TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW (4)
Daga Tahir Lawan Muaz Attijaneey
A BIRNIN
MADINA ALAMUN BAN KWANA NA MANZON (S.A.W):
Bayan
dawowar Manzon (SAW) daga aikin hajjinsa na karshe, sai ya sami ciwon kai, kamar
irin na wanda yayi tafiya ya dawo, saboda gajiya, sannan daga baya ya sami
waraka. Danga nan kuma sai alamun bankwana suka kara bayyana a fili cikin Zantuka
da ayyukan Manzon (SAW), ga kadan daga wasu abubuwa da suke nuna haka.
An
karbo daga Abu Muwaihibata baran Manzon (SAW) yace Manzon (SAW) ya tasheni a
wani tsakar dare yace dani 'ya Aba Muwaihibata hakika ni an umarce ni dana
nemawa ahlin makabartan nan ta Baki'a gafara tashi mutafi". Sai na tashi na
tafi tare dashi, koda yaje tsakiyar mamatan sai yace "Aminci ya tabbata a gareku
ya ahlin makabartar nan, abinda kuka zamo a cikin yayi muki dadi, daga abinda
mutane suka zamo a ciki. fitintunu sun fuskanto kamar yankin dare bakikkirin ta
karshe tana bin ta farko, ta karshen tafi ta farkon sharri", daga nan sai
Manzon (SAW) ya juyo zuwa gareni yace "ya Aba Muwaihibata hakika ni ambani
mubudan taskokin duniya da kuma dawwama a cikinta, sannan Aljanna sai aka bani
zabi tsakaninsu da haduwa da Ubangijina da Aljanna. Sai Abu Muwaihibatu sai
nace yace "fansarka uwata da ubana, ka karbi mubudan taskokin da dawwama a
duniya tare da Aljanne. Sai Manzon (SAW) "sam wallahi ya Aba Muwaihibata
na zabi haduwa da Ubangijina da Aljanna". Sannan ya nemawa Ahlin Baki'a
gafara ya koma gida, daga rannan kuma ya fara ciwon ajalinsa.
An
karbo daga Sayyada Aisha (RTA) tace Manzon (SAW) ya dawo daga makabartar Baki'a ya tarar dani ina
jin ciwon kai sai nace:- "wash kaina" sai yace bari dai Aisha wash!!!
Kaina nidai",wato kamar yana yi mata was an cewa duk abinda ya sameta ya
sameshi amma kuma a zahiri ma shima ciwon yake ciki. Sannan yace:- "Me zai
cukeki? Ai ba komai don ance kin mutu kafin ni, kinga sai na tashi nai miki wanka
na sa miki likkafani na miki sallah na binneki” sai tace sai nace dashi "Hmm
wallahi kamar ina kallonka in haka ta faru kana dawowa – daga binneni – ka shiga
dakina da wata daga matanka ku angwance". Sai Manzon (SAW) yai murmushi,
daga nan sai ciwon kansa ya dinga cigaba, a wannan lokaci yana ta zaga dakin Matansa
kamar yadda ya saba, har sai da ciwon ya ta'azzara sai ya nemi izinin matan da
yayi jiyya a dakin Sayyada Aisha (RA), sai sukayi masa izini.
An
rawaito daga Ayyub bn Bashirin yace " Manzon (SAW) ya fito kansa a sunkuye
har sai da yazo kafar mimbari ya zauna akansa, farkon abinda ya fara yi shine ya
nemawa shahidan Uhudu gafara ya yawaita addu'a agaresu, sannan yace "wani bawa
daga Bayin Allah, Ubangijinsa ya bashi zabi tsakanin duniya da lahira da kuma
abinda yake wurin Ubangijinsa, sai ya zabi abinda yakin wurin Allah (a lokacin
babu wanda ya fahimci abinda Manzon (SAW) yake nufi), sai nan da nan Sayyadi
Abubakar (RTA) ya fahimta cewa Annabi dai yana nufin kansa ne, sai kawai ya
kama Kuka, har wasu sahabbai na ganin bekensa cewa daga bada Labarin wani mutum
sai ya kama kuka?! To amma basu san Annabi (saw) yana nufin Kansa bane, Shi S.
Abubakar ya fahimci haka saboda haka sai yace "Bari ya Rasulallahi mu muna
fansar ka da kawunanmu da ya’ya’yenmu", sai Manzon (SAW) yace "Saurara
ya Ababakar", sannan ya sake cewa "ku duba duk tagar dake cikin
masallaci ku toshe ta sai dai tagar Abubakar, domin ni bansan wani mutum da ya
fishi kyawun abokantake gareni ba, da dai na zamo zan riki Majidadi (Badayi) da
na riki Abubakar Majidadina, sai dai kawai abota da yanuwantakar imani har
Allah ya taramu baki daya a wurinsa.
An
karbo daga Aisha (RTA) tace sau dayawa ina jin Manzon (SAW) yana fadin
"Hakika Allah bai taba karbar ran wani annabi ba har sai ya bashi
zabi". Lokacin da Manzon (SAW) yazo gargara karshen abindanaji yana cewa
shine "Bari
izuwa madangani Madaukaki:
"بل
الرفيق الأعلى".
Anan
nasan Annabi (SAW) ya zabi ya tafi, sai nace:
إذا والله لا يختارنا.
Daga
abinda yake nuna kusantowar wafatin Manzon (SAW) saukar suratun Nasri domin Allah
(SWT) ya gayawa Manzon (SAW) a cikinta cewa sa'adda yaga jama'a suna shiga
addini jama'a jama'a bayan da suna shiga daidaiku to yayi tasbihi da neman
gafarar Ubangijinsa, hakan kuwa ta faru, domin kafin tafiyar Manzon (SAW) zuwa
Hajjin bankwana kabilu sun dinga zuwa kungiya kungiya suna musulunta ga kadan
daga cikinsu:- jama'ar Najiran da sukazo suka musulunta su 60, sai kabilar Dhamam
bn sa'alabah da suka zo suka musulunta baki dayansu, sai kabilar Abdulkais, sai
kabilar banu Hanifa, wadanda a cikinsu aka sami Musailamatul Kazzab, sai
kabilar Taiyi'in da kabilar Kindah, da Uzhu shunu'ah da jama'ar Tujibah, da jama'ar
Kabilar Sa'alaba da Banu Asad da Banu Fazarata, da Banu sa'ad Huzaim, da Banu Gassan,
da Banu Muharibin, da Banu Urrata da sauransu, dukkan wadannan kabilu da jama'a
sun dinga zuwa daya, bayan daya suna mika wuya suna musulunta, koda ganin haka
Manzon (SAW) ya tabbatar da kusantowar ajalinsa shi yasa ake cewa suratu
Izaja'a ta kawowa Annabi (SAW) labarin zuwan wafatinsa ne.
Comments
Post a Comment