WAFATIN MAZON ALLAH SAW (7)



S. FADIMA DA MANZON (SAW):


An rawaito daga Sayyadah Aisha (RA) tace duk kanmu matan Annabi mun taru a wajen Annabi (SAW) sa'ar yana rashin lafiya sai ga Sayyada Fadima ta shigo tana tafiya, wallahi tafiyar ba maraba da tafiyar Manzon (SAW) tana zuwa sai yai maraba da ita yace "marhaba ya Yata", sannan ya zaunar da ita a damansa ko a hagunsa, sai ya gaya mata wata magana a asirce, sai ya gaya mata wata magana a asirce sai ta kama kuka, can kuma sai ya sake gaya mata wata maganar a asirce, sai ta fara dariya da fara'a, koda Aisha taga haka sai ta tambayi nana Fadima (AS) cewa me Manzon (SAW) ya fada mata sai tace bazan fadi sirrin Annabi (SAW) ba, sai da Bayan Mnzo saw yai wafati sNana Aisha (RTA) ta sake tambayar Nana Fadima (AS) kan wai me Manzon (SAW) ya fada mata tai kuka? Kuma me ya fada mata tai fara'a? sai tace yanzu kam zan fada miki, da farko ya gayamin cewa Jibril (AS) ya zamo yana bijoro masa da Alkur'ani duk shekara sau daya, amma wannan shekarar ya bijiromar da Alkur'ani sau biyu, saboda haka yana ganin ajalinsa ya kusanto, saboda haka kiyi hakuri kiji tsoron Allah don ni marigayi ne na gari a gareki". Daya gaya min haka sai nayi kuka, sai ya sake rada min magana a karo na biyu sa'adda yaga irin firgita ta da kukana yace "ya Fadima yanzu baki yarda ki zama shugabar matan talikai ba, kuma kece wadda zaki fara haduwa dani cikin duk ahlina". To sai nayi farin ciki da jin haka shine nayi dariya.
KAFIN RANAR WAFATI DA KWANA BIYU:
A ranar Asabar Manzon Allah  (SAW) ya sami sauki, saboda haka ya fito zuwa sallar azahar a lokacin S. Abubakar yana sallah da mutane S. Abubakar yana ganinsa sai ya fara yin  baya don ya koma cikin sahu, sai Manzon (SAW) yayi masa ishara da hannunsa cewa kar ya koma sai Manzon (SAW) ya karaso – yana dafe da mutum biyu yace ku zaunar dani a gefensa, sai suka zaunar da shi a hannun hagun din Abubakar (RTA) Manzon (SAW) yana yin sallah S. Abubakar yana koyi dashi yana daga muryarsa da kabbara don ya jiyar da musulmi.
RANAR LAHADI 11 – R/AUWAL/11:
Bayan da ya gama sai ya zauna yayi wa mutane khudbarsa ta karshe, yace "yaku mutane an rura wuta; fitintinu kamar yankin dare sun fuskanto, kuma ni wallahi ba abinda zaku rika daga gareni domin ba abinda na halatta sai abinda Alkur'ani ya halatta, kuma ba abinda na haramta sai abinda Alkur'ani ya haramta.
A ranar lahadi wato kafin yayi wafati da kwana daya  Manzon (SAW) ya yanta duk bayinsa yayi sadaka da dinare 7 da suka zuma d yake da ita, ya bawa musulmi makamansa.
A wannan dare sayyada Aisha (RTA) ta aika da fitilarta zuwa wata mata cewa ta zubo mata mai a ciki, ALLAHU AKBAR.
 Zamu Cigaba

Comments

Popular posts from this blog

SALLAR TARAWIHI DA TAHAJJUDI DA YADDA AKE YINSU

من خواص أذكار الطريقة التجانية حزب البحر للإمام الشاذلي

TARIHIN WAFATIN ANNABI SAW 1 DAGA TAHIR LAWAN MUAZ ATTIJANEEY