya da
tsantseni da koyon ilmi. Allah (S.W.T) yana fadawa waliyyin waliyyai “kace
ubangiji ka kara min ilmi.” Abinda ya dace da muridi karya tsaida (Sairinsa)
tafiyarsa har sai ya risku dani kuma lamarinsa ya shige min duhu, to a sannan
sai ya tafi ya nemi wani shehin da yafini daukaka a mukami.
Ku sani Allah Yaji kanku-cewa da yawa da
yawa daga masu da’awa suna toshe mutane daga tafarkin Allah ta hanyasr rashin
istikama daidaituwarsu. Duk wanda ko ya danganta da Allah kuma ya zamo yana
toshe mutane ga barin tafarkinsa to haka yayi fito-na-fito da Allah da yaki sai
ya zamo yana cikin zurin masu inkari da tsiyacewa, saboda kasancewarsa sababine
na haka (ga wasu). Don haka ba makawa gareku da ku halarcemu a mafi yawan
lokuta don ku karbi ladubban (suluki) tafiya cikin Allah. Kamar yadda kuka
karbi hakikar jazba. Wanda ya aikata haka to ya rabauta rabo mai girma.
Ba
makawa gareku daga canja abubuwan ki da suke faruwa cikin yan uwa, da hannu da
harshe da kuma zuciya kamar yadda yazo a hadisi.
Kuma ba makawa ga duk mai son amfanuwa daya
kiyaye abinda ke fitowa daga garemu na wasiyya a waka ko a zube. Wannan wasika
kiyayeta wajibine ga dukkan maridi. Wanda ya tsaya akanta kuma ya kwafeta ya
lazimceta ya karantata kullum.
Ku tsaida sallah ka bada zakka ku azumci
watan Ramadan ku hajjanci daki ga wanda ya sami ikon zuwa gareshi kuyi sadakar
dukiya don zatin Allah ta’ala yazo acikin hadisin muslim daga manzon Allah
(SAW) “tsarki yanki ne na imani Alhamdu lillalahi tan cika ma;auni (mizani)
subhanallahi walhamdulillah tana cikawa ko ta cika abinda ke tsakanin sammai da
kassai, sallah haske ce hakuri haskene, Alkur’ani hujja ce a gareka ko akanka
mutane sune sammako akwai mai sayar da ransa ko mai yenta shi ko mai halakar
dashi.”
Allah (SWA) yana fada shine kuwa
mafigaskiyar musu fada “hakika Allah yana umarni da adalci da kyautayi da
bayarwa ga ma’abota kusaci yana kuma hani ga barin alfasha da abin ki da
zalunci”
Kaico dukkan kaico ga wanda baya fuskantar
hukuncin Allah da manzonsa da karba cikakkiya. Sai dai wanda littafinan wannan
ya sameshi ya tuba ya sauri ya riski abinda zai iya to wannan yana da arzikin
duniya da lahira “Allah ya yafe abinda ya rigaya” amma wanda bai tsuatu ba to
ma shaidawa Allah nima ina shaida cewa babu ni bashi. Banyi baram baram da
mutun ba kuwa sai bayan da barrantar Allah da manzonsa dashi.
Ina horonku da yawaita karanta salatil
fatihi lima uglika. Ina kuma umartaku da boye sirrika a fadi da aikace. Ku
kubar bayyanawa da zacen Alhalin hakiku, ku shiga hanyar madaidaiciya wannan
abubawan sha’awa duk dagutu ne kuke bautamasa bayan kunyi da’awa Imani. Allah
(S.W.T) Yana cewa: “wanda yakafircewa Dagutu yai Imani da Allah to haqiqa yayi
riko da igiya mai karfi da bata tsinkewa Allah Mai jine masani.”
Kai Ahmad Ciyam ka isar da wannan littafi
ga duk mai dangantuwa damu ka aikawa kowane Babba a kowane wuri kwafi dan ya
karantashi ga wadanda suke tare dashi da
wadanda suke kewayensa.
Ina fata daga Allah Yasa zukata masu haske
su karvi wannan da kuma kunnuwa masu sauraro. Allah Ya shiryemu ya shiryeku.
WASSALAM WANDA YARUBUTA
IBRAHIM DAN ALHAJI
ABDULLAHI ALKAULAKHI ATTIJANI
ALLAH YA KIYAYESHI YA KARESHI DAGA DUKKAN
CUTA. AMIN.
Comments
Post a Comment