Manahilur Rashad tare da shehu Atiku Sanka (Hukumcin Shan Taba Ga Batijjane)




Amsar tambaya ta tara 9

Hukumcin Shan Taba Ga Batijjane

Batijjane da yake shan Taba ko Giya baya fitar dashi daga Tijjaniya, domin Shehu Tijani yai izinin a laqqana wurdinsa ga kowane Musulmi sawa'un Babbane ko Karami Namiji ko mace Da ko Bawa mai Da'ane ko Mai Sabo. Amsar wanda yake wazifa shi kadai ta gabata garemu, amma a rike wirdin Safe da Yamma banda wazifa baya halatta, wanda ya karba a haka to baa kirashi Batijjane!
Amma barinsa zuwa Zikirin Juma'a in yanayi shi kadai to wannan Qusuri ne (takaitawa) ne a wurinsa Zikrin jumaarsa ya inganta, saidai yabar abinda yake Lazimi gareshi.
Amma wanda yake inkarin Shehu Ibrahim in ya zamo yana riko da Darika ne to hakan bai fitar dashi daga Tijaniya saboda inkarinsa, saboda galibin Masu yiwa Shehu Ibrahim inkari Mahassada ne,sunai masa inkarine saboda Hassada.
Amma in yazamo yana inkarin Shehu Tijani da Darikarsa to wannan ne Munkirin da sallah a bayansa bata halatta.
Amma masu yiwa shehu Ibrahim Inkari da inkarin Zantukansa da ayyukansa bugu da Kari suna shan Giya suna aikata Sashin Zunubai to wadannan ba wanda zai kula su sambare ma ace a bisu Sallah saboda limancin Fasiki bai Halatta!
Intaha!

Comments

  1. KAYI KUSKURE SOSAI WAJEN AMSA TAMBAYAR BAWA MASHAYIN TABA DARIQA, MAZA KA TUNTUBI MANYA

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY